_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 17~18*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Tsaye take itakad'ai a bakin k'ofa tana kallon yanda ruwa ke sakkowa daga sama wato ruwan sama kasancewar yanayine na damina, tanajin dad'in yanayin ruwa kawai akeyi gakuma iska mai dad'i tana busowa, sanye take da wasu English were's masu kyan gaske bobza ne iya guiwa da singlet fara iya cibiya sumarta ta tufketa da ribom mai kyau, bawani make up a fuskarta amma dikda haka saida kyanta ya bayyana a fili kyakkyawar surarta ta bayyana wacca tafi kyau da arufeta ba a bayyanata ba,,,...
Tsaye take har ruwan ya d'auke sannan tasaka takalmanta plat shue tad'auki y'ar k'aramar jakar rataya da wayar ta sannan tafita,,,,....
Kai tsaye hostel d'insu sumayya tawuce koda tashiga saita taddata tana kwalliya tana ganinta tai murmushi azatonta gayyatartace ta karb'a, zama tai kan gadonta tareda fad'in "wannan gayun kuma sai ina" murmushi tai tace "fita zanyi wallahi dama kuma inaneman abokin rakiya tinda kwa kinzo nasamu" tsayarda kwalliyarda take tai tak'aremata kallo tana murmushi tace "wooww my friend kinyi matuk'ar kyau wallahi inama frnd d'ina zai sameki gaskiya daya more" shan kunu tai sannan tace,,...
"kinga wallahi yanzu zanfita nabar maki d'akinki idan baki daina man wannan banzan zancen nakiba" ohhh...!!! am sorry nabari Allah yahuci zuciyarki. tai maganar cikin tsokana, bayan tagama shirin tasaka takalmanta masu tsini kanta ba mayafi sab'anin ZULAIHERT dan ita koya tai shiri saita yafa mayafi akanta, bayan tashirya tad'auki key d'in motarta suka fita,,,..
Sumayya itama y'ar mai kud'i ce sosai kuma itakad'ai Allah yabama iyayenta hakan yasa suke bata gata sosai kamar yanda mahaifin ZULAIHERT yagina mata gida anan DOSO kawai dan tayi karatu haka itama nata mahaifin yagina mata saidai na ZULAIHERT yad'anfi nata girma da had'uwa, dikda gidanda aka ginamata amma tabarshi tadawo hostel da zama saboda taji dad'in holewa da samari acikin School saita mata dad'i take zuwa gidanta sab'anin ZULAIHERT da saboda taji sauk'in yawon hanya na zuwa da dawowa yasa tazauna hostel,.
Wata hanya taga sun hau wacca bata tab'a biba cikin sauri tajuyo tacemata "sumayya ina zamuje ne naga kinbi wannan hanyar" murmushi tai sannan tace "karki damu mana gidan k'awata fa zamuje kuma bazamu dad'eba zamu dawo" jin abunda tafad'a yasa tajuya tacigaba da kallon titi amma badan zuciyarta nacikin nutsuwa ba,,...
Bata gama tsinkewa ba saida taga sun iso wani katafaren wuri k'ato upstairs har hawa shida a bangon ginin ta sama an rubuta PETROLEUM OR GAS maza ko mata, saida tagama tsayarda motar sannan tajuyo ga ZULAIHERT wacca tagama tsinkewa tsananin tsoro ya bayyana a fuskarta tazaro dara daran idanuwanta, dariya sumayya tai sannan tace "kikwantarda hankalinki ba abunda za'amaki shiga kawai zamuyi yanzu zamu fito just come down my friend" hmm itadai tai shuru tana kallonta dakyar tace,,..
"Sumayya dama nanne zaki kawoni amma kikak'i fad'aman wallahi danasan nan ne zaki kawoni daban yarda nashigo motarkiba" wata iriyar dariya ta kyalkyale da'ita sannan tabud'e murfin mota tafita tazagayo tabud'e mata itama tareda rik'o hanunta tajanyota tafito,,,...
Hanunta na sakad'e da nata suka kama hanyar shiga ciki, sunzo dai dai k'ofar shiga saisukayi kicib'is dawasu samari su shida kowannensu fuskarsa a rufe, ZULAIHERT rufe fuskarta tai da mayafinta har suka shige ciki batasan waennan mazan sunganta ba, saida suka shige ciki sannan tabud'e fuskarta,, acikin wajen ma yahad'u karshen had'uwa naira na aiki awajen daka gansa kasan na manya ne ba yara acikinsa, tinda suka shiga mutanendake ciki suka dinga kallon ZULAIHERT maza da mata sumayya kuwa sai wagar baki take tana murmushi sab'anin ita da tsatsananin tsoro yagama mamaye zuciyarta,,,...
