41-45

715 44 2
                                    

🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘

*RUHIN 'DANA*

🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘

              RUBUTAWA
              *AYSHA ISA*
          (Mummy's friend)

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah.*_

_*Littafan marubuciya*_

_1. Na tsani maza_

_2. Meke faruwa?_

_3. Illar rik'o ('yar rik'o )_

SADAUKARWA GA:

*AUNTY HAUWA*
_(Ummu walid)_

            &

*RAHEENAT M. ABBAKAR*
_( Yayata)_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
(g̲̅i̲̅d̲̅a̲̅n̲̅ z̲̅a̲̅m̲̅a̲̅n̲̅ l̲̅a̲̅f̲̅i̲̅y̲̅a̲̅ d̲̅a̲̅ a̲̅m̲̅a̲̅n̲̅a̅,  i̲̅n̲̅s̲̅h̲̅a̲̅ A̸l̸l̸a̸h 🤜🤛). ̸ ̲

_Lissatu 'yar gidan Bukhari,Bukhari ya gaisheki yace na baki wannan shafin kyauta  don irin soyayya da kike nuna masa😜😜😜._

_Shafakillah ya Ummeey🙏🙏🙏🙏🙏_

*BIMISMILLAHIR-RAHMAIR-RAHIM*

_*Page 41-45*_

_"Dama ba komai bane illa batun auren da nake son zan k'ara. "_

_Wani irin muguwa fad'uwa gaban tayi ido ta zaro tace cike da mamaki "aure fa kace?"_

_Gyad'a mata kai yayi alamar eh._

_Hannayenta biyu ta daura akan kirjinta da ya tsananta bugu "Innalillahi wa ina ilahi raji'un" dama saka a ranta babu makawa watarana sai Bukhari ya k'ara aure ko saboda samu zuri'a amma bata kawo haka nan kusa ba,  lallai Bugaje tayi gaskiya da tace namiji bashi da tabbas, gashi nata yafara nuna mata dan tun ba'a je ko ina ba ya fara batun k'ara aure._

_"Kinyi shiru baki ce komi ba."_

_Murmushi yak'e tayi tace "Allah ya sanya albarka,  yasa ayi da ranmu" sannan ta mik'e ta nufi hanyar dakinta don tana bukatan kasancewa ita d'aya ko zata samu sassaucin rad'ad'in da take ji cikin zuciyarta._

_"Ameen,  amma ya nagan kin mik'e kuma?"_

_"Eh dama ina sa niyyan tafiya daki dawowar ka ce ya tsayar dani" ta bashi sannan tayi tafiyar ta batare da ta jira amsar sa ba_

_Girgiza kai yayi had'e da tab'a baki "mata kenan ba'a rabasu da kishi,  anyway wannan ba matsala ra bace tunda nayi mai wuyan"yace sannan shima ya mik'e ya nufi nasa dakin._

_Itako Jummai tana isa daki ta fad'o kan gado ta fashe da matsanancin kuka, saida tayi mai isarta kanan daga bisani ta mik'e ganin babu me rarrashin ta,  bayi ta fad'a ta dauro alwala tazo ta gabatar da nafila raka'a biyu tana mai kai kukata ga Allah tare da rokon zaman lafiya da duk  wacce a za'a kawo mata a matsayin kishiya._

_Shi kam Bukhari ya zuwa daki yayi barci sa dan babu abinda ya damesa._

_*Bayan kwana biyu*_

_An kasa ranar biki nan da sati biyu, shirye-shirye biki aka fara ba kama hannun yaro ta kowani bangare kusa komai na bikin Bukhari ya nauyin sa hatta da ba gidan su amaryan. Kayan daki Bukhari ya canza Jummai ya zuba sabo,  dakin yayi matukar kyau sai kace na amarya, kwantar da hankali Jummai tayi ganin wa'innan abubuwan kyautatawa da yake mata kuma tana da yakini koda yayi aure bazai wulak'anta ta ba._

_Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya,  a yau asabar aka daura Bukhari da matarsa Lissatu akan sadaki dubu d'ari wanda yasamu halarta dinbin jama'a.  Biki ne na manya wanda naira saida sukayi kuka. Jummai ita tayi d'an taro ta a gida yayinda 'yan uwa da abokin arziki suka mata kara dan babu laifi sunzo d'an yawa._

_Da yamma lis aka kai Lissatu gidan angonta wacce gida d'aya zasu zauna da kishiyata, babu wanda bai yaba da tsamin gidan ba don ya tsaru  iya tsaruwa._

_Shiko Bukhari bai dawo gida ba sai karfe tara na daidai a lokacin kowa ya ya gama watsewa ko, dakin Jummai ya nufa  kai tsaye zaune ya sameta kan dadduma taba lazami, zama yayi har ta kamala,  gained dashi tayi sannan sukayi hira kad'an kanan mike had'e da ajiye mata a certain gefenta "mu kwana lafiya uwar gida sarausatar mata"yace cike da zollaya sannan ya fice daga dakin._

_Wannan kalmar ya b'ata ran Jummai matuka wadata sanya gar saida ta zubda kwalla "watoh ni Bukhari ke wa rashin mutunci dan kawai ya k'ara aure hat dawani kirana uwargida,  mtsw.... " ta karisa maganar had'e da  jan dagon tsaki sannan ta kwanta abinta._

_Muje zuwa_

_*Mummy's friend ce 🤩*_

RUHIN 'DANAWhere stories live. Discover now