Kaine Rayuwata 14

1.5K 110 0
                                    

Kaine Rayuwata❤😭😭

By; Najaatu shehu naira

FKD Fans Writers 《《 14 》》

Saif yakalleta yace "shikenan anraba gardama, kingasun iso, muje na bude maki kofa kibisu",
ya janyota ta 'kan'kame hannunshi atsorace tace "kayi hakuri, nidai kayi hakuri kabarni nawuce, kumama inkana ganin ka taimakenine,
ainima na taimakeka, inbaccin ni wlh da Dauda ya kasheka".
Yana janta yake bata amsa yace "mainaimai dazai kasheni toh?, kinga kema yanzun saiki mutu bakiji baki ganiba kiji inda dadi ko?".

Yaja yabude 'kofar saiga Ladan, Saif cike da mamaki yace "kaine dama?"
Zinaru tayi doguwar ajiyar zuciya,
Ladan yace "yan samari nazo kiran sallar farko ne,.
yamaida kai gun Zinaru, dukda duhune zakasan eh lallai macece yace "wannan fa, daga ina?"
ya tambaya yana kallon Saif, cikin i'ina yace "eh eh  kan......kan...watace".

Ladan yace "tototoh  nafahimta, aidakunsan da mace kuke tafe saiku aikota cikin gida,
dukda 'kanwarkace kasan baidace mace acikin samari kamarku ba, shi shedan la'anan nene, danhaka saiku kiyaye gaba dan Allah",.

Saif ya saki hannunta takoma ciki, yakalli Ladan yadan sunkuyar dakai yace "Eh hakane mungode,
Gobe saita kwana gidanka"
Ladan yace "to madallah".
"Saif yadawo ciki yana ajiyar zuciya, baisan daliliba amma ganin Ladan ne ba Yarima shima hankalimsa ya kwanta",.

**************************
Daddy ke magana a waya mommy na gefensa, ya kwashe labarin komai ya gayama manager kafar sadarwa, kan tafiyar Saif yace "tun daga ranan da suka tafi, har yau ban'kara jinsa ba Manaja, kasan halin yaran yanzun! 'Karya yaimin zaije abroad,
nadauka wata babbar 'kasa zashi on trip shida abokansa, Ashe nan 'kasa Nigeria yatsaya".

Manager ya katse maganar da "toh yallabai ko wani ya kiraka akan batunsu ne? ko akan batun shi Saif din? Kasanfa 'kasarnan ta 'baci da kidnapping".
Gaban Daddy ya fad'i cikin hanzari yace  "NO NO NO NO insha Allah he is safe babu wanda yakirani,
Pls just track his number within a minute am waiting.."......... 
Manager yace "okay Sir turomin number zamubi diddigin layin yanzu mu turoma da duk wani information",
Daddy yace "nagode ina jira",
ya yanke wayar.
Yakallah gunda Mommy ke tsaye yace "amma Salma kinsan bansan aimin tsaye a kai ko? Kekam wlh bansan wacce irin mace bace, bakisan kwata-kwata ta hanyar da ake rarrashin miji inyana cikin musiba ba",.

Mommy tayi ajiyar zuciya bata tanka maiba, takoma tazauna kamar mai nazari ,.
Daddy yabita da kallo, chankuma saiga hawaye kan fuskarta, yataso cikin nutsuwa yadawo gefenta ya dafa kafadarta yace "a'ah subhanallah, hawayen na mainene? kiyi hakuri karki fara, kema nasan kindamu tunda 'Danki ne dole kidamu sorry kiyi hakuri kitsaya nima ina jiran respond ne,
kidaina 'daga hankalinki karki sama kanki hawan jini".
Zatai magana taji wayarta na ringing dasauri ta duba wayar,.

Hajiya maryam ce mahaifiyar Nazir takira.
Ta kallah Daddy cikin sanyin murya tace "Hajiya maryam ce kekira",
Cikin rashin fahimta yace "wacce Maryam kenan?"
Mommy tace "Mahaifiyar Nazir,
abokin Son, matar tsohon minister of Education Alhaji jibiril, kaganeta?"
Kafin ya bata amsa gudun kar wayar ta tsinke tadauka tare da Sallama,
Hajiya Maryam ta amsa cikin raunarniyar murya tace "Mrs Sadiq ko kinji labarin Nazir, ko kunyi waya da 'Dan wajanki Saif?"
Bata jira amsar Mommyba taci gaba da magana "Wlh Mrs Sadiq tunda yatafi ban'karajin labarinsa ba,
wayarsa nakira-nakira tun tana ringing ba'a dauka harta daina shiga,
shine nace bari nakira, dukda subhi ne nakasa rintsa idonane tun daran shekaranjiya shiyasa nakira,
kiyi hakuri inna tasheki daga barci, nace bari naji tagunki".

Mommy tagirgiza kai tace "hmmm Hajiya Maryam wlh nimadai taguna haka d'inne,
bamu samun nutsuwa bare barci yazo mana saidai addu'ah,
kuma karki damu yanzunma ansa abi diddigin layin Saif, za'abisu dan aji lafiyarsu"...........
Jin 'karar text yashigo wayar Daddy,
Mommy tayi saurin sallamar Hajiya Maryam tace "duk abunda akwai zankiraki insanar dake insha Allah".

Kaine Rayuwata😭❤❤ CompleteМесто, где живут истории. Откройте их для себя