Page 01.

3.3K 98 4
                                    

*BAK'ON LAMARI*.
Na Safiyya.

_Wattpad @Mrsjmoon._

*Alhamdulillah ina yi mana barka da kammala azimin Ramadan lafiya dafatan Allah ya amshi ibadinmu yasa kuma muna daga cikin bayi 'yantattu. Ina rok'on Allah ya k'ara tsare jinmu, ganinmu, harshenmu tare da farjinmu, ya k'ara mana hakuri da juna ya yalwata k'irjinmu da yawan yafiya adikkan lamura, Allahumma Amin.*

'''To ga dai 'yar uwanku Safiyya (Mrs j moon) d'auke da wani labari mai suna a sama ina fatan zai nishad'antar daku gami da ilmantarwa haka ina addu'ar Allah yayimin jagora akan dik abinda zan rubuta yazamo mai amfanarwa ne ya haneni fadar abin ashsha biy jahiy Nabiyyi S.A.W. Amin.'''

Bissimillahi rahamanin rahim.
_Allahumma salli ala Muhammadu wa'alaa azwajihi wa zurriyyatihi wa'alaa jami'i nabiy'ina walmursaliyna walmala'ikatihi walmuk'arrabina wa jami'i ibadillahi salihiyna._

Page 01.

"Abu Sufyan! Abu Sufyan! Abu Sufyan!!!."

A firgice ya farka sakamakon amon sautin muryan Abbansa daya doki dodon kunnuwansa, cikin k'walla masa kira.

Saukowa yayi a hanzarce daga sama gadon, ya janyo jallabiya milk ya zira tare da d'aukan carbinsa fara sol wanda dama yana tsaka da ja ne barci ya d'aukesa.

Wani kiran sunan nasa yakuma jiyo mahaifinnasa na ambata da amon da yafi na farko k'arfi wanda tunda yake baitab'a jin Abban nasa yayi masa kira irin wannan mai cike da k'araji ba a tun tsawon rayuwarsa.

Cikin gaggawa yake saukowa downstairs yana mai ambaton sunar Allah ta hanyar jan carbin hannunsa, a matakalan k'arshe yaja ya tsaya gabansa na matsanancin bugawa.

Gabaki d'aya al'umman gidan sun hallara a parlorn sunyi cirko - cirko cikin jiran tsanmani, sabida suma sautin kiran sunar Abu Sufyan d'in ne yajanyo hankalinsu har suka iso wurin.

Kallonsa ya sauke kan Abbansa sai yayi hanzarin kauda kansa gefe sakamakon wani tsanarsa da ya hango cikin idanun mahaifin nasa, atake mafarkinsa ya dawo masa tar tamkar yanzu yakeyinsa

'Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, Allahumma ajirni bi masibati wa akalifni khairan minha.'

Ya ambata cikin ransa cike da karyewar zuciya.

Da Umma ya had'a idanu abin mamaki sai yaga kamar tana cikin nishad'i, kureta da kallon da yayi ne sai ya hango ashe damuwace kwance a saman fuskanta, juyowa yayi wurin Umminsa nanma karo yaci da matsanancin damuwa saman fuskanta lamarin da yakuma jefasa cikin tashin hankali, ganin hawaye nason zubo masa sai yayi hanzarin kauda kai yana mai bin inda yayunsa maza biyu suke tsaye, suma dik fuskokinsu d'auke ya ke da tarin damuwa.

Sake sauke subansa yayi akan Abbansa cike da marairaita, langab'e kai yayi dan neman affuwa tun kafin yaji laifin da ya aikata masa.

A fusace dattijon ya tako ya iso inda yake ya d'auke shi da mari mai kyau tare fizgoshi ya ingizashi hanyar fita parlorn yana mai cewa "Yi maza ka ficemin a muhalli, tun ban illataka ba domin ni Alh. Ubaidallah bana son ganinka sam a rayuwata, na tsaneka Abu Sufyan! Dan haka bani ba ka, kuma ban amince maka da ka rab'i dangina ba, burina takafi can inda bazan kumajin labarinka ba har abada."

Salati mai sauti parlon ya rud'e dashi, dik sukayo kan Abba yayi hanzarin d'aga masu hannu fuska a had'e, dik suka ja da baya.

Yayin da Abu Sufyan yaji kamar ba a duniyar yake ba, jiwane yasoma d'ibansa Salima wacce fitowarta kenan ta hango yana layi zai fad'i, k'ara ta k'walla cikin fad'in "Ya Sufyan!."

D'aga mata hannu yayi cikin juriya ya ja k'afarsa zuwa gaban Abba ya sunkuya tare da zube hannayensa saman k'afafuwan Abban, a hanzarce ya janye k'afarsa yana mai nuna masa hanya "I said get aut! ko ranka ya b'aci yanzu bada jimawa ba dan wallahi ayarda nakejin tsanarka zan iya harbeka ka mace ba damuwata ba ne."

BAK'ON LAMARIWhere stories live. Discover now