26

781 69 0
                                    

M, 2/15/2017] Ummu Fadimatu: RANA DUBU....26

©NWA
     ©MAMANHANIF

EDITOR:UMMUL FADILA

***Ranar lahadi itace ranar da Aka kai Amarya Dan kareran gida mai sashe hud'u sashe daya cikin hudun nan ne sashen ta a yayin da wancen sashen yake mallakin iyayen mijin ta, A gaskiya bazan iya fasalta kyawun gidan ba tareda kayan Alatun dake cikin gidan a takaice dai zan iya cewa" gida ne mai kyau da tsari kirar zamani Wanda yaji kayan more rayuwa babu ce kawai babu a cikin gidan.

Ganin daular da Maryam ke ciki ya kara hura wutar hassada Wanda 'yan uwan ta ke mata, duk da wasu daga cikin su jikin su yayi sanyi a yayin da wasu sukace"ayi dai mugani! Ba girin girin!. Duk da Amina taso ta shanye bakin cikin dake dankaren cikin ranta amma saitaji takasa har saida ta matse kwallar bakin ciki a yayin dataga Anshiga da Maryam gurin uwar mijin ta cikin Shiga ta Alfarma ga wata irin kauna da kulawa da suka shiga nuna mata tamkar zasu maida ta ciki don so, duk da yayun ta na kokarin ganin ta shanye abinda ke ranta amma ina! Ai karshema sai silalewa tai tabar gidan Amaryar don gudun kar zuciyar ta tabuga don bakin ciki, sauran yayun ta su hud'u ne suka daure dai aka gama komai dasu suka biyo sauran ayari aka koma gida tare dasu.

A b'angaren Amina kuwa? Kasa komawa tayi gidan su don bata son taji ana zuzuta kyan gidan Amarya Wanda tunda akaje yimata jere ake zuzuta kyan gidan itakwa jitake tamkar ta shakesu don takaici yake kawai take hassadar ta taki boyuwa duk da tayi kokarin boyewar, a gidan ma data koma ba sanyi taji ba, don ta tarar da Adamu har yasoma bacci kasancewar goman dare ta gota shibai ma tsammaci dawowar ta yau dinba don sunyi sai angama biki kaf zata dawo kawai saiji yayi ana kwankwasa kofa, nan yataso cikin mayen bacci cike dajin haushi don dakyar yasamu baccin ya d'aukeshi Yajima a kwance kan yayi baccin, yana bude kofar dawa Allah ya hadashi? Nan ya sauke mata kwando kwando na masifa, nan ta zube a falon tana kursheken kuka tarasa me yake mata dadi a rayuwar ta saida tayi mai isarta tukun sannan takoma nata d'akin cikin sanyin jiki tarasa meyasa Maryam tafita komai na rayuwar duniya har tambayar kanta take shin dame Maryam tafita? Ita bafinta kyau tayi ba amma kowa Maryam hatta Abinda akaiwa Maryam yafi nata ko Anan an nuna mata banbanci.

****

A b'angaren Amarya kuwa? Bayan yan kawo Amaryar sun watse daga ita sai kanwar muktar Ummi wacce Maryam ta hanata tafiya don tsoro takeji na rashin sabo bataso a barta ita kadai a tafkeken d'akin barcin ta Wanda yagaji da had'uwa.

Suna zaune dai suna jiran shigowar angon Wanda akace sunacan gurin party wanda abokan sa suka shirya masa duk cikin tayashi murnar auren Wanda ita Amaryar wacce aka shirya domin ta ta kekashe kasa tace babu inda zata tagaji, sun shiryane daga gurin party zasu zarto da Amarya gidan kan tayi musu tawaye da cewa" gwara su barta yanda kowacce Amarya iyayenta ke kaita dakin mijinta itama akaita asirinta a rufe bawai abokan miji d kawaye sui mata rakiya ba"

Wajen misalin karfe sha biyun dare sukaji shigowar mota cikin sashen nasu, cikin hanzari Ummi wacce ke tayata jira tamike ta leka ta tagar d'akin tace" yauwa ga bros muktar yadawo dama nagaji bacci nakeji" nan taiwa Maryam sallama ta tafi don bataso yashigo tana d'akin.

Cikin muntuna kad'an ya bayyana cikin dakin wanda tunkan ya karaso turaren sa ya shaida mata isowar tasa, k'udun dune take cikin mayafi kanta A k'asa tana jiran yayi mata sallama ai batai aune ba saijin hannun sa tayi cikin nasa yana kokarin d'agota aiba shiri ta mik'ar da kanta, itadai batare da tasani ba ta tsinci kanta yana hajijiya da ita a tsakiyar tangamemen gadon su  take mayafin data lullub'a yayi nasa waje har ribom d'in kanta saida yayi nasa guri, karad'in sa kawai ke bugar kunnenta takasa tantance meyake fad'i tasan duk a cikin farin cikin ganin zuwan wannan ranar ne,

Itadai bata samu nutsuwa ba saida tajita a saman kirjin sa maiyi cilli da ita a saman tayal ba. Lol

RANA DUBUWhere stories live. Discover now