_*JAWAAD*_🌷
_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚
_*PAGE 41~42*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_Wata y'ar ruga ce k'arama acikin dajin suna isa kusa matar tamasa iso acikin wata y'ar buka, suna shiga yakwantar da'ita akan gado sai matar tace yafita badan yasoba yafita,,...
Dazuwansu kuwa cikin ikon Allah da taimakon matar Allah yasauki ZULAIHERT lafiya sai kukan jinjiri kawai JAWAAD yaji nan yai hamdala ga ubangiji taredayi sujudul shukr,,..
Ya zaune yana jiran akawomasa baby yagani sai wayarsa tai k'ara nan yasaka hanunsa a aljihunsa yaciro wayar tareda d'aukar kiran, momy ce nan yai sallama tin batako amsa sallamarba tace "JAWAAD inafatar kunana lafiya ya ZULAIHERT" murmushi yai sannan yace "momy lafiya k'alau muke ZULAIHERT tasauka lafiya" cikin mamaki tace "JAWAAD kuna inane hala an turo police acikin babban daji kardai bakwa cikinsa" murmushi yai yace "munanan cikinsa momy taimako muka samu a wata ruga a nanne wata mata ta karb'i haihuwar saidai bansan me aka haifaba jira nake agama shiryasu sannan nashiga",,...
Wani irin murmushi tai harsaida JAWAAD yaji sautinsa shima yai murmushi sai tace "Allah ya albarkaci abunda ta haifa sannan kayi sauri kufito saboda inda kuke ba k'arfin network saboda naurar ta gano inda kuke police suzo sud'aukeku" yace "to yanzu zamu fito" yakashe wayar sannan yawuce cikin bukar,,...
Koda yashiga kuwa ZULAIHERT na zaune tana bama babyn ta nono yanasha, murmushi yai yazo ya zauna kusa daita tareda shafa kan babyn tai murmushi yace "hubby na me aka haifa ne" tai murmushi tace "baby girl" masha Allah ubangiji ya rayamana ita ya albarkaceta. tace "ameen",,...
Suna nan har dare yafarayi duhu yafara shigowa, bayan tai wanka matar tabata kaya tasaka akayiwa babyn wanka tabama ZULAIHERT ta tacciyar madara tasha sannan suka fito domin su wuce,,...
Rakiya tamasu ta nunamasu hanyarda zata sadasu da gari sannan sukai mata godiya suka wuce,..
Tafiya suke a hankali suna fira kukan tsintsaye kawai kakeji acikin dajin sanyi yafara sauka ZULAIHERT tasaka hijab d'inta tak'ara lullub'e babyn saboda gudun mura gata kuma sabuwar haihuwa,,...
Suna cikin tafiya momy takira sai JAWAAD yabama ZULAIHERT suka gaisa ta tambayi lafiyarta tace lafiya k'alau take sannan ta tambayi baby tai murmushi tace "gatanan tana bacci", bayan sungama tabama JAWAAD nan sukai magana tace karyakashe wayar yabarta a kunne zata sadashi da shugaban masu kula da naurori shikuma zai sadashi da police d'in yadinga masu kwatancen inda suke ahaka har sucimmasu suzo sud'aukesu,..
Haka kuwa akayi suna tafiya yana fad'amasu gasu sunzo dai dai kusa da kaza sun wuce gasunan yanzu sunkawo dai dai wata bishiya katuwa ta kuka,,...
Suna cikin tafiya kamar ance ZULAIHERT waiga tana waigawa kuwa saitaga y'an daban nan a bayansu k'iris yarage su cimmasu aikwa cikin tashin hankali tace "JAWAAD gasunan a bayanzu" dasauri yawaiga saiya hangosu sunkai su goma sha, da sauri yarik'o hanunta tareda karb'an baby suka fara gudu suma y'an daban suna ganin haka saisuka dafa masu baya,,,...
Gudu suke tamkar zasu tashi sama da y'an daban sukaga kamar bazasu iya cigaba da binsuba suna b'ata masu lokaci sai kawai d'ayan yaciro bindiga yasaita JAWAAD yaharba,,...
ZULAIHERT najin k'arar sakin bindiga tajuyo da k'arfi tareda kiran sunan JAWAAD, jawaaaaaaaaddd...!! tafad'a da k'arfi tareda turasa gefe d'aya da iya k'arfinta, bayan yafad'i sannan itama tabiyo bayansa tafad'o jikinsa, saidai hankalinsa a tashe yake saboda yaji k'arar bindiga to wa suka harba acikinsu shi kokuma ita ko babyn su.....??,,...
Suna ganin sun fad'i saisukai sauri sukazo suka zagayesu tareda nunnuna masu bindigogi suka d'ora su a kansu,,...
Police d'inda ke bibiyar su JAWAAD sunzo dab dasu amma basu saniba, sunajin k'arar bindiga dasauri da gudu sukayo dai dai inda sukaji k'arar ta bindiga,,...
Suna isowa kuwa saisuka hango y'an daban diksun kewaye su JAWAAD nan suka matso kowa yafito da tashi bindiga sannan suka zagayesu ogansu yace "karku kuskura ku motsa kuma karkuyi k'ok'arin guduwa" cikin tsintsar mamaki suka juya da sauri saisukaga police diksun zagayesu ta ko'ina bawajen gudu gasu kuma da yawa wasu a gaba wasu a baya,,...
D'aya daga cikinsu tsoro yaji yaje zai gudu sai wani police yakaimasa harbi a kafa saiyafad'i ganin haka yasa sauran suka mik'a wuya suka yada bindigoginsu suka d'aga hannayensu sama,,...
Wani irin dad'i JAWAAD yaji yai godiya ga ubangiji sannan yakai hanunsa yad'ago baby tareda ZULAIHERT, zaro dara daran idanuwansa yai cikin tsananin tashin hankali......
#/Vote
#/Share
#/Comment'''AUFANA for life '''
*I.W.A*🖊
