RUWAN DAFA KAI 2

1.7K 123 10
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

15

Dayake a seat din baya aka kwantar da ita,kuma motar babbace sosai hakan ne yabawa Abban daman samun wajen zama shima isashe ma kuwa,don bawani waje taci ba, ya fara yayyafa mata ruwa,kamar dai koda yaushe,ajiyar zuciya tasaki sannan tadawo hayyacinta,ganin komai take kamar a mafarki don wannan abune dabata taba tsammani ba,ita data riga ta saddaqar dacewar a wancen dajin zata karar da rayuwarta,amma kuma dai ikon Allah yafi ga haka,indai mutum zai fawwala lamarinshi ga Ubangiji yakuma dage da addua to da sannu mafita zatazo mishi babu zato babu tsammani.

"Sannu,sannu kinji"Abba yadinga cewa,kokarin tashi zaune tafarayi yamaidata,"kiyi hakuri yar gidan Abba kwanta abinki ki huta kinji"yace cikeda farinciki mara misaltuwa,sannan ya bude kwalbar ruwa yafara bata,dandanon ruwan ma jinshi take wani sabo,tariga tasaba da na randarta,dakyar dai tadansha don bata shaawar komai ma,ba abinda yake mata dadi,ga jikinta dayayi zafi rau kamar agasa masara,shikuma kallonta yake kawai cikeda tausayi da kulawa,dakuma jajanta mata akan irin rayuwar data tsinci kanta ciki wata da watanni,amma koba komai dai yana matukar farinciki da ganinta tunda su sun riga sun gama saddaqarwa data mutu to ashe tana nan araye,Allah sarki ashe da rabon su sake ganawa,ya nemi gafararta,yanzu haka duk duniya inaga babu wanda yakaishi farinciki ahalin daake ciki,batace komai ba sai murmushi kawai data sakar mishi,dakuma hawaye dayake shatata kawai daga idanunta,saboda yadda take ganin komai sabo to yaushe rabonta ,da rayuwa cikin mutane irin haka?kallonta kawai yadingayi cikeda farinciki dakuma tausayi,duba da yadda kamaninta suka chanja gabaki daya kasusuwa ko ina,ga hakora, hmmm chanjin rayuwa babu abinda baya maida mutum tabbas.

Kamar dai dazu dazasuzo aka tsaya sallah dacin abinci yanzu ma haka akayi,inda Abban yafita yayi sallah,ya taho mata da fruits da sauran kayan ciye ciye don su take bukata,"sannu kinji tashi kidan ci wani abu"yace yana mai bare mata ayaba,tareda mika mata kallonshi kawai take tun dazu da yadda yaketa nan nan da ita yana lallabata kamar dai yadda yasaba ita data riga tasan bazata sake samun irin wannan kular ba arayuwarta,uhmm,ba abinda take sai ajiyar zuciya,ya Allah nagode maka,ya Allah ka yafemin ya Allah karkasake jefani cikin irin rayuwar danashiga ya Allah na tuba,ko makiyina bazanyiwa fatan shiga irin halinda na tsinci kaina ba,tadinga zancen zuci bayan ta karbi ayabar ta rike,tana jujjuyata tana kallonta to yaushe rabonta dawani fruit ma ai ta manta,saida Abba yaita bata baki yana lallabata sannan aka samu tadan gutsira,ta mika mishi alamun ta koshi,"yar gidan Abba har yanzu kinki cewa Abba komai"yace yana murmushi bayan ya karbi ayabar,itama murmushin kawai tamishi don bazai taba gane irin halinda take ciki ba,sanann ta gyara kwanciyarta,rabonda tajita akan abu mai laushi irin wanann tamanta kafinn ace meye wannan kuwa tayi bacci.

Abinda yafi damun Abba shine bayan ta fara bacin kusan sau nawa tana firgita,ita kadai tadinga farkawa a tsorace,saita juya ta ganshi ta yi waige waige don kara tabbatar da inda take din, saita cigaba da baccin,wayyo Allah,Allah yasa dai bawani abin suka mata ba wayanan mtanen don shi a wajenshi basuda maraba da matsafa haka dai yadinga zancen zuci inta kama yayi a fili.

Ahaka dai aka cigaba da tafiya,har Allah yasa suka isa babban birnin na kinshasa,inda aka wuce dasu iya policestation aka kullesu,su Abba kuma suka wuce asibiti.

