*BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 '''Written'''聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚www.Seemaluv.wapka.me
*#IG:* *_@Bae_Seema鉂**_@Today my dedication goes to Khadija Kabeer Yunusa(thank u for the covers)you're such a great fan in any way, Sadnaf(鉂�) & Aisha Garkuwa(鉂�) luv u..._*
*Haba waya ce na manta da JAMEESHA?馃槙, kina raina**83-84*
Bayan ya fara bacci ne ' Yaya Farook ya shigo cikin ward d'in, ya same ta rungume da kan Yaya Khaleel a cinyar ta.
鈥淎mm... Fadwa ' bara inje in maida su Umma gida, Sun ce suna da b'ukatar suje su shirya ' sannan su d'an yo abinci.鈥�
鈥淭o sai kun dawo鈥�.
Abinda ta ce kenan ' ta maida kanta ga kallon fuskar Yaya Khaleel, Shi kuma Yaya Farook ya juya ya wuce.
*AROUND 2:00PM*
Su Umma suka dawo cikin hospital d'in ita da Ilham sai kuma Yaya Farook da yake shine ya tuk'o su.
Ilham rik'e take da cooler d'in abinci a hannun ta, Cikin ward d'in suka shigo cike da sallama ' suka iske Fadwa a tsaye tana lek'e ta window.
Sallamar su da taji yasa ta waigo ' ta kalle su gami da amsa sallamar.
鈥淪annu Umma鈥�.
Cewar Fadwa
Cike da fara鈥檃 a fuskar ta.
鈥淵awwa Fadwa 鈥� har yanzu bai tashi ba?鈥�.
鈥淓h Umma ' ina ganin sunyi mashi allurar bacci ne鈥�.
鈥淗aka ne鈥�.
鈥淜e ni kizo 鈥� ki rabani da abincin nan, Na gaji鈥�.
Cewar Ilham.
Murmushi Fadwa tayi ' sannan ta matsa kusa da ita, Ta ansa ta aje a k'asa.
Umma ce taja kujerar dake wajen ta zauna ' ta tsaya tana kallon fuskar Yaya Khaleel.
Suna cikin hakane Yaya Khaleel ya farka daga bacci ' a hankali ya bud'e idon shi ya fara saukewa akan Umma, Sannan ya tashi zaune.
鈥淪annu da tashi鈥�.
Cewar Fadwa.
鈥淵awwa鈥�.
鈥淪annu Khaleel ' yaya jikin naka yanzu?鈥�.
Cewar Yaya Farook.
鈥淒a sauk'i bro鈥�.
Umma ce ta lura da drip d'in da aka sa mashi ya kusa k'are wa, Hakan yasa ta umarci Yaya Farook da yaje ya kira nurse don tazo ta cire mashi.
Haka Yaya Farook ya fita ' ba tare da wani b'ata lokaci ba suka dawo tare da nurse d'in.
Nan ta cire drip d'in sannan ta cire cannula d'inda ke jikin shi, Tare da cewa.
鈥淵au insha Allah ' za'ayi discharging d'inku, Doctor d'in yaje ya dawo ne ' amma kafin nan zan kawo warm water ingasa mashi jikin shi鈥�.
鈥淥k ' ba damuwa ai鈥�.
Cewar Yaya Farook.
Haka nurse d'in ta juya ta wuce ' sannan Fadwa ta zuba ma Yaya Khaleel ruwa a cup, Ta mik'a mashi.
鈥淣asan baza ka rasa jin k'ishi ba ko?鈥�.
Murmushi kawai yayi mata ' tukunna ya ansa ruwan yasha, Sannan ya mik'a mata cup d'in ta ajiye.
鈥淯mma ' akwai maganar da nakeso muyi nidake tun d'azu mantawa nayi bamuyi ba鈥�.
Cewar Yaya Farook.
鈥淚na jinka Farook ' fad'i kawai鈥�.
鈥淯mma ' daman family d'in Safeena ne suka matsa, Akan lallai in tura magabata na nan da kwana uku鈥�.
鈥淭o Farook ' insha Allah za'a tura abubuwan ne suka zo mana a hard'e, K'arshen tama had'a ku za'ayi dakai da Ilham ayi shi rana d'aya鈥�.
