page 28

3.4K 206 0
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨





💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )






Page2⃣8⃣



Asmah ana ta d'aukin zuwa makaranta, an gama shirin komai ranar kawai ake jira, ana gobe zata fara zuwa ranar sunday kenan, ranar ko bacci rabi da rabi tayi, wanda ma tayin cike yake da mafarkai kala kala na makaranta,  tun kan asuba ta tashi tayi alwalla tayi nafillfilu, ana kiran sallah ta tada nata, a gurguje taje sashen Abdallah tayi abunda ya dace kana ta dawo tayi wanka, sai lokacin da ta fito sannan mimi ta tashi tun asuba da ta koma, dariya tai ta ma Asmah tana fad'in JJC kenan wai har kin shirya, itama Asmah dariya tayi ta zura gogaggun uniform d'in ta bayan ta gama shafa mai, sosai uniform d'in suka amshe ta, nevy blue ne da white, wandon nevy blue ne dogo sai riga iya gwiwa fara, sai ko k'aramar hijab itama kallar wandon, sai bak'in covers masu kyau, cike da d'auki suka wuce makaranta, Na-irak'i yayi mata komai sannan aka kaita class d'inta JSS1D, seat d'inta aka kai mata kusa da wata yarinya mai d'an banza surutu, domin kuwa da suka shigo ajin muryarta kad'ai ke tashi a class d'in, ta hau kan chair d'inta tana ta masifa akan wai an sace mata home economics note d'inta, da yake lokacin teacher bai shigo ba, tana ganin class tutor d'insu ya shigo ta natsu, harara ya watsa mata domin ya gaji da punishing d'inta akan surutu a aji, ko wane teacher sai ya kai k'ararta akan hakan sai dai kuma duk surutunta, ba yadda zakai ka tambaye ta abu bata sani ba, shiyasa ma wasu ticocin suke shafa mata lafiya, class tutor d'insu yayi introducing Asmah a matsayin sabuwar d'aliba ga y'an ajin, sannan ya tafi saboda teacher d'insu ya shigo, itama Asmah mik'ewa tayi kamar yadda taga sauran d'aliban sunyi, sai da suka gaishe da malamin, ya tambaye su ya suke kana ya basu umarnin su zauna, ta lura tun zuwanta yarinyar kusa da ita ke ta kallonta, malamin na fita wani ya shigo, sai 11 akayi break, ana fita break yarinyar ta matso kusa da ita kamar dama jira take, mik'a mata hannu tayi tana fad'in "friends" tana washe baki, Asmah ma yak'e bakin tayi tare da mik'a mata hannu tana fad'in "sure", yarinyar tacigaba

"My name is Fatima Adam Waziri and u?"

"Am Asma'u Muhammad Maska"

Daga nan suka cigaba da surutansu, daga gani jininsu yazo d'aya dan in kaga yadda suke labari suna kwasar dariya kai kace childhood friends ne.


Fanin karatun masha Allah tana ganewa abunda ma bata gane ba tana tambaya, sannan in ta koma gida kuma lesson teachernta na coaching d'inta, k'awancensu da fatima zara kuma yayi nisa,  yanzu sun shak'u fiye da zato, komai na gida kuma na tafiya normal.

To masu karatu zakuji nayi shiru batun maganin da Auntyn yara ta amso daga hannun boka darb'usa, to bari na fad'an maku yadda akai, kamar yadda Jumman Jos ta mata kashedi kan kartaba Asmah wannan aiki, tayi da kanta, haka kuwa akai ita ta aiwatar da komai da kanta.





************    **********
Rayuwa Mai juyawa a yayinda lokaci ke tafiya,  rayuwa ta gungura su Asmah an gama Jss1 lafiya cike da d'umbin nasarori da sa'a, abubuwa da yawa sun faru cikin shekara d'ayan nan, ciki kuwa hadda cikar lokacin da aka d'ibar ma Abdallah na komawa asibiti, wato wata shiddan da aka d'ibar mai, sun koma sai dai tsuntsun bai canza shek'ar shi ba, Asmah taje hutu gidan auntyn Nafy ba k'aramin jin dad'in cigabar da ta samu sukai ba barin ma Marwan, kamar yadda itama Asmah tayi farinciki da wadatar data k'arun masu, an gama hutu, su Mimi da Nihal sun dawo daga hutun da sukaje gidan Aunty shaila.



Zarah duk yadda taso taje gidan su Asmah ko kuma ita tazo gidansu cikin hutun abun ya faskara, dole ta hak'ura wata rana, domin Asmah tace mata hutu zata, abunda Asmah bata gane bane shine ita Zarah duk tanayi ne don yayanta Aliyu, domin ya bayanar mata cewa yana son k'awarta ta, kuma ba k'aramin murna tayi ba dajin haka, kuma ta d'au aniyar zata cusa ma Asmah sonsa a zuciya, ta riga tasan halin yayan nata da wuya kaji yace yana son mace, shiyasa da ya gaya mata yana son Asmah ba k'aramin dad'i taji ba, shiyasa taso ayi komai a cikin hutun amman abun ya faskara,  shiyasa duk ta k'agara a dawo hutu, wannan kenan.



***** ******   ****

An dawo hutu lafiya su Asmah an zama y'an JSS2, zaune suke a class suna jiran mathematics teachern su, Zarah ce ta kulle littafinta wanda take dubawa ta kalli Asmah da itama ta dage tana ta duba nata ittafin,  zarah tace "Asmah tun tuni ina ta maki magana kinyi shiru, wallahi ya Aliyu ya damu yaji wani abu daga gareki, wallahi ni har tausayi yake ban, nasan abunda kika fad'a gaskiya ne, na cewa karatu ne a gabanki, kuma baki so ki kunyata su Ammie, ay nasan da haka kuma nima karatun ne a gabana, sai dai abunda kawai nake so dake kibashi dama kuna gaisawa, atleast dai bakiyi wulak'anci ba dan ba kyau wulak'anta maza, kuma ki sani bawai ina fad'an haka bane dan ya Aliyu yaya nane ba, a'a ina fad'ine a matsayina na k'awarki, wacce zata baki shawara, kuma ko dako ba ya Aliyu bane yace haka in dai yana da hankali kuma ba da wasa yazo ba, shawarar da zan baki kenan."

Asmah da tun fara maganar Zarah tayi shiru tana sauraranta,  ta rufe littafinta, ta maida kallonta da hankalinta kacokan kan k'awarta ta kana tace,

"Zaraaah! hak'ik'a duk abunda kika fad'a gaskiya ne, amman akwai babban dalilina nayin hakan, shiyasa kikaga kina bina da maganar ya Aliyu ina botsarewa, kar kiga kamar wulak'anci wallah ko d'aya, ai ya Aliyu ya wuce wulak'anci a guna, mutumin da ya d'auke ni kamar k'anwarsa ayi wasa ayi dariya, koma bama haka ba ni wane matsayi gare ni da har ya Aliyu da kansa yace yana sona ink'i amincewa, nima ina sonsa har zuciyata, sai dai ban iya yaudara ba kuma bazan fara akan ya Aliyu ba,  don wallah ban iya cutar d'an uwanki dan yadda nake jinki kamar shak'ik'iyar k'anwata."

Akimbo Zarah ta kama tare da turo baki tana fad'in "keeeee Asmah dakata kin dagula mun lissafi, bangane ba, kince kina son ya Aliyu, kuma kina wani zance baki son ki yaudare shi, ina kuma zance yaudara ya fito bani bayani, to Asmah ko dai an maki miji a gida ne? "

"Ko d'aya Asmah ba ayi mun miji ba, saidai akwai wani B'OYAYYAN AL'AMARI wanda ke kanki na b'oyewa, abunda ya shafi rayuwa tane, kuma danginku manya ne ba za suso had'a zuri'a dani ba"

"Hai Asmah duk kinsa kwakwalwata ta d'au caji, har kinsa gabana yana fad'uwa, koba maganar ke ba y'ar gidansu Mimi bace? ai nasan ko ba y'ar gidansu bace ai y'ar uwarsu ce ke duba da yadda kuke yanayi da Mimi"

"A'a hasashenki ba haka yake ba Zarah, hasali ma baki san matsayina a gidan ba, kuma baki san wace ni ba"

"Hmmmmmm ni dai ki fitar dani daga duhun da kika jefani dan Allah, duk kinsa............ "

"Good morning class,  sorry 4 d late coming,  actually i have a patient in d hospital"

Malamin maths ne ya katse masu maganarsu,  nan y'an aji aka d'au gaishe shi ana tambayar marar lafiyar da yace yana da a asibiti tare da jajanta mashi, sannan suka fara karatu, Zarah kam hankalinta nakan maganar da suke, sai ido take ma Asmah, wata guntuwar papper tayi rubutu akai ta mik'a ma Asmah ta k'asan benci, Asmah ta amsa ta bud'e, ga abinda ta gani

" _Asmah dan Allah ki rubuta mun wallah duk na k'agara inji"___

Itama ta maida mata da  _" Kai zarah akwai ki da rud'u, labari ne mai tsawo ki bari a fita break tukunnan"_  ta mik'a mata, bayan ta karanta ta d'aga kai alamun ta yadda a fita break d'in, sai lokacun ta bud'e littafinta ta soma rubutu, duk suka tattara natsuwarsu suka bama malamin, minti 40 yayi aka kad'a bell, da sauri Zarah ta figi Asmah sukai waje, wani wajen da suka saba zama in anyi break suka zauna.






A/N

It's what i've olwaix dreamed,  i neva thought i'd make it this far,  but now i knw dat i'll keep going forever insha Allah, All great thanks 2 u fans😍😍😘❣💘💝💞

👸🏼Queen bk🖊.....

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now