RUWAN DAFA KAI 2

1.5K 125 2
                                    

RUWAN DAFA KAI 2
Na SUMAYYA DANZABUWA

22

Kwanansu goma sha biyu a asibitin aka sallamesu bayan an tabbatar ta warke sarai sai dan abinda baa rasa ba,dakuma magunguna daaka hadata dasu.
Hakika kaunar dayake mata yanzu ta shallake hankali, wane tada?nan nan kawai yake da ita yana riritata kamar kwai,don shi aganinshi babu abinda yakai cs wahala,yanka mutum fa akayi aka fito da wani?tab,tabbas abin bana wasa bane,ahalin daake ciki ko kuda bayaso ya tabata,tabbas tawuce yar gata a wajenshi abindai sai wanda yagani kawai.

Dayake babu wani zancen taron suna dama,mai jego ma na fama da kanta,yarinya taci sunan Hajiyar Yusuf Maimuna,zaa dinga kiranta da Mimi,dukda dai inda zasuyi taron bazasu rasa mutanen gayyata ba,kasancewar sunada yan abokanai wayanda duk yawanci abokan karatu ne daaka hadu ko kuma mutanen su Aunty.
Itama Auntyn kullum tana nan sai dare take tafiya itace maiyiwa yarinyar wanka,tana kula da Amin,dukda mai dai koda yaushe yusuf din yana nan shima.
Wannan kenan.

Tunda farida ta turo sakon farkon nan, bata sake turowa ba sai yau,don tasha alwashin zatayi tayi ne har sai sanda yabata ansa,tukun.

suna zaune shida Abu suna hira wayarshi tayi kara alamun shigowar sako,zarota yayi don dubawa,kodaya duba din kuwa,irin kalaman rannan dai yagani tasake turowa,hakan ne yasashi jan tsaki afili,itadai Abu kallonshi take kawai batace komai ba,harya cillar da wayar gefe,kuma ko mai ya tuno yasake jawota yafara rubutu rai abace,don yazama dole ne ya taka mata birki bayason iskanci kuma da zakewa,wallahi shi yaji bakincikin bata numbar tashi da hajiya tayi,saboda yanata tunanin inda tasami numbar dama,to dasukayi  magana da Hajiyar rannan take tambayarshi ko faridan ta kirashi,yake cewa bata kira ba don yasan yana cemata ta kira ko ta turo sako,zata fara bin baasi, takuma sashi yayi abinda ranshi baiso ba,shiyasa gwara azauna abata nemeshi dinba,"wai waye ne haka,yake turomin da wayannan shirmen ne?babu suna bakomai ko kuwa ni Allahn musurune dazan gane bayan banida numbar?"ya tura mata,tareda ajiye wayar yacigaba da abinda yake,bama yaso yayi mita afili har Abun taji shiyasa yarike abin aranshi zuciyarshi na zafi,ita kuma tana zaune tana haddarta,don har malami ne da ita dayake zuwa suna karatu da yamma dasafe kuma ta zagaya islamiyyar bayan layi,tunda bata komai,taji karar shigowar sako wayartata,saida takai aya sannan ta janyo wayar taduba taga abinda yarubuto,bayan ko sa ran ganin ansar tashi batayi ba dama,"ikon Allah yaushe yusuf yazama haka?"tace afili, to amma yana nufin yamanta numbar tawa ne ko kuwa dai yaya abin yake"tace tareda sakin dan murmushi,"Allah sarki,kodayake komai na iya faruwa watakila mantawar yayi"tace zuciyarta kal don yanzu ita bata majin haushi,bata bata rai,to akan me duniyar ma nawa take,idan mutum ya yadda yayi imani dacewar zai mutu watarana kuma rayuwar ita kanta baa bakin komai take ba baya daukan komai dazafi,to ita kam akan haka take yanzu shiyasa takeyiwa mutane uzuri akoda yaushe,"farida ce"kawai ta tura mishi,tacigaba da abinda take.

Karar shigowar sakon yasake ji ya dauko wayar ya karanta,",mtsw yaja dogon tsaki,"to da cemiki akayi bansan kebace aikin kawai "yace afili,zantukan dayake ne da lamuranshi sukasa Abu sakin dan murmushi,don duk abinda yake akan idanunta kuma tasan kwanan zancen magana cedai dabatayiba kawai tunda baicemata komai ba,maida wayar yasakeyi aljihu bayan yasata a silent wai donma kartasake turowa har yaji kara ya dauko ya duba,sannan yacigaba dayiwa yarshi wasa.

,"mine"takira sunan nashi cikin sassanyar muryarta,"naam Angel ya akayi mekikeso"yace cikeda kauna da kulawa yana dan murmushi,"don Allah don Annabi kamanta daduk abubuwan dasuka faru abaya,ka yafewa maman Amin ka d....."nifa bacewa nayi ban manta dakomai ba,namanta dakomai nakuma yafe mata tun wani lokaci mai tsaho,zama da ita ne dai dakike da bukata bazan iya ba kiyi hakuri kinji"yace murya kasa kasa shima,"Amma d...."yakamata kisha maganinki yanzu,lokaci yayi"ya katseta tareda chanjazancen,yar dariya tayi kawai dubada yadda yayi maganar,itadai tasan harga Allah duk soyayyar dazai mata bazata taba kaiwa wadda yakewa farida ba,haushinta dai dayakeji ne yake fushi da ita har yanzu shiyasa duk yake wannan abubuwan amma dai bari ta rabu dashi komai lokacine,idan da rabon su sake zaman zasu sake dole ma kuwa"

Farida dai tana nan,tanata kara murmurewa tabbas tayi kyau matuka kammaninta sun dawo,tayi bulbul abinta,nutsuwarta da kamala kuwa hmmm abin sai wanda yagani.

Cikin ikon Allah,safeena tasami mijin Aure,wanda ko auren ma shi bai tabayi ba a baya,bayan kuwa yasan dacewar ita bazawara ce,amma ahaka ya amince zai aureta,bata bari tayi ganganci ba sun saba,bare har soyayyarshi tashiga zuciyarta ta mamayeta saida aka kammala binciki mai zurfi tukun,inda kuwa akayi saa Allah ya taimaka bashida wasu mugayen halaye ko dabiu hasali ma kowa yabonshi yake.
To irin wayannan ne mazajen aure.

Yanzu haka har antsaida lokacin aure wata uku masu zuwa inshaallah,farincikin su mama ai bazai misaltu ba don dama babu abinda take fata arayuwarta kamar Taga yayanta suna zaune lafiya gidan miji kamar sauran yayan duniya.

RUWAN DAFA KAI 2Where stories live. Discover now