page 5-6

10K 407 5
                                    

....🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹🌹 *BABBAN...GIDA*🌹🌹
    🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

      *_P.W.F_*

© '''Written'''      
       By
*_Seemaluvv_*👄   

                   5-6page🌹

     Har saida Yaya Farook Yaje ya dauko key din ya dawo parlor,  ya zauna zaman jiran Fadwa.
  sai da ta Bata Minti 30,sanan Ta fito Parlon.
      "Yaya Farook gani!
Cewar Fadwa.
Tashi tsaye yayi tare da saka hannun shi cikin aljihu ' gami da yimata Wani mugun kallo,
     "Na dauka ko ' kinji sauki ne ai.
     "Don Allah nidai Farook ka kaimin yarinya aduba ta.
Cewar Umma dake zaune a dinning table ta na kallon shi.
   Yaya Farook  fitane yayi Fadwa na biye dashi a baya har suka isa wajen motan, Ya fara shiga sannan itama tashiga cikin hanzari mai gadi ya bude gate din ' tukunna Yaya Farook Yaja motar.
    Ba tare Da wani bata lokaci ba suka isa cikin Hospital yayi packing A gefe sannan suka fito, ganin Fadwa ba ta sauri yasa ya kama hannun ta ' Haka ya dunga janta har suka kai Office din Doctor din. Sannan likitan ya duba ta Ya rubuta mata magun gunan da za'a siya, Cikin jin Dadin Fadwa ta Ansa takaddar magungu nan don ganin babu allura ko daya aciki.
    Har ta mike tsaye Likitan ya tsaida ita da cewa,
      "Ki tsaya Akwai Allurar da za'ayi yanzu guda biyu, Data amai da kuma Wanda zata rage maki zafin jiki.
Ta najin haka ta juyo ta kalli Yaya Farook, Suka hada ido ' Ganin Ya hade rai ne yasa ta sunkuyar da kanta ba tare da tace komai.
      "Idan kin shirya sai ki juyo.
Cewar doctor,
   Jin haka Yasa ta juya ta mika mashi baya kamar da gaske ' Daya matso sai ta matsa haka suka dungayi da Dr din, Abin ne yabawa Yaya Farook haushi ' A fusace ya mike tare da finciko Fadwa ' ya rungumeta sosai ta yadda bazata iya motsi ba,
      "Doctor yi mata Allurar ' don sauri nakeyi.
Cewar Yaya Farook,
  Fadwa bata ankara ba taji shigar karfe ajikin ta ' jin haka yasa tasaki ihu cike da kankame Yaya Farook,
      "Wayyo Allah Yaya Farook!!!
      "Shhhh, kiyi hakuri saura guda daya kinji ko?
Cewar Yaya Farook.
     Fadwa ta naji tana gani aka sake tsira mata wani allurar, Sai da aka gama sannan Yaya Farook ya zaunar da ita.
      "Yanzu Zaku iya tafiya ' but saika dan rike ta saboda akwai Allurar da akayi mai sanya jiri.
Ok kawai Yaya Farook ya ce ' sannan Ya rike hannun Fadwa suka fita daga wajen ' daker Fadwa Take jan kafar ta Yaya Farook ya lura da haka,
       "Zaki daga kafa kimin sauri Ko saina dauke ki tukunna?
  Dago kai tayi ta kalleshi a gala baice ,
      "Yaya Farook bazan iya bane!
  Bata gama rufe baki ba ' taji ya dauketa cakk tamkar wata jaririya, Fadwa Kara lafewa tayi a jikin shi don kuwa batada wani karfi a jikinta.
      Haka ya ratsa cikin Hospital din da Fadwa a hannun shi ' mutane kuwa sai kallon shi sukeyi, kai tsaye ya nufi wajen Motar shi yasa key ya bude sannan ya zagaya ya saka Fadwa A seat din baya,
      "Saura kuma ki 'ki kwanciya.
Abinda ya fada kenan sannan ya shiga mota yaja suka koma gida A cikin *30* *Minutes* .
    Horn Yaya Farook ya yiwa Maigadi yazo ya bude ' tukunna ya karasa ciki. Packing yayi cikin hanzari ya fito gami da Jan hannun Fadwa,
     "kokarta ki fito don Yanzu dai ' nima nagaji bazan iya Daukanki ba don nauyine dake!.
Jin haka yasa Fadwa taja jikin ta fito daga motar cikin sanyin jiki, har suka shiga cikin parlor ' A zaune suka Iske *Ilham* tana Danna waya, Ganin su Yaya Farook ne yasa tayi saurin sake wayar a riga.
      "Ina Umma?
Cewar Yaya Farook.
      "Tana Sashen ta,
      "Tor ki kawowa Fadwa Dinner dinta yanzu taci a gaba na.
   Cikin hanzari Ilham ta tashi ta nufi Kitchen,
      "Ke kuma bazaki sami waje ki zauna bane kokuwa?
Cikin sanyin jiki ta zauna ' Gami da kallon kasa, don batamaso su hada Ido dashi.
Cikin dan kan kanin lokaci Ilham ta dawo da plate a hannun ta, Jellof rice ce a ciki sai naman kaza cinYa daya.
  Fadwa ansan abincin tayi tare da toshe hanci '
      "Aiko zaki amayar da Hanjin cikin kine ' saikin cinye abincin nan tass, bakina wani toshe hanci ba.
cewar Yaya Farook,
   Tun da ta ansa abincin ' sai kollon shi takeyi, takasa sawa abaki. Ganin haka ne Yaya Farook Ya Ansa abincin daga Hannun ta tareda diban spoon daya,
     "Oya Ansa ' dakaina zanba ki ' kinayin Amai kuma kiji saukan duka.
    Ba musu Fadwa ta bude bakin ta Yasa ka mata Abincin ' daker ta iya haddiyewa. Ilham na tsaye a wajen Ta na kallon su ' Dukka dukka Spoon uku kawai Ta ci, ta fara Kakarin Amai ' Bata Ankara ba Taji saukan dundu tiim Abayan ta haka yayi Dai dai da Shigowar Umma Parlon,
      "Subhanallah ' Wai kai Farook mekakeso ka maida kanka? Mugu ko mene?
   Umma zuwa tayi taja hannun Fadwa, ta zauna a kusa da ita.
      "Ya jikin naki?
Cewar Umma.
      "Umma da sauki ' Amma Umma na koshi da abincin haka bacci zanyi.
    Kai Umma ta daga mata tare da cewa,
      "Shikenan, *Ilham* rike ta ku tafi daki.
  Hannu *ilham* ta kamama *Fadwa* sannan suka tafi daki.    Yaya Farook kallon wristwatch din hannun shi yayi yaga ' 9:20pm dare yayi sosai, sannan ya maida kallon shi wajen Umma.
      "Umma sai da safe , ni zan kwanta.
     "To Allah ya tashemu lafiya!
A tare suka tashi kowannen su ya wuce sashen shi. yaya Farook na shiga daki ya cenja kayan jikin shi zuwa na bacci, sannan ya Haye gado tare da ciro Wayar Fadwa a drower gado ' ya shiga Gallery ya fara kallon pictures dinta inbanda smilling babu abinda yakeyi, Cen sai ya cikaro da wani hoton da tayi itada wani namiji A School ta dafa shi. Nan fa Zuciyar shi tafara mai radadi da zafi,.
     "Allah ya kaimu gobe saikin Fadamin Uban waye wannan.
   Ya na gama fadin haka jefar da wayar a kasa, Daker ya iyayin bacci a wannan lokacin.

*Washe* *Gari*  *Around* 4:00am
   Yaya Farook Ya tashi ya wuce masallaci, Bayan ya dawo ne ya koma bacci.
    Wajen 6:30 *Ilham* ta shi ' tashiga bathroom tayo Alwala sannan ta tada *Fadwa* daga bacci,
     "Fadwa tashi muyi Sallah ' kada lokaci ya kure.
Cikin Magagin bacci ta tashi tafada Bathroom ita tayi Alwalan tukunna ta fito suka yi sallah, Bayan sun sallame ne Fadwa taga Ilham ta haye gado tare da Lullube wa.
     "Ilham bazaki je School bane yau?
     "Eh ' saboda bakida lafiya konaje school din bazaimun dadi ba.
    Murmushi kawai tayi sannan ta mike tsaye tare da cire hijjab dinta,
      "Allah yasa Yaya Farook ya gane cewa bazakije School ba.
     Nan take ilham taji cikin ta ya murda,
      "insha Allah haka bazata faruba.
  Fadwa hayewa gado tayi ' bacci yayi awon gaba da ita. Basu suka tashi ba sai wajen 7:30, koda suka tashi Ilham kitchen ta shiga domin hada Breakfast. Yaya Farook ' farkawa yayi daga Bacci yashiga bathroom yayi wanka ya fito sannan ya  shirya ' ya fita siyowa Fadwa Magungunan ta, Ba shiya dawo ba saida aka gama hada breakfast sannan ' Yana shigowa parlor ya iske su Umma a dinning suna shan tea.  
   Karasawa wajen yayi yasami waje ya zauna ' sannan ya gaida Umma cike da ladabi, Bayan ta amsa ne ya maida kallon shi akan Fadwa.
     "Idan kingama breakfast din ' kizo Ki sameni a daki Kisha magana.
   To kawai tace ' sannan Ya dauki tea dinshi ya sha, Yana gama wa ya mike tsaye gami da cewa.
     "kiyi ki gama Kizo ina jiranki ' don akwai inda zanje,
     "To wai Shi maganin dole saikai ne zaka bata?
Cewar Umma.
     "Eh Umma ' Saboda Batason magani.
  Yana fadin haka ya juya ya wuce dakin shi, Ita kuwa Fadwa Hankalin ta atashe yake ' Cikin Zulumi ta ajiye cup din da ke hannun Ta tashi ta bishi Dakin.






*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
👄👄👄😜

BABBAN GIDA complete Where stories live. Discover now