Ai su kansu likitocin saida suka tsorata dasuka ganta don tazama irin kashi da ran nan,komai ya kare kawai dai tana numfashi ne dakyar,ga jikinta duka shacin bulala ne,duk tabo,babu makawa inda takara wani dan lokaci ahaka da bazata kai labari ba saidai kuma wani ikon Allah,batareda bata lokaci ba kuwa suka shiga gudanar da gwaje gwaje tare kuma da bata duk wani taimako dasukasan tana bukata,hardasu karin jini,ruwa kuwa Allah kadai yasan nawa ta shanye.

saida komai ya dan lafa,sannan Abba yasamu damar kiran su Mama agida,to ai murna da farincikin dasuka tsinci kansu ciki bazai fadu ba a wannan dan rubutun,abin dai sai wanda yagani Ashe dai tana raye shine abinda suka dinga cewa,su dasuka riga suka gama saddaqarwa,Allah sarki,babu bata lokaci kuwa aka fara kiran yanuwa da abokannanarziki ana sanar dasu wannan labarin mai dadi,amma idan aka tambaya a ina aka gantan akace congo kowa sai yaita mamaki,atoh ai dole ayi mamaki saboda kuwa duk cigiyar ma dazaayi congo shine zai zama kasar karshe ma dazaa iya cewa zaa duba to meyasa ma dama waye dasu acen wakuma suka sani,kuma ma ko a cen dinne,an kaita wancen dajin tayaya zaayi ataba ganota dama?to aikin gama dai yagama,saidai a kiyaye gaba akuma lura,amma rashin bincikensu shi ya ja musu komai,tunda inda sun san asalinshi dama tun farko shi din dasun sami idea.

Ba yadda mama batayi ba akan Abba yatura mata hoton yarinyar tata taganta ko ranta yadanyi sanyi hankalinta kuma ya kwanta amma kememe yaki saboda yasan abin bazai bada kala ba,yasan halinta yanzunnan zatabi ta tada hankali ta kasa sukuni watakila ma tace saita biyosu,to ilai kuwa,ai tana ganin hoton yar tata ta rikice tasa kuka,saboda kuwa duk wani mai imani indazai ganta awannan hali saiya zubda mata da hawaye,shima Abban karfin hali dai kawai yaketayi,cewa tayi kawai idan yasan ta mutu ne yafada musu kawai su sani sai hasashensu ya tabbata,"wallahi tallahi da ranta sarai har magana ma munyi"yadinga mata rantsuwa," ahakan? "tace cikin tsoro cikeda mamaki, "eh wallahi ahakan,kedai kawai ayi addua likitocin sunce tsananin yunwa ce da tashi hankali suka mata yawa,hmmm Asiya inda kinsan a inda muka dauko yarinyar nan ko!,"sai kuma yayi shiru saboda kuka dayake neman cin karfinshi,don ko tunowa bayasonyi,duk shi yajawo mata komai ai,inda bai goya mata baya ba ai da duk haka bata faru ba,"kai innalillahi waninna ilaihi rajiun wannan yaro bai kyauta mana ba,Allah kuma saiya saka mata damu kanmu saboda wahalar damu dayayi gabaki daya"tace hawaye wani nabin wani "ai zai ga rashin kyautawa kuwa ganin idonshi tunda bashida mutumci nasa an daureshi daga shi har shashashar uwar tashi tunda basuda hankali duka,wai kinsan ma mezai kara baki ammaki?ashe daniskan yaron nan ba musulmi bane?"ai kujera mama ta nema tazauna saboda kafafauwanta dasuke neman su gaza jure tsayuwa,"la ilaha ilallahu?yanzu duk tsahon lokacin nan cikin kafurai take rayuwa?Allah yasa ma dai basu mata wani abin ba""hmm Amin dai" Abba yace,dahaka dai sukayi sallama akan duk wani dan cigaba daaka samu zai sake kira,sannan ya tura mata hotunan gidan Abdallahn da garin dakomai daya dauka dazu,don dai ta gasgata don duk irin labarin dazaa bawa mutum bazai taba fuskanta ba gani ya kori ji inji hausawa.

Ai wayannan hotuna da mama tagani takuma nunawa su Safina dasuma hankalinsu in yayi dubu yatashi ne yakara tada mata hankali,bazata iya kara jurewa ba kuma,in bataga yarinyar nan ba hankalinta bazai taba kwanciya ba,take takira Abba tasanar dashi cewar fa suma suna hanya don bazasu iya ba,bazai iya hanasu zuwa ba,fatan Alkhairi kawai yamusu akan Allah ya kawosu lafiya.
Batareda wani bata lokaci ba kuwa suka fara processing tafiya,baa wani dau lokaci ba kuwa aka musu visa,itada Safina da sauda.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now