🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘
*RUHIN 'DANA*
🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘
RUBUTAWA
*AYSHA ISA*
(Mummy's friend)_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah.*_
_*Littafan marubuciya*_
_1. Na tsani maza_
_2. Meke faruwa?_
_3. Illar rik'o ('yar rik'o )_
SADAUKARWA GA:
*AUNTY HAUWA*
_(Ummu walid)_&
*RAHEENAT M. ABBAKAR*
_(Yayata)_*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
(g̲̅i̲̅d̲̅a̲̅n̲̅ z̲̅a̲̅m̲̅a̲̅n̲̅ l̲̅a̲̅f̲̅i̲̅y̲̅a̲̅ d̲̅a̲̅ a̲̅m̲̅a̲̅n̲̅a̅, i̲̅n̲̅s̲̅h̲̅a̲̅ A̸l̸l̸a̸h 🤜🤛). ̸ ̲*BIMISMILLAHIR-RAHMAIR-RAHIM*
_*Sorry for the long wait dudes, kusan jiki da jini sai a slow but Alhamdulillah am now fit. Ina yinku irin totally*_
_*101-105*_
_Batare da bata lokaci ba su nufa Hafiz. Sun kuwa yi sa'a yana gidan, bayan 'yan gaishe-gaishe Musa ya sanar dashi halin da suke ciki, ransa ya mutakar b'aci da jin bayanan su don shi a nashi ganin sakaci na irin tasu ta sanya hakan faruwa, daga bisa ni dai ya basu shawara da koma gun bokan ya tabbatar zai samar masu mafita. Godiya suka masa sannan suka mik'e kowa ya nufi gidansa banyan sun yanke shawaran tafiya gidan bokan gobe._
_Haka Lissa ta gama kumbure-kumburanta cikin kwanaki biyun har ta gaji don kanta ta sauko don ko k'yar Bukhari ta daina gani._
_Ita kam Jummai bata da matsalar da ya wuce ta wannan tukunyar dake wurinta don ganin take kamar barin shi a gun ta bai dace ba, bayan wannan bata da wata matsala don yanxu jikin Baffa alhamdulillah kullum dad'a sauki yake._
_*Washegari*_
_Da misalin karfe 10pm Bukhari da Musa dau hanya sai gidan bokan. Tafiyar 20mins sukayi sai gasu a gidan, sunyi zaman kusan awanni biyu kam su samu ganinsa. Bayanin abinda ya kawosu suka masa, da farko koransu yayi amma bayan magiya da suka masa yace su dawo nan da sati d'aya. Haka suka masa godiya suka tafi jikinsu duk a sanyaye dan ba haka suka so ba._
_Haka al'amura suka cigaba da tafiya masu sam babu dad'i don har wata irin rama Bukhari yayi don sam babu wani sauyi ta b'angaren Jummai duk da kuwa irin soyyayar da kulawar da yake nuna mata wannan bai saka ta maida masa tukunyar ba, duk ya k'agu ranar littinin yayi suka koma gun boka don ranar ne sati d'aya cif._
_Musa kam kafin da sauki don a washegarin ranar da suka taje gidan bokan yaron aikinsa ya shaida masa an samu jinin, a ranar ya aiwatar da aiki wannan yasa ya rage yawan mafarke-mafarken da yake yi._
_'Bangaren Lissa kuwa duk inda taso su keb'e da Bukhari abin yaci turo don sam bata gan fuska yin hakan ba._
_*Bayan Sati d'aya*_
_A yau littinin wanda yayi daidai da sati gudu da boko basu, tun da asuba suka kama hanya suka tafi gidan bokan inajin ko sallar basuyi don a gun 5am tayi masu._
_Bayan bokan ya gama buge-buge sa ya gyara murya yace "kai Musa taka matsalar mai sauki ce don nagan har ta farawa dawowa daidai dama rashin aiwatar da aikin ne kan lokaci ne ya kawo haka, don haka yanzu baka da wani matsala._
