NAZIR

2.9K 84 20
                                    

*🧑🏻NAZIR🧑🏻*

     _*(The journalist)*_

*(Based on luv and Romantic story)*

  *Na*

*Janaf ce*✍

*Vote me on WATTPAD:Janafnancy*

_*INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION*_

*DIDECATED TO SAHIBA HAFSART HAFNAN*

_*Wow....Ina matukar jin dadin comment dinku yan groups dina irinsu NAZIR FANS1&2 JANAF FANS,HIBBATULLAH FANS,DA INTERLLIGENT WRITERS ASSOCIATION FANS....Ina matukar godiya ga soyayyarku gareni kusani ku kara sani janaf na muku son da baida iyaka...One luv*_


5/6

Tsayawa sukayi cak jikinsu na rawa duk da suna son waskewa Nazir dake tsaye ya sa hannu ya zare bakin gilas din dake fuskarsa manaja daya dago ya kallesa sai da yaji fitsarin dayake makalewa tun dazu na neman zubowa dago kai kawai yayi ammh ma"aikatan dake gurin suka hau dare cikin sadda kai idanunsa ne masu ban sha"awa suka chanza kammani zuwa jajaye jijiyoyin kansa sun mike radam ba kyan gani wani huci yake fitarwa kamar zaki daya samu nama adawa cikin wani irin fusata ya daki wata randan flower dake gabansa yana fadi cikin tsawa"Who iz she...."Muryansa tana fitar da amo na tashin hankali,Rahma dake rike Nusiba tun bayan shigansu office din ta kamkame tana fadin"Mun shiga uku Nusiba..Mekikayi kenan? kinsan waye Nazir kuwa? Nusiba tayi mirmishin karfin hali kan tace"Sanin koshi waye ba damuwar Nusiba bace illa kawai abu daya nasani bazan zauna ya wulakantani ba don dai kawai yana takama da kudi"Tana fadar haka ta zare hannunta ta wuce ta isa kan kujera ta zauna ita kuwa Rahma bin Nusiba tayi da kallo tana mata kallom tattaba tunda har ta shararama Nazir mari ammh ko ajikinta.

Manaja kuwa jikinsa yana kyarma yace cikin rawan murya"Ban....Ban...Ban sani ba yallabai nidai....."Shout up....Nazir ya fada da tsawa kan yace cikin sauri"Awa goma na baka ka bincikomin waye ita,dawa take takama,waye ubanta?infact komai daya danganceta nake sonji kafin yammah tagabata ina so in nuna mata waye NAZIR FREEKING ADAM GALADANCHI"yafada yana wuce zuwa gun mota da rawan jiki ilu ya bude masa sai da ya shiga kana ya nuna manaja da hannu yace"10 hours na baka matukar ka kauce koda dakika dayane u too u ar in trouble"Yana fadan haka ya maida kofa ya rufe suma bodygound dinshi nasu motan suka shiga suka bi bayan ta boss din nasu wanda suka fice da gudu,suna fita manaja dayayi zaman yan bori ya mike harda gudu ya bamka office din su Nusiba yana fadi cikin rawan murya"Nusiba kin kashemu...Haba Nusiba what all dis don Allah duk zafin ranki ki rasa wanda tsautsayi zai kai ki mara sai Nazir"Yafada kamar yayi kuka Nusibq dake zaune dafe da kai tataso tana fadin"Haba yallabai kai baka ga cin zarafin dayayi min ba...Haba kowa sai ganin laifina yakeyi shi baza"a ga nashi ba"Tafada fuskanta na nuna damuwarta manaja ya cije baki yana fadin"Kinsan me kika jefa kanki aciki kuwa?to wlh Nazir bazai taba kyaleki ba Nusiba tsoro nake ji kada yayi miki wani Abun"Nusiba tadanyi jim azahirin gaskiya tadan tsorata ammh sai ta dake tace"Babu abunda ya isa yamin wanda Allah bai minba..Yallabai karka damu ni Nusiba ga Allah na dogara"Kallonta yakeyi yana kada kai kawai kafin yace wani Abu ta rigasa da cewa"Ayimin uzuri yallabai zan koma gida wlh ciwon kai kedamuna"kai kawai ya gyada mata saboda bai da bakin mgana jakarta ta dauka tana ma Rahma sallama daga ita har manaja kallon karshe suke mata don sunsan tabbas akwai Abunda Nazir ya tanadar mata haka awaje kowa binta da kallo yake sai ta waigo akauda kai itama din sai taji ta tsorata kada yazo yasa akasheta"sai da gabanta yafadi datayi wannan tunanin shiyasa da sauri ta tsaida yar kurkura ta shige tana waige.

