Page 03

1.1K 49 2
                                    

*BAK'ON LAMARI.*
Na Safiyya.

_Wattpad@Mrsjmoom._

*It's ur page my mentor😍 Bahijja (Bebeelo).*

Page 03.

Gaban family picture nasu ya tsaya sadda ya fito, shiru yayi tare da tsirawa photon idanu yana tuno irin tarin k'auna gami da shak'uwar dake tsakanknsa da Abbansa amma sai gashi a dare d'aya komi ya rikid'e zuwa k'iyayya ta ban mamaki.

Cikin sanyin jiki ya mik'a hannu ya shafi fuskan Mahaifin nasa ya sauke hannun kan face d'in Ummiensa, zuciyarsa ce ta karya ya zube gaban photon yana cigaba da kallonsu, kalaman Ummie ya tuna a wani shud'add'en lokaci can, inda takan ce masa.

"Abu wannan fifikon da Alhaji ke nuna maka ba abu ne mai alkhairi ba, ina guje maka kiyayya irin ta 'yan uba dik da banjin haka zai faru amma dai raina baya son lamarin sam dan in so yayi yawa wata rana k'iyayya ke rikid'ewa sabida haka karik'a nusar da Alhaji a fakaice da ya daina nuna maku banbanci ko dan kiyaye dokokin Allah."

"Uhmm Ummie ga hasashenki nan yau ya zama gaskiya.

Ya furta hakan a fili.

Motsin tak'un tafiya yajiyo wanda ya tabba na Abba ne, shi yasanya shi barin wurin a hanzarce.

Site d'in Umma ya nufa, kafin ya isa ya dai-daita kansa.

Zaune ya cinmata a parlor, yayin da Bello ke sunkuye gefenta da alama magana takeyi masa, shigowarsa yasa Bellon komawa zaune gefenta, kamar zai shige jikinta

Gabanta Abu Sufyan ya durk'usa yayi shiru, hannunta ta d'ora saman kansa tana cewa.

"Kayi hak'uri Abu Sufyan, wannan lamari k'addararka ce tazo da hakan amma ni da 'yan uwanka zamu dage wurin yiwa lamarin addu'a akan Allah ya daidaita komi."

"Nagode Umma, yanzu zan wuce Maradi gidan Uncle Ishaq."

"Oh can kanufa?"

"Eh."

"To Allah ya tsare hanya, in kasamu isa ka gaisarmin da Jidda tare da k'anninta."

"Insha Allah zasuji."

Daga haka ya mik'e yana duban Bello yace "Abokin fad'a sai watarana."

Shiru Bello yayi, ganin yak'i amsawa sai ya dafa kafad'arsa ya matsa yace.

"Yaya Bello ina sonka wallahi sosai zanyi kewarka."

Cikin sheshshekan kuka Bello ya amsa da "Wallahi nima ina sonka d'an uwa."

Sai ya mik'e suka rungume juna, wani abu ya mintsili Umma a zucci ta rintse idanu, lallai ba shakka tausayin yaron ya kamata ainun.

"Kuyi hak'uri ai ba rabuwa na har abada zakuyi ba."

Umma tace dasu yayin da take raba tsakaninsu.

Da gudu Bello ya nufi bedroom d'in ta dan bazai iya ganin tafiyar d'an uwansa ba.

Shi kam Abu Sufyan ficewa yayi cikin sharan hawaye, dik da rashin jittuwarsu amma ahakan yanajin k'uncin rabuwarsu da juna.

A harabar gidan ya tsaya yasoma waige - waige ko zai hango inda Bashir da Salima suke.

"Gani nan d'an k'anina, farin cikinmu"

Bashir yace dashi hakan cikin murmishin yak'e.

Rungumesa Abu Sufyan yayi tsantsan "I will miss you Yayana mai sona fiye da kansa."

"Nima haka k'anina sosai zanyi kewarka, wallahi kasani ruhin Bashir na tare da kai a ko wani second na fitar numfashinsa, fatana tare da burina shine alkhairin Allah yayi ta samuwa agareka."

BAK'ON LAMARIWhere stories live. Discover now