Jin hakan yasa murmushi ya sub'uto wa Ilham, Tayi sauri ta rufe bakin.
鈥淭unda kaga auren Ilham ' yau saura kwana 5, To kaga kawai gwara a tura gobe a sanar musu ' don su shirya鈥�.
鈥淗aka ne Umma鈥�.
Suna cikin wannan maganar ne nurse ta shigo ciki ' rik'e da bucket d'in ruwan d'umi, Fadwa tana ganin ta tayi wuf ta mik'e tare da cewa.
鈥淏ara in gasa mashi jikin ' am his wife, so don't bother to鈥�.
Nurse d'in mik'a ma Fadwa k'aramin towel d'in tayi, Sannan ta juya ta wuce.
Nan Fadwa ta fara gaggasa mashi jikin shi a hankali ' tana daddanna mashi wajen da yaji rauni da towel, Bayan ta gama ne Ilham ta zuba mashi abinci a plates ta mik'a mashi.
Yaya Khaleel ansa yayi ya fara cin abincin ' cikin sauri hakan yasa Fadwa tsaya wa tana kallon shi, Cike da murmushi.
Yana cikin cin abincin ne Doctor ya shigo cikin ward d'in nasu, Gami da yi musu sallama.
Dukkansu a tare suka ansa sallamar ' tukunna likitan ya mik'awa Yaya Farook hannu suka gaisa, Sannan ya juya kan Yaya Khaleel.
"Gaskiya sauk'i ya samu Alhamdulillah".
Likitan ne ya fad'i haka tare da juyowa ya kalli Umma.
"Amm...Bayan ya gama cin abincin ma ' zaku iya tafiya gida, Insha Allah ba wani problem".
"To Alhamdulillah".
Cewar Umma.
Doctor har ya juya zai fita ' Yaya Farook ya tsaida shi, Da cewa.
"Doctor nawa ne charges d'in mu?".
A hankali likitan ya juyo ya kalle shi ' d'auke da fara'a a fuskar shi.
"Haba! Aini baka sanni bane ' amma ni na sanka, Abban ku ya taimake ni a rayuwa ' saboda haka kuje babu komai zan iya yin fin hakan, Ai daga *BABBAN GIDA* kuke".
Murmushi gaba d'ayan su sukayi ' sannan likitan ya juya ya fita, Yaya Khaleel ya ajiye abincin a gefen sa tare da cewa.
"Umma nina k'oshi haka nan, Mu tafi gida don na k'osa ingan ni a gida".
Dariya suka sake kwashe wa dashi ' sannan Ilham ta d'auki plate d'in abincin ta maida cikin cooler, suka fara haramar barin cikin hospital d'in.
Su Yaya Khaleel ' bayan sun fito daga hospital d'in ne suka shiga mota suka koma gida.
*A TAK'AICE...*Haka Fadwa ta cigaba da kulawa dashi har na tsawon kwanaki uku ' har Yaya Khaleel ya samu cikakken lafiya.
Abba da Yaya Farook kuwa ' maida Safeena sukayi cen Bangladesh, Abba ya tsaya ya nema ma Yaya Farook auren ta.
Acen aka d'aura auren Yaya Farook da Safeena , Sannan su Abba suka dawo gida nigeria ' Kafin gobe a kawo wa Yaya Farook matar shi.
B'angaren Ilham kuwa ' zaune take a d'akin ta tare da Fadwa sai kuma k'awaye birjit a d'akin, Ado kawai ake cab'awa Ilham ' cikin jajayen riga da skirt .
"Allah sarki Ilham ' gwara ni ina tare da su Umma, ke kuwa Al'ameen zaizo ya d'auke ki zuwa wani gida".
Nan hawaye suka fara cicciko ma Ilham a ido ' dakewa tayi ta cigaba da kallon mirror ana mata makeup, Fadwa ta cigaba da cewa.
"Kuma sai da yardar shi ' zaki zo kiga su Umma da Abba dani kaina...".
Nan Ilham tayi sauri ta mik'e tsaye hawaye na sauko mata a fuska.
"Please Fadwa stop it ' bana so, kinyi alk'awarin bazaki sani kuka ba fa!".
