_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 5~6*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Rumaisa ce tadawo daga School tashiga d'aki domin tacire uniform nata saitaganta a kwance tana bacci kafanta da farin abu an d'auro, dagudu tafito waje tazo gun ummi tace "ummi wacece acikin d'aki tana bacci" murmushi tai tace "wata baiwar Allah ce JAWAAD yataimaka acikin dajin DOSO kiyi a hankali karki tadata tana bacci saboda tana buk'atar hutu" kai gaskiya ummi tanada kyau sosai harma tafini suma nida 'yan class d'inmu kefadin inada suma sosai to yau naga wacca tafini ita. dariya ummi tai tace "kije kicire kayan kizo kici abinci",,,,..
Damisalin 2:00pm ta farka ummi tasaka Rumaisa ta taimaka mata tai alwala tai sallah bayan tagama sai tai zaune, Rumaisa tashigo d'akin d'auke da nono kindirmo tana murmushi tak'araso kusa da'ita ta ajiye sannan tazauna tareda fad'in "sannu baiwar Allah ya jikinki" itama murmushin tai tace "dasauk'i" sake kallonta tai tace "ga nono nan ummi tace akawomaki kisha" tafad'a tana mik'a mata kwaryar dake d'auke da nonon itama ta karb'a tareda fad'in "ok thanks my friend" sannan takai bakinta tafara sha,,,, kalmarda tafad'a ce Rumaisa tasake maimaitawa acikin zuciyarta wai my friend tana nufin ni k'awartace to shikenan tayanka a gaba,,,,,,".Bayan tagama sha ta'ajiye sauran tarufe da murfi, Rumaisa takalleta tace "ko zamu iya zama k'awaye" murmushi tai tace "why not zamu iya mana" wani da'di ne yatirnike Rumaisa har saida takasa boyeshi tace "kai amma naji dad'i sunana Rumaisa kefa...?" tafad'a tana dariya tana kallonta "nikuma sunana ZULAIHERT" laa sunan k'awata ta makarantarmu. Nanfa tazake taita zubamata surutu da labarin gidansu dana JAWAAD da yanda yakeyi idan yana fushi ya turo bakinshi a gaba nan ZULAIHERT taita dariya tana rik'e ciki saboda Rumaisa akwai ban dariya ga iya tsokana,,, haka sukaita firarsu atare har lokacin zuwa islamiyya yai sannan ta tashi tashirya tawuce,,,,,..
Acikin kwanakinda tai a gidan ta fahimci abubuwa da dama k'awancensu da Rumaisa kuma yak'ara k'ullawa sosai,, yau kimaninta uku kenan a gidan taji sauk'i sosai dan har yawo fita sukeyi da Rumaisa inda JAWAAD kebata kulawa sosai ta iya k'arfinsa saboda lurarda yai ZULAIHERT 'yar mai kud'i ce hakan yasa yake kula da'ita sosai,,, aranarda tacika kwana na hud'u aranar ne tace zata wuce gida kuma aranarne tafad'a masu ko ita wacece dakuma inda tafito, sunji dad'in zama da'ita sosai saboda sam batada halayyar wasu y'ay'an na masu hannu da shuni,, har tasha suka rakata saida tashiga mota sannan suka dawo Rumaisa harda y'an kwallanta saboda cikin y'an kwanakinda sukai sunshak'u da juna,,,,,"..
**** **** *****
*SHIN WACECE ITA....?*
ZULAIHERT SA'AD MAINASARA shine cikakken sunanta haifaffiyar k'asar KEBBI acikin Birnin kebbi local government, ita 'ya ce agun Barrister Sa'ad mainasara shugaban lauyoyin Nigeria, Zulaihat kyakkawa ce sosai komai nata is so fine sexy eye's nata pink lips and skin color nata eye bolls nata gakuma thick eye lashes nata,, Zulaihert takasance yarinya mai hankali nutsuwa dakuma tausayi takan sadaukarda nata farinciki domin wani yasamu nashi farincikin, mahaifiyarta hajiya Amina kyakkawace bafulatana hakama mahaifinta kyakkawane bafulatani, Zulaihat itace first born agidansu k'anenta biyu Zuwairat da Zayyad,,, dikda kud'in mahaifinsu amma sam basuda girman kai basu damu da duniya ba bare kuma abunda ke cikinta sab'anin mahaifinsu daya d'auki duniya da girma, burinsa ga y'ay'ansa shine suyi karatu mai zurfi kaman yanda yai koma sufisa sab'anin su dasukeso suyi aure tinda sun kammala secondry School gakuma manema nata zuwa amma yacije yakafe bazasuyi aure a yanzuba,, ganin zasuyi westing time nashi yasa yad'aukesu daga k'asar gaba d'aya Zuwairat yakaita England a wata katafariyar University dake babban birnin na England, sai itakuma Zulaihert yakaita Niger a wata sabuwar University dake garin DOSO dan sunema first sate nata tana karantar medical doctor inda kuma suke year one,,,"
Wannan kenan***** **** *****
Tana isa tafara neman k'awayenta waenda sukaje atare saikuwa tagansu dika nan ta zauna sunata labarin tafiyar tasu suna shan dariya dayanzu ZULAIHERT tazama jini ko gawa nan suka tambayeta yanda akai takubuta daga hannun wannan mayunwacin zaki ta kwashe komai tafad'a masu har zamanta gidansu JAWAAD dakuma irin shak'uwarda sukai acikin k'ank'anen lokaci,,,,..
Sunyi mamaki sosai da jarumta irinta JAWAAD anya za'asamu irinsa kuwa musamman acikin birni nansukaita yabonsa wata harda cewa inama zata gansa aikwa nan ZULAIHERT tawatsa mata wata uwar harara saboda maganarda tafad'a saida taji wani abu yataso ya tokaremata zuciya wato kishi tbd lallai kuwa ZULAIHERT hhh Lol,,,"..
Firar gabad'aya ji tai tafita a ranta ta tashi tawuce abunta sukwa suka kwashe da dariya suka tafa,,,"..
Kwananta biyu da dawowa tashirye tawuce gida KEBBI..
#/Vote
#/Share
#/Comment'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖊
