🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah🤜🤛 )Page5⃣1⃣
*TO ALLAH DO BELONG THE UNSEEN (SECRETS) OF THE HEAVENS AND* *EARTH AND TO HIM GOETH BACK EVERY* *AFFAIR ( FOR DECICION) THEN WORSHIP HIM,* *AND PUT THY TRUST IN*
*HIM, AND THY LORD IS NOT UNLIMITED OF AUGHT THAT YE DO.**WASHEGARI*
Asmah kamar yadda ta kwana da abun haka ta tashi dashi a zuciyarta, bayan rabin daren rayashi tai da addu'oin neman tsari, sai zagaye take a ɗakinta tana so ta gano mafita yanzu matsalar ta ɗaya taya zata riƙa sanin me Auntyn yara take ƙullawa, ganin bata da wata shawara ɗuk ta jagule kamar ta kurma ihu take ji, kan gado ta faɗa tana ƙara kiran Allah ya kawo mata mafita.
Sai da ta gaji ta tashi ta hau gyaran gidan, ta masu girki can tayo wanka tana so ta sa kaya sai ta buɗo akwatin da system ɗin nan yake ciki, murmushi tayi ta janyo ta tace "ko kunnata ban ma taɓa yi ba".
Kwalin ta shiga buɗewa, cikin assesories ɗin da ta zo dasu nan taga wani ear piece mai kyau, sai bluthooth mouth, sai wata ƙaramar recoder mai haɗe da camera, ɗauka tayi tana jujjuyawa tace "laa wannan kallar wadda Zarah ta maƙala mun a baya ne amman wannan hadda camera" ta taɓe baki ta aje gefe guda.
Take kuma tace "what am i doing ohh Allah, wannan ai kamar mafita ce na samu yadda zan riƙa sanin me Auntyn yara take ƙullawa". wani tsalle tai tana murna tana gode ma Allah.
Can kuma ta dakata tace "but this issue is complicated, taya zan iya maƙala ma Aunty, tabbas zai ɗauko duk abunda take cewa da kuma inda take zuwa, to sai da asiri na zai tonu kona maƙala mata bata gani ba da tazo wanka zata iya yadda shi ko ta gani, in kuma har ta gani kashi na ya bushe wallahi" kama kanta tayi tana murzawa can kuma ta kaɗa hannu tana murmushi tace,
"Ban mayi tunanin da zai fisshe ni ba taya zan maƙala mata a jikinta ai na ma tona ma kai asiri kenan, a ɗakinta kawai zan maƙala ko yane zanji wani sirrin, to amman taya zan maƙala? akwai rikici fa, Allahna ka kawo mun mafita".
Can kuma ta ƙara cewa "ya salam taya zan riƙa ɗauko abun in na maƙala duk bayan kwana ɗaya ko biyu dan inga abunda take, kai bazai yu ba zata kamani in ma bata kamani ba zata zarge ni da yawan shiga ɗakinta da nake akwai wata manufar a ƙasa, yadda za'ai kawai in nasa ba sai na wayyaye abun ba ace zan iya conecting through system direct kawai irinƙa gani, to amman taya?".
Kwance recorder tayi daga cikin leɗar da aka sako ta, ta shiga buɗe duk Inda taga yana buɗuwa taga wajen sa memory hadda memory a ciki "cewa tai wayyo Allah na, ya zanyi kenan sai dai asa memory in yayo recording sai a cire a kunna memory ɗinko", iska ta zuƙa tana furzarwa ta faɗa kan gado tana kara jujjuya abun a hannunta sai tsaki take saki ganin duk effort ɗinta a banza, can tana cikin juya shi taga tambarin apple a jiki a fili tace "ba shakka wannan abun a tare suke da computer nan dole akwai connection a tsakani kuma i have to find it no matter what it takes domin na tseratar da mu daga kaidin marasu imani".

KAMU SEDANG MEMBACA
ZAN SOKA A HAKA
Fiksi Umum#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021.