NAZIR

2.1K 45 1
                                    

*🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*

_*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_

*DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN*

_*Wannan Shafin nakune Anty Sainah Ummu meenal,da ke Swt Anty Sis Naja"atu...Ku sani wlh ina muku son kaunah mai dorewa har Abada*_

'''Mamn Afra ko nace maman baddo...Aishatu m yusuf kina ina ina so ki sani ko na ambace ko ban ambaceki ba kina cikin kokon Rainah...Allah yarayamana Afra da baddo cikin Addinin islama'''

3/4

Nusiba tana ficewa batayi kokarin hawa Abun hawa ba sai ta rage sauran kudi takoma a kafa tana shiga gidan ta iske kawu na goge yar mashin dinsa zai Fita Anty na gefe tana rike da hularsa tayi sallama ta Shigo gabadayansu suka zuba mata ido suna kallonta cikin kuzarinta ta kariso tana jan kujeran yar tsugunne dake wurin tana Fadin"Kawu har zaka fita"Kallonta yayi yace"Nusiba yana ga kindawo Allah yasa ba latti da kikayi bane yajawo miki mtsala ba"Yamutsa fuska tayi kan tace"Oho musu dai kawu wai koda naje wanda zamuyi shirin tare yatafi wai kajifa kawu wai baya jira sai dai ajirasa"Kawu yace"Topha shiko waye wannan mai tsautsaran hali haka"Nusiba ta tabe baki tace"Nama sanshi wai wani NAZIR ADAM GALADANCHI..."Kawu ya dakata da sauri yana maimata sunan abakinsa Nusiba da Anty suka zuba masa ido kafin tace"Kawu kasanshi ne hala"Kura mata ido yayi kan yace"Dashi aka hadaki aiki"Tagyada kai zatai mgana kawu ya katseta dacewa"A"a Nusiba ki hakura da aikin nan...Bani so sam inga anci zarafinki"Nusiba tace"Meyasa kawu basshi da kirki ko"Yayi ajiyarzuciya yana fadin"Nasanshi Nusiba a office din mahaifinsa nake masinja wlh sam yaron baisan darajan mutane ba bakaramin aikin sabane ya tozarta ka ko ajikinsa sam bai biyo halin mahaifinsa ba"Nusiba ta kalli kawu idanunta ya ciko da kwallah tace"Wlh kawu tunda naji sunanshi naji na tsaneshi ashe basshi da mutumci kawu fadamin yataba maka wani abu wlh in ya tabamaka sai na rama maka" kawu yayi saurin cewa"Bai tabamin ba Nusiba kawai bani son ya tozartamunke ne in har basu chanzaki miki aiki ba kidawo gida munema awani gurin"Nusiba tace"Allah ma yatsareni manaja yace gobe nadawo ya chanzamin inda zanyi aiki"Anty tace"shikenan ma kinga kin huta ammh meza ai da marasa mutumci"Kawu yace"Allah dai ya kyauta.Sallama kawu yayi musu kan yafice suna mai Allah yadawo lpy.

*WACECE NUSIBA*

NUSIBA SADDIQ BUNZA....shine cikakken sunanta ita din yace ga shahararren Manomin nan dake garin zaria wato Alhaji Saddiq bunza wanda yakasance mahaifisa dan jahar kebbi ce akaramar hukumar bunza shima din cirani ya kawosa har yafado zaria,yayi zaman noma tunyana yi da kansa har yakai mtsayin sai da yasa ayimasa yana da matar aure gudaya mardiyah suna kiranta Dada Sai dansu kwara daya Saddiq wanda yataso cikin gatane da tattali mahaifinsa  suna zaune ne a tudun jukum dan gidansu mai kyau da tsari bai rasu ba sai da yayimasa auren fari dayake ba boko yayi ba iyaka kawai yana sauka a allo lokacin shekaransa 23,Aduniya matarsa ta fari Fatsima sunanta ita yar zarian ce agwarbai  Fatsima dai bata da kowa aduniya sai yayanta guda daya mai suna jibril wanda ya kasance jigo agareta Fatsima itama batayi boko ba iyakarta allon yayan natane ma yagama sakandiri.

Auren Fatsima da saddiq auren soyayyah ce sukai susuka hada kansu har iyaye suka shiga ciki...aurensu da wata biyu fatsima tafara fuskanta matsi wurin mijinta saboda ta fahimci mugune kansa kawai ya sani duk da iyayensa ke musu komai ammh dan abu in yasamu bayama son tasan yasamu dan balagun nan kuwa haka zaizo dashi yazauna yanaga Abunsa wlh koda zata mutu bazai bata ba tun Abun baya damunta har ya fara damunta domin ko Abu Alhaji yabada amata shi da Dada zasu hana wlh baza su bata ba,awurina daya take samun Sauki gun Alhaji kuma Allah yazo ya karbi Aransa tundaga lokacin Abubuwa suka fara nisa Fatsima bata samun sauki ta wurin Saddiq kuma bata samu wurin Dada domin Dada irin tsofaffun nan ne masu shegen kwadayi ga sa"Ido da gulma duk wani motsin fatsima tana sane dashi,wani lokacin in Abun ya isheta sai dai tafadama yaya jibo to shima din saidai yabata hakuri saboda bai da yadda zaiyi shima da sana"ar facin dayakeyine yasamu yafada Fce zaria shine in yasamu wani Abu yake dakewa yakaima kanwarsa.

NAZIRWhere stories live. Discover now