ilu direba kuwa suna ficewa ya mike titi daya kawo sai yayi new town saboda tsoro ma yakeji ya tambaye oga ya sauke akansa Nazir dake baya yana huci kuma hannunsa dafe da kunci yace cikin tsawa"Don ubanka zagayen me kake dani"Ilu jikinsa yafara kyarma yace"Srry sir...Ban san ina zamu nufa bane,Abuja zmu koma""Ubanka zanyi a Abujan..."in koma Abuja batare da naci uban da ya haifi yarinyarnan ba"yafada muryansa har tana rawa saboda bacin rai"Ilu bai yi mgana ba ya saka motarsu kan hanyar zuwa hotoro GRA,suma gound din suka rufa musu baya.

Nusiba duk afirgice takarisa gida Anty na kichen ta ji shigowarta cikin mamaki tafito tana fadin"Ke kuma lpy daga zuwa sai dawowa"Dan yamutsa fuska Nusiba tayi kan tace"Wlh Anty kaina ne ya mtsamin da ciwo shine nadau escuse nadawo'girgiza kai Anty tayi tana fadin"Ash.sannu ki duba kan mirro na akwai panadol kidauka kisha kinji kidan kwanta rashin samun hutu ne dabakiyi kwana biyu"Gyada kai kawai tayi ta shige daki ammh fargaba na ranta kan katifarta ta fada tana sauke Numfashi.


Shiko manaja office dinsa yakoma gabadaya ya firgice shi banda sunanta wlh bai san komai nata ba ta ina zai fara kuma wlh matukar bai aikata abun yasashi ba to shima yana da baraza sosai arayuwarsa wayarsa ya jawo yana kiran wani abokinsa da ke zoom road din da dazu Rahma ke fadamasa anguwansu,bayan sungama gaisawa manaja yake fadamasa don Allah yayi mai bincike kan wannan sunan,Yafadi sunan Nusiba"Bello abokin manaja yace"Shege sama wato ka hango wata za"a ma madam kishiya ko"Mirmishin yake kawai yayi yana fadin"Bello kayi abunda nace kawai don Allah ka hanzarta komai daya danganceta nakeso cikin awa goma don Allah"yakareshe kamar zaiyi kuka bello yace"ammh lpy naji muryanka wni iri"manaja yace"zaka ji komai daga baya kai dai kawai ka taimakamin bello don Allah"ok kawai yace ya kashe waya.



Cikin mintinan dabasu kai talatin suka isa bakin tamgamemen get din suna sakin get megadi yazo ya bude musu suka sulala parking space firfitowa sukayi suka jeru bakin motar ilu ya bude masa ammh sai daya bata lokaci kafin yafito abun mamaki da ban dariya har yanzu hannunsa dafe da kuncinsa kamar zararre daya cire sai kuma ya maida yana shafawa domin shifa har yanzu bai yarda ba,wucewa yayi fuu kamar kabubuwa cikin gida babu ko sallama ya fada falon,musty ne zaune kan daya daga cikin kujeran data ma falon kwanya gefensa Aisha ce taci ado sai Jidda dake gefe tadora kafa daya kan daya tana taunan cimgam gefe kuma inna zainaba ne tana zaune gabanta filet din ferfesun naman kaji ne take yaga kamar anjehosa haka ya shigo dafe da kunci Gabadayansu suka bishi da kallon mamaki ko barayinsu bai kalla ba ya wuce zai haura sama jidda ce ta mike tana wani rawan jiki tace"u wlm ya Nazir"tafada tana shan gabansa cak ya tsaya yana kallonta da jajayen idanunsa ganin yanayinta yasa taja baya cikin tsoro shikuwa wai rikidemai tayi ta koma mai Nusiba ai cikin zafin nama yayi taku ya rikota shake mata wuya yayi yana fadin"i will kill u"yafada da karfi da sauri Musty da Aisha suka mike kan suje inna zainaba ta rigasu da gudu ta isa tana kokarin bambare hannunsa kan wuyan jidda data fara galabaita Ammi dake kichen taji hayaniya ta Leko Abunda taganine yasa ta sandare ta na Fadin"NAZIR...Da karfi ina ko jinta bayayi inna zainaba tafada cikin tsawa"Sakarta don Ubanka..."musty ya karisa yana

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 24, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NAZIRWhere stories live. Discover now