⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*SHI NAKE SO*
_*(Labarin Fusailah)*_🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN*
_*BY*_
_*AYSHA ISA (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah 🤜🤛)'''
https://www.facebook.com/ZAMAN-AMANA-Writers-FANS-311893699485963/
*DEDICATED TO:*
_*BILKISU Z. YA'U*_
_(Tawan)_*LIKE AND COMMENT*
👇👇👇👇👇👇
https://www.facebook.com/groups/171841133699012/permalink/171846937031765/?app=fbl
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM"*_
_*Please wanda keda Illar rik'o ('yar rik'o) daga page 62-75 ya/ta taimaka ya/tamin sending ta wannan number 08146960525*_
_*Mamienmu wannan pajin naki ne ke kadai kiyi duk yanda kikeso dashi kyauta ce daga Mummy's friend.*_
_*Page 22*_
*Bayan kwana biyu*
Yau kwana na hud'u kenan cif a gidan Uwaimir, a yau ne kuma na tsarkake amma sai pretending nakeyi sabida kar Umaiwir ya sani. Yanayin da shi kuma Uwaimir duk abinda nake yi yana ankare dani sai dai kawai ya bini da murmushi.
Da misalin k'arfe 8pm Uwaimir ya shigo d'aki rik'e da leda, mik'ewa nayi na amshi leda dake hannunsa had'i da masa sannu da zuwa. Amsawa yayi cike da fara'a sannan ya zuwa bisa tabarman dake shimfid'e a falon mu.
Hira muka d'an sannan ya mik'e yace " bari naje na d'auro alwala, kema kije kiyi d'auro alwala sai muzo mu gabbatar da nafila kamar yanda Manzo S.A.W ya umurce da yi."
Murmushi nayi ina wasa da zob'en dake yatsa na sannan nace "ai ban dashi"
"Baki da me?" ya tambaya yana bai kafeni da idanu.
"Uhmm! Bai tsaya ba ko."
"Au da gaskiye, amma ana iya sauran sallan dashi kenan, wannan kawai ne ba'a iyawa?" Uwaimir ya tambayeni yana min wani irin kallo.
Girgiza masa kai nayi alamar a'a.
Dawowa yayi ya zauna kusa dani sannan yace cikin sanyin murya " Fusailah wai meyesa kika fiya tsoro ne?, kar ki manta fa d'azu akan idona kika yi sallar la'asar koda shike baki sannan da shigowata ba. Don Allah ki rage tsoro I promise to be nice " hannuna ya rik'e muka mik'e a tare.
Fita yayi zuwa waje ya d'auro alwala, inda ya barni tsaye a gun yazo ya sameni, " lafiya Fusailah kike tsaye anan har yanzu?"
"Ina da alwala" na fad'a a takaice don wallahi na riga na tsure don irin labarin nake ji na daren farko sai a hankali.
Murmushi yayi yace " toh saka hijabi mu gabatar da sallan."
Hijabi na saka sannan nazo muka gabatar da sallan nafilah raka'a biyu kamar yanda Manzo S.A.W ya koyar. Bayan idda ya dafa kaina ya kwararo addu'o'i sannan ya mik'e zuwa falo, jim kad'an sai gashi ya dawo rik'e da kofi da pkate. Ledan ya bud'e ya ciro kaza da yoghurt, d'aura kazan yayi nisa plate, ya tsiyaye yoghurt a cup sannan yace min " bismillah habibaty."

BINABASA MO ANG
SHI NAKE SO
Short StoryLabari ne wanda ya kunsa soyayya, hak'uri da juriya,da kuma imani da k'addara. Wannan labarin ya farune da gaske,ku biyoni ku sha labari.