Wani katafaren d'aki suka shiga had'adden gaske suna shiga sai taga wata mata wacca daka ganta kaga tantiriyar karuwa yar daba, suna shiga sumayya taje suka tafa suna dariya matar takalli ZULAIHERT tace "y'ammata kisaki jikinki nan kamar gidanku ne kinji" b'ata fuska tai tamurtuk'eta tamkar bata tab'a dariya ba tajuya fuskarta daga kallonsu batateda tace da'ita uffan ba, wani k'aton gardine yashigo cikin dak'in dagashi sai d'an kamfai yana shigowa yai tsaye yana kallon ZULAIHERT yana murmushi nandai sukai maganarsu cikin wani irin yare wanda sam ZULAIHERT bata iyashiba, bayan sungama sumayya ta taso tacemata sutafi aikwa kamar ajiraye take tawuce tashige gaba suka fita,,,,...
Acikin mota k'ala batace da'ita ba har suka iso School, suna isowa tai sauri tabud'e murfin mota tafita, hartafara tafiya ta tsaya tajuyo tace "Sumayya ina jimaki tsoron had'uwarki da ubangiji dan na tabbata bazakiji da dad'i ba kiji tsoron Allah kituba kidaina wannan banzar sana'ar dakika saka kanki aciki tin kar Allah yakarb'i rayuwarki shin idan kika mutu ahaka wace amsa zakibama ubangijinki me zakice masa...!!!" kalaman ZULAIHERT sunso suyi tasiri agareta amma shaid'an yana ganin haka yai saurin fad'awa zuciyarta yak'ara tinzirata tai murmushi sannan tace "ZULAIHERT dik halinda nashiga mahaifina shine sila kuma yafi kowa babban kaso na zunibi saboda shine silar shigata wannan k'ungiyar, yak'i ya aurardani yace dole sainayi karatu mai zurfi dayayiman aure tin da wuri dayanzu banfad'a wannan rayuwar danake cikiba saboda haka kidainaman wa'azi dan nariga danayi nisa d'an guntun wa'azinki batai tab'a tasiri agareniba" tana gama fad'ar haka ta tada motarta tawuce,,,..
Mamaki yacikata nan take kuma wani tinanin yafad'o mata kenan itama matuk'ar batasan abunyiba shaid'an zai iya ingizata kamar yanda ya'ingiza sumayya tafad'a wannan mummunar d'abiar tabbas yazama wajibi tai gaggawar d'aukan mataki tinkan shaid'an yayi nasara akanta,,, da wannan tinanin ta'isa d'akinta,,,...
****** *****
Suna isa yawuce gida kai tsaye ransa a b'ace, yana isa gida yakira Rumaisa yace "Rumaisa daga yau karna sake ganinki tareda yarinyar nan ZULAIHERT karnasake ganinta agidan" cikin mamaki ummi tace "JAWAAD lafiya meya faru ne wani laifin tamaka" matsowa yai gun ummi yace "ummi yarinyar nan ashe ba yarinyar kirki bace yau sarki ya aikemu muyi masa zagaye mu nemomasa wani yaro acikin shegiyar k'ungiyar nan ta masu neman mata da mata maza da mata ta y'an Nigeria shine naganta tareda wata y'ar iskar tantiriyar karuwa Sumy baby kuma a yanda nagansu natabbata ba kawota akayiba itama y'ar cikinsu ce saboda haka bazan sake barinta da Rumaisa ba kartaje ta lallata man ita watakil ma sone take taja hankalinta itama tasakata ta lallata mata rayuwa to daga yau nakatse wannan alak'ar" yana gama fad'ar haka yawuce yafita,,,...
Ummi sam nataji dad'in haka ba bataso haka takasanceba saidai har yanzu bata gasgata hakan ba saboda tasan ZULAIHERT yarinyace mai kirki ga hankali ga nutsuwa dikda k'ananan kayanda take sakawa amma tanada kirki sosai tana kare mutuncinta kai yakamata dai JAWAAD yai bincike sosai,, hakama Rumaisa takasa yarda da abunda JAWAAD yafad'a bama dan shine yafad'a ba da agaban ko waye zata k'aryatashi kuma tamasa Allah ya'isa akan sharrinda yayiwa y'ar uwarta k'awarta to amma ina yayan tane dole ta yarda da hakan,,...
********
Yauma dai kamar kullum karatu yafara tab'ata tagaji sosai tana buk'atar hutu ganitai ba inda yafi dad'in hutu da shan iska kamar unguwarsu JAWAAD saboda su sunada lambu sosai ga bakin rafi kaje kasha iska mai dad'i, cikin sauri tashirya cikin wata doguwar abaya bak'a har k'asa tai rolling da veal d'in rigar sannan tasaka takalma tafita....
#/Vote
#/Share
#/Comment'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖊
