page 69-70

6.4K 214 1
                                    

*BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
      馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮

*_Pure Moment Of Life writers_*

漏 '''Written'''聽聽 聽 聽
       By
*_Seemaluv_*馃憚

www.Seemaluv.wapka.me


                     *69-70*

  Tana shiga suka had'e da Yaya Khaleel yana k'ok'arin fitowa.
     "Baby nah?."
Ta d'ago kai ta kalle shi ' sam ta kasa b'oye damuwar da ke bayyane a fuskar ta.
     "Yanzu na dawo daga masallaci ban ganki ba."
     "Amm...Eh naje wajen su Umma ne." 
  Ta fad'i haka tare da k'arasawa ciki ta nemi waje ta zauna, Shima kusa da ita ya zauna yana kallon ta.
     "Baby nah! Are you alright?  Ko dai jikin ne?."
     "No! Babu komai Sweetheart ' gajiya ce kawai."
     "Ok ' to yanzu muci abinci tukunna ko?"
  Kai Fadwa ta d'aga mashi alaman to, Sannan ta tashi gami da rik'e hannun shi suka nufi dinning table.
   Sai da ya zauna tukunna ta juya ta wuce kitchen don d'auko abincin, Bayan ta fito daga kitchen d'in ne rik'e da tuwo da miya a hannun ta ' ta ajiye zata koma d'auko plates Yaya Khaleel yayi saurin rik'e mata hannu.
     "Baby nah! Dawo ki huta haka nan ' ni sai inje in d'auko sauran kinga ba kyajin dad'i.
     "No Sweetheart bara kawai in k'arasa ladar tawa."
     "A'a kema kinsan bazan bari ba ' so kawai ki hak'ura ki dawo ki zauna."
  Murmushi ta sakar mashi ' hakan yasa shi jin dad'i sosai, Ya tashi yaja mata kujera ta zauna ' tare da cewa.
     "Yawwa Baby nah!."
Tukunna ya juya ya wuce kitchen d'in Fadwa ta bishi da kallo cike da murmushi.
  Bai wani b'ata lokaci ba ya dawo parlor rik'e da plates a hannun shi da sarving spoon & spoon, Bayan ya zauna ne ' ya zuba tuwo da miyan a plate d'aya, Sannan ya fara kaiwa bakin shi.
     "Ummm.... Yummy! Ashe dai na iya miya."
  Da sauri Fadwa ta harare shi ' tare da turo baki.
     "Na iya miya dai! Bayan kai burkawa kawai kayi? Kuma ma duk ka zubarmin da miyan!."
     "Oho dai! Ai dai akwai hannu na aciki ko? To oya bud'e bakin."
Babu musu Fadwa ta bud'e baki ya fara feeding d'inta ' yana yi yana sawa a bakin shi shima, Sai da ya tabbatar ta k'oshi tukunna ya kyale ta.
     "Baby nah! Nidai ban k'oshi ba tukunna sai na cinye tuwon tass."
     "To ai gaka gashi ' daman don kai nayi shi ai Sweetheart, Kaga kuwa ai baza'ayi maka rowan shi ba."
     "Baby nah ' kinsan mene ne? Gobe insha Allah zan kaiki hospital a dubamin lafiyar ki ' daga nan sai inkaiki saloon d'in ko?."
     "To shikenan Sweetheart ' Allah ya kaimu."
  Fadwa tashi tayi zata wuce d'aki ya tsaida ita.
     "Ina kuma zakije?."
     "Sweetheart ' rigar bacci zan sanya, zafi duk ya isheni."
     "Haba Baby nah! duk da AC d'in nan?, Kuma ma aida kin bari sai anyi isha'i tukunna."
     "Ok to bari ind'an watsa ruwan sanyi."
  Fadwa d'akin ta tashige don yin wanka tukunna Yaya Khaleel ya had'a komai na wajen ya kai kitchen.
    bayan ya dawo ne ya koma harabar parlor ya zauna, Nan wayar shi ta fara k'ara ' cikin hanzari ya cire ta daga aljihun shi ya duba, Ganin Lubna ce ke kiran shi yasa yayi rejecting call d'in cikin fushi ' tare da jan tsaki.
   Lubna sake kiran shi tayi ' ganin zata dame shine yasa ya d'aga wayar.
     "Wace irin mace ce ke?."
Daram taji gaban ta ya fad'i.
     "Ni mace ce wacce ' mukayi rayuwa tare kuma muke k'aunar junan mu."
     "Lubna meyasa baki da tunani? for God sake ' bazaki kyaleni inyi rayuwa ta ba.?"
     "Khaleel ni kake fad'awa haka? Ni ce fa Lubna! Kana so kace min zaka watsar dani kenan?"
     "Eh inaso ne kema kije ' kiyi aure ki hutawa rayuwar ki, Lubna kid'au ka rayuwar da mukayi a baya munyi ta ne a bisa kuskure ' kuma yanzu ne yakamata mu fara istigfari."
     "Am i dreaming?."
Ta fad'a cikin rawar murya ' tamkar zatayi kuka.
     "No you are not! Lubna ina cikin kwanciyar hankali da mata ta ' and i love her so much, Please try to understand ko dama cen kece kika cusa mun sonki ' tun banaso har kika saba min."
     "No!!! Stop it please! I have had enough ' Khaleel zan so mu had'u face to face, Don wallahi ban yarda wad'an nan kalaman daga bakin ka suke fitowa ba..."
   Ta fad'i haka cikin kuka mai tab'a zuciya, Haka yasa yayi saurin kashe wayar ' gami da cilla wayar saman kujera.
  Yaya Khaleel mik'ewa yayi da niyyar  shiga d'aki yaga Fadwa a tsaye tana kallon shi.
    "Baby nah ' har kin fito wankan ne?."
Da sauri Fadwa ta k'arasa ta rungume shi ' cike da jin dad'i, Shima matse ta yayi da hannun shi.
    "Sweetheart ' naji dad'i sosai! Hakane ya nuna min cewa lallai kana so na."
  Bubbuga bayan ta yakeyi a hankali ' tukunna ya rabata da jikin shi suka zauna."
    "Baby nah! Kiyi hak'uri da abunda ya faru a baya ' tabbas munyi zaman haramun da bid'ala tsakani na da Lubna, Yanzu ne ya kamata mu gyara kuskuren mu ' and am willing to do anything just to make you happy!."
  Fadwa pecking d'in shi tayi a kumatu馃槉, Sannan ta koma ta lafe a jikin shi.
    "Thank you Sweetheart ' Yaya Khaleel d'ina na kaina!."
  D'an ture ta yayi kad'an, Hakan yasa ta d'ago kai ta kalle shi.
    "Bana ce ki daina cemin Yaya ba? Ai gara ki kira ni da Khaleel d'in ma."
     "Ahhh! Haba ba ba ba...wane ni? Babu girma kenan Sweetheart."
  Murmushi yayi ' tare da d'ago fuskarta zaiyi kissing d'in lips d'in ta tayi saurin mak'ale bakin.
     "Meye haka kuma?."
Girgiza mashi kai kawai tayi ' tare da bazo mashi idanu.
     "Wannan d'in ma? A'a baki isa ba kuwa!."
  Nan ya fara mata cakulkuli ' ta fara ihu cikin dariya, Ganin tana neman sik'ewa ne yasa tayi saurin cewa.
     "Ahh ahaha!.. Sweetheart ' wallahi ji nayi an kira sallah shiyasa, Kaje Mosque kada alwallar ta karye."
     "Kin sha! Amma ki bari in dawo ' sai bakin ki yayi tsini."
  Tashi yayi ya fita zuwa masallaci ' idon ta na kanshi har ya fice bata daina murmushi ba.
     "Huh! Allah na gode maka ' daka misanya min da Yaya Khaleel, Wanda a yanzu shi kad'ai kawai zan iya kallo inji sanyi a raina."
  Tana gama fad'in haka ta tashi ta wuce d'akin ta ' har ta sanya hijab sai kuma ta cire.
     "Anya? Alwallar nan bata karye ba? Bari dai kawai in cenja wata."
  Bathroom ta fad'a tayo alwala tukunna ta fito ' ta sanya hijab d'inta ta tada sallah.
   Bayan ta idar ne ' ta mik'e gami da cire hijab d'in, Sannan ta nufi madubi ta jawo kwalbar turaren  nan ' ta zuba a tafin hannun ta tukunna ta mutsits-tsika shi ta shafa a jikin ta.
   Fadwa sai da tabi ko ina na jikin ta ' ta shafeshi tass da turare, Tukunna ta bud'e wardrope ta ciro rigar bacci 'yar k'arama dai dai gwiwa ta sanya.
   Sai da ta gama shirya wa ' sannan ta fito parlor kai tsaye taje ta kunna TV ta dawo ta zauna, Bata dad'e da zama ba Yaya Khaleel ya dawo daga masallaci ' sallama yayi Fadwa ta d'ago kai ta kalle shi tare da amsawa.
    "Sannu da dawo wa!."
Ta fad'a tare da mik'ewa tsaye zata nufi kitchen.   
    "Duk ki gama rara gefen ki ' yau bazaki iya k'watar kanki ba."
  A tsora ce ta juyo ' ta kalle shi tare da yin innocent face.
    "Sweetheart kana magana ne?"
  Sai da ya sami waje ' ya zauna sannan ya ce.
    "A'a da kaina nake magana!."
Yaya Khaleel ya fad'i haka tare da watso mata wani irin kallo, Fadwa juyawa tayi ta wuce kitchen d'in gaban ta na d'ar d'ar, Fridge ta bud'e ta d'auko roban youghout mai sanyi ' sannan ta juya ta dawo parlor tayi zamanta suka fara kallon kallon.
    "Baby nah ' inzo ki bani?."
A tsora ce ta kalle shi ' don tasan ba komai ke jan shi haka ba, Illa turaren da ta sanya.
    "Ko bazaki bani ba?."
Fadwa kasa magana tayi ' sai dai ta tsinci kanta da girgiza mashi kai.
  Murmushin mugunta Yaya Khaleel yayi ' tare da mik'e wa tsaye yana takowa a hankali inda take zaune, Hakan yasa Fadwa tayi wuff zata tashi gudu ' ya dank'ota da hannu d'aya.
     "Sweetheart bacci nakeji.?"
Waro idon shi yayi' cike mamaki.
     "Bacci? Haba! Aiba yanzu ba tukunna."
  Juyawa yayi ' yaje ya sanya key a k'ofa, Sannan ya dawo ya d'auke ta cak tamkar wata baby ' yayi d'akin shi da ita a hannu.
   Yaya Khaleel a saman gado ya a jeta ' tare da cewa.
    "Ki fara addu'o'i kafin in kashe TV in dawo."
  Had'iye miyau Fadwa tayi da kyar don kuwa duk tsoro ya gama cika ta ' sannan ya fice, Bai wani b'ata lokaci ba ya dawo ' a zaune ya iske ta kanta  a sunkuye.
  Yaya Khaleel k'arasa wa yayi kusa da ita ya zauna ' ya fara sunsunar ko ina na jikin ta, ganin hakan ba zaiyi satisfying d'inshi bane yasa shi kwantar da ita saman gadon ' sannan shima ya haye.
   Fadwa hannu biyu tasa ta tallabo fuskar shi ' cikin sanyin murya tace.
    "I love you so much ' Sweetheart..."
    "love you more Baby nah..."
Ni *Seemaluv* hannu naga Yaya Khaleel yasa ya kashe wutar d'akin, Hakan yasa na tattara 'yan komatsai na ' na koma parlor na yada zango kafin gari ya waye.


*Dedicated To My Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣

BABBAN GIDA complete Where stories live. Discover now