JAWAAD part 27-28

2.1K 119 0
                                        

_*JAWAAD*_🌷

_*BY~AUFANA*_
_Wattpad@Aufana8183_

® *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION~I.W.A*📚

_*PAGE 27~28*_
_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Wanka yai sannan yad'auro towel yafito, bayan yatsane jikinsa yad'auki kayansa yamayar sannan ya kwanta tareda juya mata baya, ahankali tabud'e idanuwanta saitaganshi konce amma yajuya mata baya ranta ya baci amma sai kawai ta share koba komai tad'an ji dad'i saboda baishigetaba bare yabarta da jinyar jikinta da gashi da ruwan zafi,, tana cikin tinani har bacci yad'auketa saidai shikam yagagara yin bacci abun sai dawomasa yake acikin kwakwalwarshi kamar ma yanzune yake faruwa, jin zuciyarshi yake kamar zata fashe saboda tsananin kishi,,,...

Sai kusan 4:00am sannan yai bacci,,,, washe gari tin 6:00am ta farka tarigashi tashi danhaka tai sauri tashige toilet saboda kar yafarka yaganta ba kaya ajikinta,,..

Wanka tai ta tsabtace jikinta sannan ta dauro towel tafito, bayan tafito tashafa mayukanta sannan tabud'e wardrobe taciro wata had'addiyar atamfa light blue and white color mai tsadar gaske tasaka underwear sannan tasaka atamfar, d'inkin mutan kebbi ne riga da sket da d'ankwali kayan sunmata kyau sosai, bayan tagama tai d'an simple make up sannan tad'akko tirare tafeshe jikinta dashi,,,,...

Daddad'an k'amshin tirarenta ne yadaki doogon hancinsa ahankali yafara bud'e idanuwansa sai yai tozali da kyakkyawar surarta, kasa d'auke idanuwansa yai har saida tajuyo yaga kyakkyawar fuskarta cikin ladabi tamasa barka da kwana tareda d'ukarda fuskarta k'asa tana murmushi cikin jin kunyarsa,,..

Shima cikin murmushin ya amsa mata sannan yataso yazo kusa da'ita yanamata wani shu'umin kallo yana murmushi "kintashi lafiya amaryata" kanta na k'asa tace "lafiya k'alau"  hanunsa yakai yarik'o hanunta yai kissing nashi yace "kai gaskiya amaryata lallennan yamun kyau sosai" murmushi tai batareda tace komaiba, matsowa yai kusa da'ita yak'ara janyota jikinshi yarungume yana shinshinar wuyanta yace "tirarennan yamun dad'i amaryata"  abun nashi tsoro yafara bata dasauri tajanye jikinta tai saurin barin dak'in hakan kuwa bak'aramin b'ata masa rai yaiba yai kwafa sannan yawuce toilet domin ya dauro alwala,,..

Kai tsaye d'akinsu zuwairat tawuce koda taje ta tarar zuwairat na kan sallaya tana jan carbi, cikin sallama tashiga ciki nan sukaimata barka da sfy ta amsa cikin murmushi, bayan sun gaisa tafita tawuce kitchen domin had'a masu breakfast,, zuwairat ce tashigo tareda rumaisa suka tayata aikin cikin k'ank'anen lokaci suka kammala nan suka d'akko suka fito dashi, ZULAIHERT wayarta ta d'akko takira sumayya domin tazo suyi break har kusan 5 miss calls amma bata d'agaba sai kawai ta kashe wayar ta ajiye,,,...

Bayan sunci sungama sannan JAWAAD yadawo nan ta d'auki nasa takaimasa shima yaci,,,, aranar zuwairat tashirya takoma School rumaisa ma takoma gida yarage daga ango sai amaryarsa,,,,...

Zaune take ita kad'ai acikin parlor tana kallon tashar zeeworld suna wani series film twist of fate saigashi yashigo, sannu da zuwa tamasa ya amsa cikin fara'ah nan yazuna kusa da'ita sannan yamik'a mata ledarda yashigo da'ita ta karb'a cikin ladabi sannan tabud'e,, naman d'awisi ne soyayye da zafinsa sai k'amshi yake, murmushi tai sannan takallesa tace "JAWAAD" yajuyo shima yakalleta saiyaji kamar tafi kowa iya fad'ar sunan harda umminsa dayake ganin kamar ita kad'ai ce ta'iya kiran Sunansa amma yau gashi yaji wacca tafita iya fad'a,,...

"Na am" yakarb'a mata cikin sassanyar murya nan tashagwab'e fuska sannan tace "meyasa kakesan wahalarda kanka ne nifa bance dole saika siyoman nama ba" murmushi yai sannan yace "karki damu alk'awarine nayiwa kaina jiya idan baki mantaba kuma sunnah ce ta manzon tsira idan ango zaizo gun amaryarsa yashigo mata da wani abu naci ko kaza ko madara kamar yanda annabi yai lokacinda ya auri nana Aysha Allah yak'ara masu yarda, lokacin aka kawota dazai shigo saida yarik'omata tatacciyar madara to saboda hakane muma muke koyi dashi"  murmushi tai tace "to Allah yabamu ikon cigaba da koyi dashi adikkannin al'amuranmu" yai murmushi yace ameen,,..

Tashi tai taje kitchen ta d'akko plate tazo tazuba naman sannan ta ajiye suka fara ci, batawani ci mai yawaba tace tak'oshi shikam yaci abarsa saida yakoshi, bayan yagama ta kwashe kayan takai kitchen sannan tad'akko masa ruwa a fridge yasha,,,...