_Washe baki Musa yayi cike da murna yace " godiya nake, Allah yaja da nisan kwana, haka ya cigaba da wasa bokan. Bokan ne ya dakatar dashi sannan ya juya gun Bukhari yana mai muna shi da d'an yatsa " kai kuma tun d'aga fari kaso ka bamu matsala gashi yanzu ma ta wurin ka matsalar ta kunno kai,idan ba kai sokon namiji ba yaya za'ayi ace abu mai muhimmanci kamar wannan ka bari matarka tasan dashi?,tofa ka sani babu wani abu da zamu iya yi a yanzu illa kawar da ita a doran k'asa don ta riga tasan sirrin mu ko._
_Kwalo ido yayi jin abinda bokan yace, k'asa magana nayi ya cigaba da kallonsa._
_"Baka ji abinda nace bane?" bokan fad"a cikin daka tsawa._
_"N..a..n..a..ji, amma ina son a min alfarma a bani wata mafita banda wannan._
_"Hhh! babu wani mafita bayan wannan sai dai zamu maka alfarma d'aya kaje kayi tunani a kai zuwa gobe, ko kuma rayyunka dukkan ku uku ku yazama fansar wannan laifin da ta aikata, zaku iya tafiya" bokan yace sannan ya tashi yayi shigewansa ciki. Sannan suma mik'e suka bar gun motarsu suka nufa kai tsaye. Bayan sun shiga sun zauna har Bukhari yayi kunna mota Musa ya juya ya fuskanci Bukhari yace " wai kai wani irin mutum ne, munata niman mafita bamu samu ba yanxu kuma da muka samu maimakon ka amince ka tsaya bata lokaci, wai Jumman ce baka son rabuda ko meye?, inace maka daina sonta kuma ka daina yayinta sai Lissatu?_
_Ajiyar zuciya Bukhari ya sauke sannan yace " hakan Musa amma a 'yan kwanakin nan sam babu natsuwa tattare dani ganin nake kamar abinda nake mata bai dace, kuma maganar gaskiya banza iya kasheta ba kai bama ita kadai ba kowa ma banza kashewa._
_Kafe da idanu Musa yayi tunda ya fara magana har ya idda " hmmm Bukhari kenan watoh muda muka bada rayuwan mutane bamu san darajan su ba kenan?, ko me kake nufi da wannan zance naka?"_
_"Ni ba haka nake nufi ba, amma gaskiya nikam bazan iya ba" Bukhari yace had'e da tada motar suka tafi. Gidan Musa suka fara tafiya don sauke farili sannan Bukhari ya tafi gida._.
_Lokacin da ya isa gida, Lissa d'aya ya samu zaune a dinning area tana breakfast haka ya wuce ta batare yayi sallama ba balle ta samu kallon arziki hasali ma bai san tana zaune a gun ba, tashi tayi ta rufe masa baya har dakinsa, " mall. ina son magana da kai kuma wallahi yau dole ka saurareni ayi ta k'are ehee" lissa ta fad'a cike da tsiwa. Uffan bai ce mata illa ma gefe ta da ya rab'a ya nufi hanyar bayi, gabansa ta sha tace "kai fa Bukhari magana nake da kai ka maidani kamar zautacciya."_
_Tsayawa yayi yace " ina sauraronki."_
_"Dama da *ruhin d'anka* kayi arziki?, dama ba haka aka haife baffa ba?, dama wannan dalilin ne yasa sauke Batool as manager na companyn ka?"_
_Muje zuwa_
_*Mummy's friend ce🤩*_

YOU ARE READING
RUHIN 'DANA
SpiritualLabarin ne akan mahaifin da yayi amfani da RUHIN dansa gun niyyar arziki. Wannan labari ne mai ban tausayi, cin amana. Kubiyo ni don jin inda wannan labarin zata kaya.