SHI NAKE SO

206 10 0
                                    

🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾

*SHI NAKE SO*
_*(Labarin Fusailah)*_

🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾

*A TRUE LIFE STORY*

          *WRITTEN*
               

             _*BY*_

_*AYSHA ISA (Mummy's friend)*_

_*Vote me on  wattpad @ AyshaIsah*_

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*

'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah 🤜🤛)'''

https://www.facebook.com/ZAMAN-AMANA-Writers-FANS-311893699485963/

*DEDICATED TO:*

_*BILKISU Z. YA'U*_
      _(Tawan)_

*LIKE AND COMMENT*

👇👇👇👇👇👇

https://www.facebook.com/groups/171841133699012/permalink/171846937031765/?app=fbl

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM"*_

_*Sorry for the long wait dudes.*_

*Page 18*


Bayan bikin yayana da kwana biyu Uwaimir yazo ya min sallama zai tafi garin da yake d'an buga-buga shi don gani yake kamar zai kuma rasani ne a karo na biyu. Haka nima ya kansance a wurina don ko a tsakanin k'awaye na daina maganar, ko saka ranar da akayi ban fada masu ba don gani nake wani sabon hanyar hana wa Uwaimir aurena ne Babanmu ya kuma b'ullo dashi.

Haka dai muka cigaba da gudunar da soyayyar mu cikin shakku ko zamu kasance wuri d'aya a matsayi ma'aurata ko a'a. Duk lokacin da Uwaimir ya samu sarari yakan zo sha hiran mu irin ta masoya sai dai yanzu bai fiya min siyayya ko kyauta  kamar da, nima kuma banga laifinsa ba.

Wannan kenan.

A kwana a tashi babu wuya gun Allah yanzu wata d'aya cif ya rage aurena da Uwaimir kamar yanda Babanmu yace.

Yau ma kamar kullum zaune muke nida k'awaye muna hira bayan a fito break, nace " ku saura fa wata d'aya bikina..."

"Au ashe dama maganar da nake ci a gari gaskiya ne, ni ina can sai k'aryata mutane nake don dai mu baki fad'a mana ba" cewan Fatima d'aya daga cikin k'awayen na.

"Oh ni Fusailah! Wai ace duk yanda nake ta son b'oye wannan batun saida 'yan gulma suka fad'e ta, don Allah kuyi hak'uri.."

"Toh munyi " cewan Fatima, Zainab, Aisha da Khadija sannan Khadija ta cigaba da fad'in " nayi zaton ko baki buk'atan mu ne a bikin naki shiyasa baki sanar damu ba don naji ance harda su anko ma an fito dashi ko."

"Oh ni 'yarsu! yanzu dai an daina kiwon dabba an koma kiwon mutane, wannan gulma har haka, don Allah wai ina kika ji wannan  maganar ne?, d'azu fa mukayi da aunty Samira gobe zata kasuwa a fidda anko amma shine 'yan gulma harda nasu k'arin" na fad'a cike da mamaki.

Aisha tace "kedai fad'i gaskiya..."

"Haba Aisha yanzu meye riba na idan nayi maku k'arya?" nace raina a d'an b'ace.

"Don Allah a bar wannan maganar haka " inji Fatima.

"Yauwa da fatan dai naki bikin zamu d'an cashe, don kin san a na Kamila mallama ta hana" cewan Khadija.

"Da wuya dai don Babanmu ba bari yake ba."

"Hmm amma dai biki babu irin casu d'in nan babu dad'i wallahi "  Khadija tace cikin nuna rashin jin dad'in ta.

Haka dai muka cigaba hira ranan kan yanda bikin zai gudana har lokacin komawa aji yayi.


******

Kwanakin bikin mu sai k'ara matsowa kusa yake amma ni banga wani shirye-shiryen da ake min ba dangane siyan kayan d'aki duk da abin yana cikin raina amma sai na barshi a raina don nayi magana a min wata fassara ta daban.

Tunda da lokacin bikin mu ya matso kusa Uwaimir ya rage zuwa gurina, bai fi yazo sau d'aya a sati ba wani satin ma baya zuwa a cewan shi hidimomi sun mashi yawa, tun ina k'orafi har gaji na daina.


*BAYAN KWANA BIYU*

Zaune muke a tsakar gida muna hira da matan gida, Jumma mai kaya ta doka sallama " Salama alaikum mutanen gidan nan, ina yini."

Amsa mata mukayi sannan ta k'araso cikin rik'e da kaya riki-riki kai tsaye wurina ta nufa ta jida kayan a gabana, bud'e kayan tayi ta ciro wani lesi uban-uban su tace "amarya wannan kalar irin taku ce, ba k'aramin fitowa zakiyi ba a cikin ta" gwada lesin tayi da fatan hannuna sannan ta cigaba "wai ba dai kyau, Ladi wai don Allah baki ga yanda wannan kayan ya mata kyau ba?"

"Wallah na gani, har na hange ki cikin ta,  ki dauka kawai Fusailah" cewan Ladi.

"Kaji ki da wata magana haka kawai zan dauki kaya ban san ko nawa bane, king  amshi  kayanki " nace had'i da mik'a ma Jummai Lesin.

"Allah Fusailah ki dauki kayan nan sun dace dake, nasan kuma ba wani tsada garesu kuma ai mamanku ne zata biya " cewan d'aya daga cikin matan gidan.

"Ina kuwa yake da tsada dududu baifa fi dubu 16 ba" inji Jummai.

Dago kai nayi wanda yayi da had'a ido da Mamanmu wacce take daga bakin kofar d'akin mu zaune, harara ta banka min wanda yasa babu shiri na ajiye kayan sannan nace " Allah dai ya kawo kasuwa.."

"Haba maman Fusailah nawa akayi dubu sha 16 da kika banka mata wannan uban hararan, wai idan ku bakuyi mata ba wa zai mata ne? "  Ladi ta fad'a rai a b'ace, sannan ta jiyo gareni tace " maza dauki kuma dole ta biya..."

K'in dauka nayi ina kallon Mamansu amma ko kallona bata yi ba.

"Wai bacewa nayi ki d'auki kayan bane? " Ladi tace tana mik'a min kayan. Hannanu nasa na amshi kayan a sanyaye sannan na mik'e na shiga d'aki. Ban jima da shiga ba Mamanmu itama ta shigo " yanda kika dauki kayan nan toh ki sani fa kud'in d'inkinsu baza su fito a jikana ba, dama ga sauran cen baki gama biya ba" tace sannan tayi shigewan ta  uwar d'aki.

Wani hawaye mai zafi naki yana zubo min, ji nake kamar ba ita ta haifeni, meye laifina don kawai nace *SHI NAKE SO?*, a cikin 'yan kwanakin nan Uwaimir ya bani kusan dubu goma ko duk da su nake ta siyan wasu abubuwa, a cikin su ne kuma na rage kud'in d'inki, yanzu kuma ga wannan ance ni zan biya, wannam wani irin rayuwa ne, a iya sani na iyaye ke ma yara kayan fitan biki amma nikam nawa yasha banban, kuma a hakan gani suke baya bani komai ko ina suke tunanin ina samu wa'inan kud'aden idam bashi ke bani. Goge hawaye na nayi na saka hijabina na tafi gidan d'inki.


Wannan kenan.



Sannu sannu bata hana tafiya saidai a dad'e ba'a je ba, yau ne Uwaimir ya kawo min katin bikin mu wanda yake saura sati biyu yanzu. Fad'in irin murna da nake ciki baya misaltuwa domin ganin mafarkina ya kusa zama gaskiya. Hiran mu ta yau ta daban ce kuma ta musamman wanda yasa naji na k'agu na ganni a d'akin abin alfaharina, ruhina, rayuwana, masoyina...
 

Saida muka gama shan hiran mu sannan na fara masa k'orafi kan abin da abokansa suke ma k'awaye don har yanzu suk'asa basu had'in kai sai yawo suke masu da hankali gashi kuma su anty Samira sunce komai bazasu basu ba saidai su ansa gun abokan ango.

Hak'uri ya bani don shima dai baya da kud'in da zai bani yanzu. Haka dai dole na hak'ura don babu abinda na iya idan banyi hak'urin ba.


_*🌹Mummy's friend ce🌹*_

SHI NAKE SODonde viven las historias. Descúbrelo ahora