BABI NA UKU

1.1K 101 2
                                    

RANA DUBU....3

©NWA

©MAMANHANIF

Editor:Ummul Fadeela

***Mutuwar Fateema mutuwa ce wacce ba'atab'ayin  wacce ta tab'asu kamar ta ba, kafatanin yan uwa da abokan arziki sunyi kukan rashin ta sabida nagartar ta tareda kyakyawar mu'amalar ta, don macace mai hakuri da matukar kirki kowa ya budi baki saiya fadi dunbin alkairin ta garesa,

Bazan iya misalta irin yanayin da mijin ta yashiga ba sakamakon juriya da tawqkalli tareda dunbin nutsuwa da Allah ya wadatashi dasu Wanda suka boye ainihin rudanin dake cikin zuciyar sa suka haddasa masa kukan zuci Wanda yafi na fili kuna, gefe daya kuma? Ga tsantsar tausayin yaran sa wanda yasoma tunanin kalubale dazai tunkara a gaba sakamakon maraici,

Hakanan suka cigaba da amsar gaisuwa har sati ya zagayo akai addu'ar bakwai aka share zaman makoki, ranar saita zamewa adamu tamkar ranar mutuwar don sai yaune ya tabbatar sunyi maraici,

Bayan sallar la'sar ne 'yan gidan su Fateema suka shiga shirin barin gidan don komawa gida nan suka kumaiwa juna ta'aziyya  kaf dinsu sai mutuwar tadawo musu sabuwa, kafatanin su tausayin yaran shike daga hankalin su don tunda akayi rasuwar ganin yan uwa yadebe musu kewar uwar ayau kuma da sukaga kowa yana sallamar tafiya sai jikin su Yy la'asar sun rike Maryam Sam sun hanata sakewa, haka ma da zasu tafin suka cika gidan da kuka fafur sunki barin jikin ta itama ta kankame su batada niyyar sakin su, wannan shiyayi sanadin zubar hawayen uban su Wanda yayi kukan dabai taba tunanin zaiyi shiba duk jamaar da sukai saura sharar kwallar suke don tsantsar tausayin yaran da uban su,

Nan dai kakar su mahaifiyar adamu wacce ta kudiri tafiya dasu don rikon su yadawo hannun ta,da kanta tashiga hado musu kayan su ta damkawa Maryam d iyayen fateema don dama yaran sunfi sabawa dasu, sunkwa ji dadin hakan don haka suka karasa sallama suka dau kayan su suka tafi, har bakin mota sukai masu rakiya suna sharar hawaye adamu kuwa jiyake tamkar yabisu y amso yaran haka nan ya daure zuciyar sa ya hakura ya koma cikin gidan ya shiga dakin fateema ya dasa wani sabon kukan don jiyake a ransa kukan shine samun salama a cikin ransa.

A washe garin ranar ne hajiyan sa itama takoma natq gidan tareda yan uwanta Wanda sukai saura, shima d'in a ranar yayi sallama da mahaifiyar sa yakoma gurin aiki sa Wanda yake aiki a wani kamfani dake garin Kaduna garin gwamna, bayan yaje yaga yaran sa ya barmusu duk abinda yasan zasu bukata kan yayi sallama da sirikan sa ya dau hanya.

RANA DUBUWhere stories live. Discover now