*BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 '''Written'''聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚www.Seemaluv.wapka.me
*#IG:* *_@Bae_Seema鉂**77-78*
Fadwa wuf tayi ta mik'e tsaye cike da mamakin shigowar ta cikin gidan.
"Me ya kawo ki gidan nan?."
Fadwa ta fad'a tana share hawayen da ke fuskarta, Kallon uku saura kwata Lubna ke mata ' hakan yasa Fadwa k'arasa wa har gaban ta, Ta d'aga hannu ta sharara mata mari a fuska.
A gigice Lubna ta dafe fuskar ' cikin wani irin k'ara.
"Ahhhhgh."
Nan Ilham ta taso tazo ta rik'e Fadwa, Su Ige da Yaya Farook tasowa sukayi sukai kansu.
"Ke baki da hankali ne? Ya zaki mare ta haka? ' ku bari muji da d'aya mana!."
Cewar Yaya Farook.
"Kad'an ma ta gani wallahi ' inda ba'a raba ba kashe kine kawai bazanyi ba, Banza kawai karuwa mai bin mazajen mutane."
Nan Fadwa ta sakeyo wani kukan kura ' zata sake marin ta Yaya Farook ya rik'e hannun.
"Meyasa ba kyajin magana ne waike! ' ashe b'atan mijin ki ma bata dame kiba kenan?."
Fadwa fincike hannun ta tayi daga nashi ' ta maida kallon ta kan Lubna, Wacce har yanzu rik'e take da fuska ' Umma da Abba kuwa suna gefe a zauna abun duniya duk ya ishe su.
"To kwartuwa! Ai saiki fad'i abunda ya kawo ki."
Safeena ce taja hannun Fadwa ' suka koma suka zauna.
"Haba! Fadwa ' ai fad'a ba naki bane yanzu."
Wata harara Fadwa ta watsama Safeena ' aiba arzik'i ta fita harkar ta.
Yaya Farook da Ilham ' suma komawa sukayi suka zauna.
"Baiwar Allah ' muna sauraron ki."
Lubna k'arasa ciki tayi ' ta sami waje ta zauna, Sannan ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya.
"Nidai suna na Lubna ' kuma ni budurwar Khaleel ce ada, Yana sona kuma nima inason shi."
Had'a ido sukayi da Fadwa ta kalle ta ' ta watsar sannan ta cigaba da cewa.
"Wato a tak'aice dai nazo ne akan maganar kidnapping d'in Khaleel da akayi.
Nan Umma da Abba ' suka mik'e tsaye a tare suka ce.
"Kinsan inda yake ne?."
"Yes ' har mutanen ma nasani."
Gaba d'ayan su mik'ewa tsaye sukayi, Idanun Fadwa kyar akan Lubna.
"Baiwar Allah su waye? Ki fad'a mana don Allah."
Cewar Umma.
Nan Lubna ta kwashe duk abinda ya faru ' ta fad'a masu.
"Kun gani ko? So take ta raba ni da miji na ' duk abinda ya faru da miji na itace sila, Don Allah ku barni inyi k'asa k'asa da ita anan wajen."
Fadwa ta fad'a haka cikin kuka.
"Umma don Allah ku zazzauna abi komai a hankali."
Cewar Yaya Farook.
Bayan sun zauna ne ' Yaya Farook yace.
"Yanzu ke basu fad'a maki inda suke a b'oye ba?."
"Basu fad'amun ba ' amma idan na nemi nasan hakan wannan abune mai sauk'i."
"Lubna ko?."
Ta d'aga mashi kai alaman Eh, Sannan ya ce.
"Zamu so ki taimake mu akan hakan ' don nasan dama taimako ne ya kawo ki."
"K'warai kuwa, Amma kasan cewar yanzu dare yayi *8:30pm* zamu bari sai gobe da safe ' don zanje gida yanzu."
Yaya Farook zaiyi magana kenan ' Fadwa ta tari numfashin shi.
"Mtsw! Wai don kinga ana neman taimakon ki? ' ko kuwa don miji na ne?, Idan da mijin kine fisabilillahi ya zakiyi?."
"Fadwa ' can't you be patient? Zamu iya jira har goben muddin wani abu bazai same shiba."
Cewar Abba.
Fadwa shuru tayi ' idanuwan ta na zubar da hawaye.
"Lubna zaki iya tafiya ' Allah ya kaimu goben.!"
Lubna tashi tayi zata wuce ' har ta kai bakin k'ofa, Fadwa ta tsai da ita da cewa.
"Inaso ki sani cewa ' ni Fadwa wallahi bazan tab'a kyale ki haka ba, Saboda duk wannan abun da ya faru da miji na ' ke ce sila."
Lubna girgiza kanta kawai tayi ' tare da jan tsaki, Sannan tace.
"Da zakiyi ' hak'uri nima biki na saura kwana uku, So kinga kuwa babu abinda zanyi da mijin ki ' kawai zan taimaka maku ne don har yanzu akwai sauran tausayin sa a cikin zuciya ta".
Tana fad'in haka ta fice.
"Haba Fadwa! Bakya tunanin wad'an nan magan ganun zasu iya sawa ta cenja ra'ayin ta?.
Cewar Yaya Farook.
Banza tayi ta kyale shi ' tukunna yaja tsaki gami da cewa.
"Abba ' muje masallaci muyi sallah, don bamu sami magrib ba ' ga isha'i ma."
Ok Abba yace, Sannan suka tashi suka fita zuwa masallaci.
Bayan fitar sune Umma da Ige suka haura sama ' don yin sallah, Fadwa da Ilham da Safeena kuma ' d'aki suka nufa suma suyi nasu sallolin.
Bayan sun idar ne ' Fadwa ta haye saman gado, Ta sake dasa wani sabon kukan ' Ilham da Safeena suka shiga lallashin ta .
Ko da su Abba suka dawo cikin gidan ' kowa d'akin shi ya zarce cike da fargaban abinda gobe zata haifar.
Haka suka kwanta babu wanda ya sanya komai a cikin sa, Fadwa kuwa bacci? ai sai dai b'arawo.*** *** *** *** *** *** ***
*WASHE GARI*
Da sassafe Fadwa ta tashi ' ta riga kowa tashi, kai tsaye ta wuce sashen ta ' wai ko a tunanin ta zata ga mijin ta, Amma ko da ta shiga tsit taji ' babu motsin komai.
"Sweetheart?."
Ta fad'a kamar zatayi kuka ' haka ta shige d'akin shi ta fad'a bathroom tayo alwala, Sannan ta fito tayi sallah.
Bayan ta sallame ne ' ta tashi tsaye tana k'arewa d'akin kallo.
"Allah ka taimake ni ' Yaya Khaleel d'ina ya dawo lafiya."
Ta fad'i hakan gami da d'aga hannun ta sama.
Fadwa barin d'akin tayi ta dawo parlor ' tayi tsaye tana tuna irin wasan nin da suka rik'ayi tare da shi, Nan da nan k'walla ta ciko mata ido.
Hakan yasa ta barin sashen nata cikin hanzari ' ta nufi sashen su Ilham, Fadwa tana tafiya tana share hawaye ' ko da ta shiga iske Ilham tayi wajen dinning table tana jera cups d'in da za'a sha tea wato breakfast.
Wajen dinning table d'in Fadwa ta nufa ' taje ta zauna tare da sunkuyar da kanta k'asa.
"Fadwa in zuba miki tea d'in ne yanzu?."
Girgiza mata kai tayi ' tukunna Ilham ta sami waje ta zauna.
Umma da Ige ne ' suka shigo parlon suma suka zauna a wajen, Fadwa da Ilham suka gaishe su ' sannan Ilham ta zuba musu tea d'in su a cup ta ajewa kowa a gaban shi.
Bayan su Umma sun fara karyawa ne ' Yaya Farook da Safeena suka shigo parlon suma a tare suka ja kujera ' suka zauna, Kai zakace a d'aki d'aya suka kwana.
Safeena gaishe da su Umma tayi ' tukunna Ilham ta tsiyaya masu nasu tea d'in a cup ita da Yaya Farook, Safeena ta b'alli bread ta mik'a mashi shima ya b'alla.
"Aww! Ilham na manta ' zubawa Abban ku tea d'in shi a cup ki kai mashi."
Cewar Umma.
To tace ' sannan tayi yadda aka umarce ta.
Ilham bayan ta kaine ta dawo ' ta cigaba da breakfast, Yaya Farook lura yayi da Fadwa ' don tunda yazo baiga tana breakfast ba.
"Fadwa! Ke kin gama naki breakfast d'inne?".
Kai ta girgiza mashi ' tare da cewa.
"A'a bana jin yunwa."
"What do you mean by ' bakya jin yunwa? Come on ki zuba tea kisha."
D'ago kai tayi ta kalle shi ' idanuwan ta cike da hawaye.
"Yaya Farook kawai bana jin cin komai ne."
Zaiyi magana Umma ta dakatar dashi ' da cewa.
"Farook ' ka kyaleta , Ai tamayi k'ok'ari dole a d'aga mata k'afa don tana cikin damuwa!".
"Amma Umma ai ya kamata tayi breakfast ' for her own health".
Yaya Farook kallon ta yayi ' yayi k'wafa, Sannan ya tashi ya wuce d'akin shi ba tare da ya gama breakfast d'in ba.
Safeena kuwa kishi ya riga ya gama turnik'e ta yadda ya nuna damuwar shi akan ta sosai, Don kuwa ya riga ya bata labarin rayuwar shi ' da wadda sukayi tare da Fadwa a baya.
Hakan yasa Safeena jan tsaki ' tsakin da batasan zai fito fili ba, Da sauri Ilham ta kalle ta.
"Lafiya Safeena?".
"Me kika gani?".
"Tsaki kika yi!".
"Well.. am just worried about Farook's health too, Don ya tashi ba tare da ya gama breakfast ba."
"Oh! Ayya!."
Abunda Ilham tace kenan ' ta ajiye cup d'in hannun ta, Ta rik'o hannun Fadwa tana tausar ta akan ta daure tasha tea d'in ko kad'an ne.
Suna cikin haka ne ' sukaji anyi sallama, hakan yasa Fadwa yin saurin juya wa don taga waye.
Lubna ce ' a tsaye cikin pink d'in atamfa rik'e da wayar ta a hannu mai riga pink ' komai nata pink ta saka, Cikin hanzari Fadwa ta tashi ' ta k'arasa har inda take.*Dedicated To My Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槡
