🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*SHI NAKE SO*
🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN*
_*BY*_
_*AYSHA ISA (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah 🤜🤛)'''
*DEDICATED TO:*
_*BILKISU Z. YA'U*_
_(Tawan)_*LIKE AND COMMENT*
👇👇👇👇👇👇
https://www.facebook.com/groups/171841133699012/permalink/171846937031765/?app=fbl
_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM"*_
'''Ina jin dad'in comments d'inku wallah yana sakani nishad'i mussam 'yan SHI NAKE SO FANS GROUP'''
'''Gaisuwa ta mussam gareki Maman labyb (Mamien mu), ina jin dad'in yanda kika bada lokacin kike sharhi akan wannan littafin,don wannan shafin naki ne ke d'aya kyauta daga mummy's friend kiyi duk yanda kike so dashi.'''
*Page 8*
Haka na tashi washegari cikin rashin walwala kowa ya min magana bana iya amsa masa don har ga Allah daurewa kawai nake don ko magana nace zanyi sai naji kwalla na shirin zubomin, har yanzu gani nake kamar mafarki nake wani zai zo ya tashi yace Fusailah tashi mafarki kike amma ina aikin gama ya riga ta gama ko.
Haka 'yan gidan mu suke ta tambayan mamanmu ko meke damuna na sauta farat d'aya nan take sanar dasu cewa a dakatar da maganar aurena da Uwaimir ne, babu wacce bata tausaya min ba domin kuwa sun san yanda muka shak'u dashi.
Bayan kwana biyu Babanmu ya amshi kud'in sadakin dake hannuna aka maida masu, a nan na k'ara tabbatarwa lallai an fasa aure da Uwaimir ranar na ci kuka kamar raina zai fita, daga k'arshe ma ji nayi kamar na gudu na var gidan na shiga duniya ko zan ji saukin rad'ad'in da zuciyata ke min.
Wani abun haushi da takaici koda na kira aunty Samira ina sanar da ira abinda ya fara ita ko a jikinta illa ma haushi da ta k'ara cusamin ta hanyar fad'in "toh sai me don a fasa aurenki da wannan talakan, dama can ke va matarsa bace amma tunda kin nuna kema kina sonsa shiyasa na zuba maku ido, yaron da bashi da tarbiya.."katse wayar nayi don haushi wai ace har anti Samira ce ke fadin irin wanban kalaman game da Uwaimir.
Daga lokacin ban k'ara jin d'uriyan Uwaimir ba, sai daga bayane nake jin wai ya bar gari ya koma makaranta.
Da k'yar Mamanmu tayi Babanmu ya sanae da ita abinda Uwaimir yayi maganar ma babu tushe balle asalu wai cewa yayi abokinsa yace Uwaimir yagan shi amma bai gaishe shi, harda mijin aunty Samira a cikin wanda sukayi dalilin fasa bikin don shima cewa yayi idan Uwaimir yagan shi baya gaidashi, ai koda mamanmu ta fad'a min dalili naja masu Allah ya isa yafi a k'irga.
Haka dai ba ci gaba da rayuwa da k'yar Maman mu ta samu ta koma schoolda tahfiz don cigaba da rayuwata kamar da.
*Ci gaban labari*
Hawayen da ya zubomin ne da goge da bayan hannuna ina me k'ara wa'innan bayin Allah ya isa.
Tafe nake wani mutumi nata bina yana kwala min kira "malama..! malama..!!"
Yi nayi kamar banji shi ba,
"Don ki tsaye "cewar mutumin, wanda yasa na tsaya cak.
Sallama yayi min sannan yace " don Allah idan babu damuwa malamar matan aure ce ko buduwar?"
"Matar aure ce" bace a takaice nada tafiya, bina yayi yace "don Allah kiyi hak'uri fa amma wallahi bakiyi kama da wacce tayi aure ba."
"Ko?" nace ina mw ci gaba da tafiya ta had'a k'arewa kaina kallon me ya ganu a jikina wanda yasa shi fad'an hakan amma gar na k'arewa kaina kallo banga wani abu da aibin da nayi ba don hijabi har k'asa a jikina ina tsaka da tunanu naji yace "don Allah ki taimaka min da lambar wayarki."
"Mallam nace maka ni matar aure ce, haba wannan irin nacin haka."
Murmushi yayi yace "nasan ke ba matar aure bace don sai dana yi bincike kafin nazo gareki, Allah ki d'aure ki taimaka min da lambarki karki min ce babu don nasan akwai ta don Allah."
Babu yansa na iya dole na basa number na, a nan ne yake sanar dani sunansa Mujaheed.
Muje zuwa.
_*Mummy's friend ce🌹*_

STAI LEGGENDO
SHI NAKE SO
Storie breviLabari ne wanda ya kunsa soyayya, hak'uri da juriya,da kuma imani da k'addara. Wannan labarin ya farune da gaske,ku biyoni ku sha labari.