SHI NAKE SO

385 25 0
                                    

https://www.facebook.com/groups/171841133699012/permalink/171846937031765/?app=fbl

🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾

*SHI NAKE SO*

🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾

*A TRUE LIFE STORY*

          *WRITTEN*
               

             _*BY*_

_*AYSHA ISA (Mummy's friend)*_

_*Vote me on  wattpad @ AyshaIsah*_

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*

'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah 🤜🤛)'''

*DEDICATED TO:*

_*BILKISU Z. YA'U*_
      _(Tawan)_


_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

*Page 3*

*SOME YEARS BACK*


Tafiya nake ina 'yan wake-wake na hannu rik'e da sanda, d'ayan kuma rik'e yake da markad'an na da d'auko zaman kai gida.

"Ummin baba...!, Ummin baba!!" naji na kwala min kira da sunan da na tsana a rayuwata dama haka ake kirana sabida sunan sunan kakata gareni wato mahaifiyar babanmu, yi nayi kamar banji na cigaba tafiyata.

"Fusailah...! Fusailah...!!" naji an k'ara kwala min wani kiran amma duk da haka ban tsaya ba, da gudu ya k'araso wurina yace " haba mana Ummi tun d'azu nake ta faman kiranki kika shareni kuma nasan kin ji sarai."

Murgud'a masa baki nayi nace cikin tsiwa " ai ba haka aka rad'amin ba, kaima ai kasan sunana."

Murmushi yayi sannan yace " toh yi hak'uri Fusailah ta, na d'au alk'awari daga yau bazan k'ara kiranki da wannan sunan ba kin ji Fusailah. Kawo in tayaki d'aukan mark'aden..."

Gyad'a masa kai nayi gami da mik'a masa. Har gida ya rakoni muna tafiya muna hira wanda duk yawanci labarin fina-finan dana kalla ne nake bashi. Muna isa daidai k'ofan gidansu aunty Samira na mik'a masa hannu da nufi ansan mark'aden don na shiga dashi cikin gida, kai na girgirza yace min " mu shiga kawai , ai kema kinsan gidan ba bako na bane."

"Toh" shine abinda nace sannan na k'arasa ciki yana biye dani a baya, da shigata aunty Samira ta rufeni da fad'a " yanzu ke Ummi abinda kike yi kin kyauta  kenan?, wai ace tun d'azu mutum yaje d'auki mark'ade bai dawo ba sai yanzu, wai ma ina mark'aden da kika d'auko yake ne?"

Waigawa nayi ina kallon shi yana k'arasowa inda muke tsaye yana isa yace " aunty kiyi hak'uri don Allah ni na tsayar da ita, ga nik'an" k'arasa maganar gami da mik'a mata.

"Babu komai Uwaimir nagode, ina zaton ko ta tsaya shiriritan ne kasan Fusailah da wasa."

Murmushi yayi sukayi sallama sannan ya wuce. Nikam tuni na jima da ficewa daga gidan ko.

Haka rayuwan mu ta cigaba da tafiya cikin ji dad'i, kwana biyu ina unguwarsu aunty Samira, kwana biyu ina can gida wurin iyayena,shak'uwa mai tsanani ya d'ada shiga tsakanin mu da Uwaimir don kusan kullum indan har ina unguwarsu zaka same shi a gidansu aunty, gashi sam Uwaimir bashi da kiwuya duk inda auntyta aike shi yana zuwa don tun san da take amarya yake zuwa mata aike har izuwa yanzu da ta kai ga haihuwa uku.

Duk wannan shak'uwar dake tsakanin mu ni da Uwaimir bai tab'a cewa yana sona ba sai dai alamu da yake nuna min, nikam ko a jiki na don a lokacin bansan ko me ake kira so ba don a lokacin banfi 13years ba.

Ban tab'a manta ranar da Uwaimir ya furta min yana sona don rana ne me mat'ukar tarihi a rayuwata koda dai a lokacin bansan mene ake nufi da hakan ba, kamar kullum zaune muke ni da Uwaimir muna hira bayan mun tab'a hira, Uwaimir yayi gyaran murya yace " Ina sonki Fusailah."

"Nima ina sonka "  nace ina d'an murmushi don na d'auka irin wasan nan ne da muka saba.

"Da gaske fa nake Fusailah, ina sonki da aure, ina son ki zama matata, uwar 'ya'ya, kamar yanda aunty Samira take ga Abban su Yasir."

"Tab! yanzu kana nufi kace zan bar gidansu Maman mu kenan na koma gidan ku?, aito nayi k'arama ni dai bana sonka in dai haka ne" nace ina me zumb'uro baki.


"Ai ba yanzu za'ayi aure ba Fusailah sai kin k'ara girma kinji Fusailah ta, don Allah ki soni kin ji tawan." yace cikin sigar lallashi.

"Uhmm."


"Toh! Don Allah kice kina sona ko zan d'an ji sanyi a raina, please Fusailah."

Mik'ewa tsaya nayi sai da na kai daidai bak'in k'ofan gida nace " nima ina sonka Uwaimir " sannan na ruga gida a guje.

Murmushi Uwaimir yayi had'a da girgirza kai " Fusailah kenan, In Shaa Allah ni zan koya ma zuciyarki yanda  zata soni " sannan ya mik'e yayi tafiyarsa ba tare da ya k'araso ciki ba kamar yanda ya saba.


Tsakar gida na samu aunty Samira tana gyaran shinkafa, d'ago kai tayi ta dubeni tace " ke da waye kika rugo a guje?"

Waigawa nayi na duba ko ya biyoni, ganin babu kowa na juyo  nace da ita " babu komai."

Girgirza kai aunty Samira tayi tace " Allah ya shiryeki, ni Samira bansan sanda zakiyi hankali ba Fusailah " sannan ta cigaba da aikinta. Ni kuma naje na tattara kwanuka na fara wanke-wanke.


Bayan kwana biyu lokacin na riga na koma gidan mu ko. Da misalin k'arfe 3:00pm nayi shiri na tafi makarata tafiz da yake duk ranar Alhamis da Juma'a k'arfe uku muke zuwa mu dawo tara, koda na isa makarantan naje na taradda wai mallamin mu yayi tafiya, shafin hira muka bud'e maimakon karatu a nan ne nake basu labarin yanda mukayi da Uwaimir.

"Ke yarinya wallahi ki amince kawai, ba wani k'ank'anta da kikayi, ai a k'auyen mu ma wasu basu kaiki ba ake masu aure, ina ma ace nice yace yana so " Hafsat k'awata tace har da wani lumshe ido take yi.

"Au! Daga niman shawara zaki wani ce ina ma ace ke yake so?, kaji 'yar iska dama kina son aure shine baki fad'a ma babanki ba ya daina wahalar da kanshi yana kai makaranta, toh bari ki ji Uwaimir ma ba zai tab'a cewa yana sonki ba ehee."

" Allah ya huci zuciyarki, ni wasa ma nake yi."

"Ameen..." nace daga nan kowa yayi shiru babu wanda ya k'ara cewa ko ufan daga cikinmu har lokacin sallah yayi muka mik'e muka je maka sauke farali.



_Anya kuna jin dad'in labarin nan kuwa?, nagan bana ganin comments d'inku._



Muje zuwa.




_*Mummy's friend ce🌹*_

SHI NAKE SOWhere stories live. Discover now