_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
🔟
Da sauri ya fito daga office d'insa,
har yana tuntub'e, akan step ya tsaya yana hanga yarinyar da zai samu ya aika kiran su Sanah,
daga can nesa ya hango wata yarinyar tana k'ok'arin shiga Hostel get,
da k'arfi ya d'aga murya yace " hey,
yarinyar ta juyo a d'an tsorace,
ganin Sir Moli tsaye yasa jikinta d'aukar kerrrrma,
da sauri ta k'araso ta tsuguna a gabansa,
gaidashi take amma bai iya amsawa ba,
saboda yadda zuciyarsa ta gama jagulewa,
yace " ke ajinki nawa?Jikinta na tsuma tace " JSS2,
yace " kin san Sanah Hamraz?Ya tambaye ta idanshi na kanta,
cikin kerrrmar jiki tace " eh,
mamaki ne ya kama shi sosai jin ta santa,
kamar zai share sai kuma yace " ya akayi kika san su,
bayan ba class mate d'inki bane?Jikinta na rawa tace " kowa ai ya san su a makarantar nan,
" saboda me?Ya kuma tambayar ta a tak'aice,
yana yi mata tambayar ne dan yana san samun k'arin hujjar cin uban Sanah,
"tun ranar da suka daki Aunty Era suka zama popular's,
"Ok, maza jeki kira min su yanzu,
yayi maganar yana komawa cikin office d'insa,
da sauri yarinyar ta mik'e jiki na rawa tayi hanyar hostel,
a zaune ta iske su suna hira da Halan,
yarinyar tayi sallama, kana ta kalli su Sanah tace " Sir Moli na kiranku,
k'irjinta ta dafe had'i da zaro idanuwa waje,
tace " mu kuma?Yarinyar tace " eh ku yace,
Halan ta kalli yarinyar tace " waya ce ku kira masa?"Sanah Hamraz ta bata amsa,
ido Sanah ta kuma zarowa tace " na shiga uku me kuma nayi masa?Ta tambayi yarinyar, tace " ban sani ba, ya dai ce kawai na kira masa ku,
Halan tace " ya kika ga yanayinsa?Yarinyar tace " ban kula da fuskarsa ba dan kai na duk'e yake har ya gama yi man magana,
Yarinyar ta fad'i haka ne saboda gudun abinda zai je ya dawo,
dan tasan halin Sir Moli sarai,
Halan tagai dubanta ga Khulud ,
da jikinta ya fara rawa tun jin kiran da Sir Moli yake yi musu,
tace " me kuma kuka kuma yi masa?A tsorace Khulud tace " wacce ni, mai kai ba gashi,
ai sai dai ki tambayi Oga,
Halan ta kalli Sanah tace " yau kuma mai kika tarowa kanki?Kamar zatayi kuka tace " wallahi Aunty Halan tunda muka dawo ban sashi a ido na ba,
balle nayi masa wani laifin,
idon Halan na kanta tace " kin tabbatar?Kai Sanah ta gyad'a mata, cikin sanyin jiki suka mik'e had'i da zarar hijabansu,
Halan tace " Allah dai yasa alkhairi ne,
Sanah tace " kayya Aunty Halan kema kin san a kira mutumin nan babu alkhairi,
Halan tayi murmushi, tace " ku irink'a maimaita " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
ku kuma d'auke numfashinku,
ku karanta, Qulhuwallahu Ahad,
sannan ku maido da numfashinku ku karanta Nasi da Falak'i,
da لا حول ولا قوه الا بالله العلي العظيم,
har ku isa gare shi, in sha Allah duk girman laifin da kuka yi masa Allah zai d'ora ku a kansa,
cikin sanyin murya Khulud tace " to Aunty Halan mun gode,
kamar zata fasa ihu Sanah tace " wai ni meye dalilin kiran dayake mana?Halan tace " o! o! ni da nake nan tare daku ina zan sani?
" Idan kinje can sai ki tambaye shi,
ko idanki ya gane miki,
batare dasun kuma cewa komai ba suka fita,
addu'o'in da Halan ta gaya musu suke ta maimaktawa,
Moli nacan zaune kamar zai fashe saboda tsananin zugin da zuciyarsa keyi masa,
minta d'aya minti biyu sai da duba agogo had'i da jan tsoki,
kishingid'a yayi ya rufe idanta,
yana sauraren yadda zuciya ke azalzalarsa gami da bugawa da sauri,
a k'ofar office d'in suka ci burgi,
kowa yana kallan kowa still they're praying,
Sanah tace " kiyi sallama,
Khulud tace " inyi sallama kamar yaya?

YOU ARE READING
RASHIN SANI......!!!
Teen FictionHeart touching story. Lots of folks confuse bad management with destiny. Destiny is no matter of chance. It's a matter of choice's. It's not a thing to be waiting for, it's a thing to be achieved. Our destiny change's with our thought, we shall bec...