page 56

5.1K 284 56
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨





💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )

















Page5⃣6⃣

*KADA KA FIDDA RAI DAGA RAHAMAR UBANGIJI.......*


"Nanawo? Nana? Nanar mu? wannan ai Halimatun muce da ɗiyarta wadda ita da babanta ba'a san ko suna da rai ko sun mutu ba tun faruwar rikicin Damaturu, to ya akai wannan hoton yazo nan Abdallah ko Asma'u waye a cikinsu danni nasan banda wannan hoton tabbas, kai bama Abdallah ke dashi ba, to na Asmah ne kenan kuma sunanta Asma'u kenan itace ɗiyar Halimatun mu data bata kenan, anya to taya hakan ya faru ko shiyasa nake ganin kamarsu kuma nake jin Asmah a jiki kamar ƴata ashe ko ƴata ɗince?" take ta tuna jiranta ake takaddun ta tattaro inda ta sake su ta ɗauki hoton ta fito, mutumin ta ba ya tafi.


Ta zauna tana ƙara nazarin wasu abubuwa wayatta ta jawo zata kira Halima amman sai ta maida har kuma zata kira Naty sai ta fasa tabi ra'ayin zuciyarta akan ta bari ta gaskatar da lamarin tukun, duk da wani ɓangare na zuciyarta na faɗa mata ai ba wani tabbaci da ya wuce wanda ta samu yanzu tunda suna yazo iri ɗaya ga kuma manyan shedu hoton da kamanni da ta daɗe tana maganar shiyasa da biki taso Nana taga amaryar dan tana ta bata labarin kamanninsu itama Nana taso ganin amaryar sai dai a ruɗe ta tafi, tashi tayi tana ta zirga zirga duk ta ƙagara Asmah ta dawo ji take kamar mafarki take bata so ta farka Asmah bata dawo ba taji gaskiyar lamarin.



Wani tunani ne ya faɗo mata rai da sauri ta jawo wayarta ta kira Na iraƙi tace mai yai sauri yaje ya ɗauko Asmah.





Asmah na zaune a tsakar gida bayan sun gama la'asar tana taya Aunty Nafi ɗaura tuwon dare sai wahalar tada wuta suke tana mutuwa saboda wani iska da ake tayi tun shigowar la'asar hadari ne ya taru cunkus a sama daga gani ruwa za'ayi kuma ruwan farko ba, su Asmah masu gona ana tajin daɗi ruwa yazo suna yi suna hirarsu sai suka ji sallama Asmah tasa mayafinta ta leƙa ai sai sukai kiciɓis da Na iraƙi, a ranta tace "to shi wannan ko bai ji lokacin da aka ce ya dawo bane?" katse mata tunani yayi da faɗin "ance na zo ɗaukar ki ne" bayan ya gaisheta.

Cewa tai "gani nan fitowa" ta juya kamar ta rusa kuka take ji.

"Ya naga kina bata rai me  ya faru? waye ne yai sallamar?".

"Wallahi Aunty Nafy Na iraƙi ne wai yazo ɗaukata tun yanzu" ta faɗa tana turo baki.

"To meye na ɓata rai Asmah ban sanki da haka ba, ina ma laifi ai mun gaisa ko gwanda ma da aka zo kina ganin yadda hadarin nan ya taru duk da na farko ne sai akasin tsammani amman da wuya ba'ayi ruwa ba yau duba da yadda hadarin ya taru ai gwanda ki koma ɗakin mijin ki Asma'u ya fiye maki alheri".

"Wayoo wallahi ni ban gaji da ganinku ba".

"Haba ƴar ɗiyata ba muna waya kullum ba kar ki damu sai wani lokacin kuma".

"To shikenan Aunty Nafy bari na ɗauko jaka ta".

"yauwa kayan na nan na haɗa maki cikin ƴar bakko a bayan ƙofa sai ki fito da su kar a manta".

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now