Cikin rawar murya Ilham ta k'arasa maganar, Hakan yasa Fadwa ta rungume ta ' cike da tausayi da bege.
"Am sorry sis ' na daina kinji so ki bar kukan".
Nan Fadwa ta zaunar da Ilham ' ta cigaba da facing d'in madubi, Sannan ta zari tissue ta share mata hawaye.
Fadwa kallon wristwatch d'in hannun ta tayi, Taga 3:56pm.
"Ilham lokacin tafiya KAMU d'in nan ya kusa".
Fadwa juyawa tayi ta sanar wa k'awayen amarya, domin su kasan ce cikin shiri.
"Ilham bari inje ind'an sake gyara jiki na ko".
Kai kawai Ilham ta d'aga mata alaman to, Sannan Fadwa ta juya ta nufi sashen ta.
Fadwa ko da ta isa sashen ta ' a zaune ta iske Yaya Khaleel , cikin manyan kaya Farar shadda, rik'e da laptop d'in shi a hannu.
K'arasa wa inda yake tayi d'auke da sallama a bakin ta, Ya amsa mata ' sannan ta shige jikin shi.
"Sweetheart ' kayi kyau sosai Allah".
"Thank you Baby!".
Tare da manna mata kiss a goshi ' ya cigaba da kallon laptop.
"Wai meye ne ' a cikin laptop d'in, Ni ka bani hankalin ka nan".
Smilling yayi mata ' sannan ya rufe laptop d'in.
"To Baby nah ' gaba d'aya na tattara maki hankali na, Na baki".
Fadwa manna kanta tayi a k'irjin shi, Tana wasa da mab'allen rigar shi tace.
"Sweetheart ' zanje KAMU d'in Ilham, Dama kasan ya zama dole inje ko?".
"A'a bai zama dole ba! Baby nah bana so ko wane tom and jerry ya kallan mun ke, So ki hak'ura kawai ' dama yau inason jin d'umin jikin mata ta".
Nan Fadwa tayi tsumu tsumu da fuska ' ta turo baki, zata zame jikin ta kenan ya rik'eta, Ya cigaba da cewa.
"Baby nah ' inason yara please ki bani yara, kinji".
Ya fad'a tare da shafa ruwan cikin ta, Fadwa kuwa gaban ta dukan uku uku yake.
"Sweetheart ' bara inje in fad'a wa Ilham su tafi kawai kar su tsaya jira na".
"A'a yi zaman ki, bari in kira ta a waya".
"A'a karka kira ' ni dai kabarni inje in same ta, in ba haka ba akwai matsala".
Ok kawai ya ce ' sannan Fadwa ta tashi ta fita, Tana fita suka had'e da Ilham da k'awayen a harabar garege da alamun ita suke jira.
Da hanzari Fadwa ta k'arasa inda Ilham take.
"Amm. Ilham kin san ' yaya za'ayi? Ku fara tafiya kawai, Yayan ki ya sani abu ne ' inhar na gama da wuri zai kawo ni".
"To amma please Fadwa kizo da dawuri ' karki dad'e".
To Fadwa tace ' sannan Ilham suka shige mota, Motaci uku sukayi amfani da ita a ranar.
Fadwa sai da ta tsaya ta ga wuce warsu ' tukunna ta juya ta koma sashen ta.
Tana shiga ta iske shi ' har ya cire manyan kayan shi, Ya zauna daga shi sai singlet sai boxer ' murmushi ta d'an mashi sannan ta fiske zata wuce wuce d'aki.
"Baby nah?".
A hankali ta juyo ta kalle shi ' sannan ya yi mata sign da ido cewar tazo nan, Hakan yasa Fadwa d'aga kafad'ar ta d'aya tare da cewa.
"Um um".
Waro idanu Yaya Khaleel yayi ' tare da yunk'ura wa.
"To ni bara in taso".
Fadwa zabura tayi ta kwasa a guje zata shige d'aki yayi saurin taran gaban ta.
"Oh ashe kin iya gudu haka!".
Kafin ta bud'e baki tayi magana ya sunkuce ta ya sab'a ta a kafad'a, Ya nufi d'akin shi da ita.
*DEDICATED TO MY FAN'S*
馃憚馃憚馃憚