Sunjima sosai a parlor suna kallo sai kusan 9:00pm sannan ta tashi yawuce d'aki domin yin shirin bacci, wanka tai tashafa mai sannan tawanke jikinta da sihirtattun tirarukanta masu k'amshin dad'i, bayan tagama sannan ta tashi tafara gyara gadon tacanja masa bedsheet, tana cikin gyarawa JAWAAD yashigo baice da'ita k'ala ba yashige toilet domin yin wanka,..

Bayan yai wanka yafito lokacin ita harta kwanta yasaka jallabiyarsa sannan yakashe fitilar d'akin shima ya kwanta,, dikda taga ya kyaleta amma zuciyarta cike take da fargaba shikuwa zuciyarsa cike take da takaici da tsintsar kishi shi kansa yasan yana matuk'ar k'aunar ZULAIHERT kuma yanaso yayi tarayyar aure da'ita amma zuciyarsa takasa hak'ura ta manta abunda yafaru hakan yasa dik abunda yakeji na buk'atar matarsa yai k'ok'arin dannesa saboda masifar kishi, ahaka yakwana batareda wani abu yashiga tsakaninsa da'ita ba saidai kam yadaiyi baccin ne amma badan yaji dad'insaba a tattakure yayisa,, haka itama dakyar baccin ya d'auketa saboda tsananin fargabanda take ciki saboda tanaji su Amina na labarin yanda mata keshan wuya da azaba a first night wannan shike sakata fargaba da jin tsoro,,,...

Washe gari tana tashi sukai sallah tawuce kitchen tahad'a masu breakfast, bayan tagama tazo wanka tashirya tsab cikin wata dakakkiyar atamfa Super wax mai kyan gaske dakuma tsada pink mai ratsin fari da bak'i acikinta, cikin sauri tashirya tafito tasameshi a parlor, yaukam atare sukai break d'in bayan sungama yarakata da kansa tahau a dai daita sahu tawuce School,, bayan tawuce shima yashirya yarufe gidan yawuce izuwa neman na halak d'insa,,..

        *****  *****

Yau kimanin kwana uku kenan dayin aurensu tin ranar farko rabonta da wani abu yashiga tsakaninta da JAWAAD abun yana matuk'ar bata mamaki saitai kamar tamasa magana saikuma tafasa saboda kunyarda takeji sam bazata iya masa wannan zancenba, a ranta tace "to miye amfanin yin aure na tindadai matsalata bata kawarba" haka zataita zama tana wannan tinani,,..

Karatunta yacigaba da tafiya dai dai yanzukam karatu suke ba kakkautawa saboda yanayin curse d'insu yanada wahalar karatu dole sai an dage an maida hankali hakan yasa take bama karatunta muhimmanci sosai, account d'inta yai low sosai gashi abincinsu yakusa k'arewa saidai JAWAAD namatukar k'ok'ari dik abunda tace tanaso nan take yake siyomatashi kan tadawo daga School har yai girki yagama ya gyara gida kasancewar shi baya dad'ewa sosai yake dawowa,,..

       Ahakanli kuma shak'uwa da soyayya ke gudana tsakaninsu tini suka sauyawa junansu suna ita takirashi da habibi shikuma hubby na wasa da barkwanci kuwa kaikace ba ma'aurata bane kaman abokanan wasan juna, acikin k'ank'ane lokaci suka shaku da juna kamar yaya da k'anwa saidai har yanzu bata tab'a masa k'orafi akan abunda yake mata ba agun kwanciya saboda har yanzu bai kusancetaba,, hmm lallai ZULAIHERT kinyi k'ok'ari da waennan yaran zamanine da tini anfara masifa da bala'i hhh Lol,,,..

Kiran dadyn ta tai tafad'a masa tana buk'atar kud'i account d'inta yai low, cikin kulawa ya tambayeta nawa take so nan ta fad'a masa sannam tak'ara da cewa tana buk'atar sabuwar waya phone dik yacemata bakomai zai aiko mata,, ba'afi kwana d'aya ba kuwa taji alert na naira dubu d'ari uku sannan aka kawomata dalleliyar waya sabuwa fall a kwali,,..

Yana zaune acikin parlor tashigo tamasa barka da hutawa ya amsa mata cikin fara'ah da sakin fuska nan ta zauna sannan tamik'a masa kwalin wayar, saida ya tambayeta menene ta kyalesa tad'agamasa gira alamar yabud'e yagani yai murmushi sannan yafara bud'ewa,,..

Numfashinshine yakusa d'aukewa saboda ganin dalleliyar waya sabuwa gal nan yasaka hanunsa yaciro sannan yajuyo ya kalleta yace "pleace hubby na kiman bayani mana" dariya tai sannan tace "it's for u only dady nane yabaka"  zaro idanuwansa yai cikin mamaki wanda hakan da yai saida yabata dariya taita kyalkyalata,,,..

Cikin mamaki yace "hubby na are u shure dady yabani wannan phone d'in" shuru tai sannan tace "a,a nice nabaka saboda wani lokacin ko inaso naji muryanka ba hali shiyasa kawai nace bara nasiyamaka phone kaga yanzu any time nake buk'atar san jin muryanka zanji" wani irin k'aya taccen murmushi yai yamatso yajanyo ta yarungume tsam ajikinsa taredayin kissing nata a baki yana fad'in "nagode nagode sosai matata Allah yamaki albarka yasa kigama da duniya lafiya Allah yabani abunda zan ramamaki alkhairinda kikeman" murmushi tai tace "kadainaman godiya habibi idan banmakaba wazan yiwa bakomai Allah yabaka aikinyi kacigaba da kula damu" yace ameeen hubby na,, daganan sukacigaba da kallo suna fira....



#/Vote
#/Share
#/Comment

'''AUFANA for life '''
  *I.W.A*🖊

JAWAADWhere stories live. Discover now