_*RASHIN SANI.......*_
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_'''Wattpad:HauwaAUsmanjiddarh'''
6⃣8⃣
Murmushin bak'in ciki da takaici Hanash yayi gami da sunkuyar da kanshi k'asa hawaye na zubo mishi,
ya dad'e a haka kana ya d'ago kanshi ya kalli Mimmee ya kuma yin murmushi a karo na biyu,
dake nuni da tsantsar bak'in ciki.....!,
kallanshi ya mayar ga Sir Moli da Sanah da har lokacin suke zube a k'asa,
a hankali ya kawar kanshi gefe, cikin muryar kuka yace,
" Mimmee tun farko danayi k'ok'arin yin magana kika dakatar dani abinda nayi niyyar yi kenan kika dakatar dani.....!,
wanne marar san rahamar Allah da rashin tausayi gami da tawakkali ne zai shiga tsananin masoya irin wad'annan.......!?"Ko makaho ya kalli Aryan da Sanah yasan akwai soyayya ta gaskiya a tsakanin su,
duk rashin imanin mutum dole ya tausaya musu,
idan har son da nake yiwa Sanah na gaskiya ne ai zanfi kowa san ganinta cikin farin ciki,
nafi kowa san kasancewar ta cikin walwala da annuri a rayuwar ta,
a soyayya an yarda akwai sadaukarwa,
Allah da kanshi yace duk masoyan gaskiya wad'anda suka so junansu,
bisa gaskiya da amana akan tafarkin Allah zai sanya su a aljanna,
kamar Lailah & Majanun
a hankali ya sanya hannu ya goge hawayen dake ta sunturin zubo mishi,
yadda kasan an bud'e bakin teku,
cikin nutsuwa Sir Moli da Sanah suka mik'e tsaye, cike da tsantsar murna da farin cikin abinda Hanash ke da niyyar yi,
" ka tabbatar zaka iya auranta a matsayin BAZARAWA ba BUDURWA ba, mai 'ya'ya har uku.......!?Hanash ya fad'a idanshi kan Sir Moli,
murmushin gefen baki Sir Moli yayi gami da sunkuyar da kanshi k'asa hawaye na d'iga daga cikin idonshi,
k'ok'arin magana ya soma yi sai kuma yayi shiru,
hakan da yayi yasa gaban Sanah ya shiga dukan uku-uku,
ya dad'e a haka kana ya d'ago kanshi ya kalli Hanash cikin nutsuwa ya soma magana,
" kyawun mace kamar kyendir ne, dukda ana samun launika daban-daban,
hasken dayake bayarwa iri d'aya ne kuma zayyi ta bada hassken har sayya mutu ko ya k'are,
shima kyau kamar haka yake zayyi ta bada shek'i har sai tsufa, ko mutuwa sunzo,
saboda haka mahimmancin abu ya dogare ne ga amfaninshi,
idan budurci yana da wata daraja a duniya da Allah bai bawa Annabi Muhammad SAW Nana Khadija,
ya aura tana a matsayin bazarawa kuma wacce ta girmeshi ba,
da budurci yana da wata fa'ida da Allah bai sanya duka matan Annabi Muhammad SAW wanda akayi duniya da lahira dominsa,
akayi wuta da aljanna dominsa,
akayi su kansu matan da auran damin shi dukansu sun kasance zawarawa ba,
sai guda d'aya tak ce ta kasance budurwa a cikin matanshi gudu 11 sun kasance zawarawa,
ka sani ya auri Nana Khadija tana da shekara 40 shi kuma yana 25 ne,
sai Zainab, Habiba, Maimunat, Safiyya, Zuwaira, Hafsatu, Hindatu, Saudatu, Mariya,
Nana Aisha ce kad'ai ce aura tana a matsayin budurwa, dan haka auran bazawara ga saurayi sunna ce mai k'arfi,
ba'ad zalika,
duk duniya babu yare da k'abilar da take wulak'anta aure kamar k'abilar Malam BAHAUSHE,
babu wad'anda basu san daraja da k'imar aure ba irin HAUSAWA,
babu wad'anda basu d'auki saki da mutuwar aure komai ba kamar HAUSAWA,
babu wad'anda suke wulak'anta aure kamar HAUSAWA, babu k'abilar da ZAWARAWA sukayi yawa da mace-macen aure kamar a k'asar HAUSA,
wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba, duk duniya babu inda ba'asan dajarar aure ba sai a k'asar Hausa,
kasan me yasa.....!?Sir Moli ya tambayi Hanash.....!
da ido kawai Hanash yake binshi,
Sir Moli ya cigaba da magana,
" saboda yawancin mu musulmai ne, amma kwata-kwata bama bin dokokin Allah wajen neman aure,
bama yin abinda yace, bama nutsawa wajen zab'awa kan mu abokanan rayuwa,
tun daga waje mun gaba d'ebe albarkar auren,
mun gama janye duk wani tallafi na auren,
an gama cinye juna tun a titi,
yanzu biki idan ba'ayi bidi'a anyi free wedding pictures ba ai mutum bai waye ba,
a fito ayi bidi'a da kid'e-kid'e da raye-raye shine burgewa,
a tattaro shaid'an da jama'arshi da al'ummarshi an jajige an d'au magana shine burgewa,
dan Allah fad'a min ta yadda aure zayyi albarka....!?

YOU ARE READING
RASHIN SANI......!!!
Teen FictionHeart touching story. Lots of folks confuse bad management with destiny. Destiny is no matter of chance. It's a matter of choice's. It's not a thing to be waiting for, it's a thing to be achieved. Our destiny change's with our thought, we shall bec...