_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
3⃣2⃣
Cikin rawar jiki da matsananciyar kerrrma ya nufe su gadan-gadan,
Sir Moli na zuwa bayyi wata-wata ba ya makawa matashin saurayin gigitattun marika har guda hud'u a jere ji kake kauuuuuu,
a kid'ime Sanah ta d'ago kanta tana gyara tsaiwarta,
shiko yaron durk'ushewa yayi a wajen,
take jin sa da ganinsa suka yi d'aukewar wucin gadi,
yakai wajen minti biyu zuwa uku kana saurayin ya dawo normal,
cikin zafin rai saurayin ya d'ago cikin matsananciyar zafin zuciya ya d'aga hannunsa da niyyar rama marin da Sir Moli yayi masa,
cak ya tsaida hannunsa ganin wanda ke gabansa tsaye cikin wani irin yanayi,
a d'an tsorace saurayin ya zaro ido waje,
had'i dayin baya yana sauke hannunsa,
a k'ufule Sir Moli ya kalle shi da jajayen idanuwanshi,
yace " do you want hit me!?Ya tambayi yarin yana k'ara matsawa kusa da shi,
sadda kansa k'asa yaron yayi cikin alamun tsoro yana ja da baya,
" oya hit! me Sir Moli ya fad'a a tsawace,
" I'm sorry Sir ban san kai bane,
" I said hit! me Sir Moli ya kuma fad'a cikin d'aga murya da hargowa,
maganar da Sir Moli yayi da k'arfi ce ta jayo hankalin sauran jama'ar dake wajen,
kowa ya tsaya cak had'i da mayar da hankalin su gare su dan ganin abinda ke faruwa,
a kid'ime saurayin ya bud'e baki da niyyar yin magana Sir Moli ya k'ara maka masa gigitattatun marika biyu,
take bakin saurayin ya fashe jini ya fara zuba,
ganin jinin yasa Sanah zaro ido had'i da sanya hannayenta ta rufe bakinta cike da tsoro,
" sorry Si........!
kafin yaron ya k'arasa Sir Moli ya k'ara maka masa mari,
yana cewa " am I your mate?Kai yaron ya girgiza masa cike da tsoro dan yanayin Sir Moli kad'ai ya isa ya d'imauta yaron,
mari Sir Moli ya k'ara maka masa yace " dan uwarka ba magana nake yi maka ba?Yaron zayyi magana Sir Moli ya k'ara d'auke shi da mari,
daga yaron har sauran jama'ar dake wajen babu wanda yasan takamaiman laifin da yayi masa,
ganin Sir Moli yana niyyar illata yaron da gigitattun marikansa yasa Sanah saurin shiga tsakaiyarsu,
ta tare Sir Moli hawaye na zuba daga idonta ta take girgiza masa kanta had'i da cewa " no please!
d'ago jajayen idanuwansa yayi ya zuba cikin nata yana kallan cikin kwayar idonta,
" move! ya fad'a a fusace...
" please! ta kuma fad'a kuka na neman kufce mata,
da k'arfi Sir Moli yace " I said move!
yadda yayi maganar yasa duk ilahirin jikinta d'aukar tsuma da kerrrma,
sosai bala'in tsoro yayi masifar shiga jikin Sanah,
zagaye ta yayi yana sake nufar yaron dake durk'ushe yana goge jinin dake zubo masa,
dakewa Sanah tayi had'i da sake zagayawa ta shiga tsakiyarsu,
ta jefa idanta cikin nashi tana kallanshi tarrr ido cikin ido,
cike da tsantsar tsiwa tace " wai meyasa kai azzalumi ne?"If I say I love him what will you do?
Ta fad'a k'asa-k'asa yadda babu mai jinta sai shi kad'ai,
ido ya zuba mata cikin takaici da tsananin zafin da zuciyarsa ke yi masa,
cikin tsiwa Sanah tace " I hate you and I love h.......
tassssss tassss Sir Moli ya d'auke ta da gigitattun marika itama,
babu wanda yaji abinda tace masa sai k'arar marin da yayi mata suka ji,
cikin zafin rai Sir Moli ya k'ara nufar yaron gadan-gadan,
da sauri Sanah ta kuma shan gabansa hannunta dafe saman kuncinta,
tace " wallahi matuk'ar ina raye baka isa ka sake tab'a shi ba,
abinka da mai bak'ar zuciya,
wanda yake dama a k'ufule aiko cikin zafin rai ya rik'o hannunta ya jefata gefe,
Sanah ta zube k'asa, da sauri ta kuma mik'ewa ta k'ara nufarsa tana k'ok'arin k'ara tare shi,
dan kar ya kuma dukan yaron,
amma kafin ta k'arasa har ya isa ga yaron ya cakumo wuyanshi ya k'ara kifa masa mari,
da k'arfi cikin tsiwa Sanah tace " I HATE YOU!!!,
and I will never accept you as a lover,
cak Sir Moli ya tsaya had'i da sakin yaron ya fad'i k'asa,
baya yayi ya koma jikin motarsa,
ya kifa kansa yana ji kamar yayi hauka,
a hankali ya d'ago yasa hannunsa ya dafe motar had'i da sunkuyawa yana kallan saman motar daga gaba.

VOCÊ ESTÁ LENDO
RASHIN SANI......!!!
Ficção AdolescenteHeart touching story. Lots of folks confuse bad management with destiny. Destiny is no matter of chance. It's a matter of choice's. It's not a thing to be waiting for, it's a thing to be achieved. Our destiny change's with our thought, we shall bec...