Kaine Rayuwata 29

1.8K 138 8
                                    

Kaine Rayuwata😭❤❤

Written By: Najaatu Shehu Naira

FKD Fans Writers 《《 29 》》

Murmushi tasaki cikin sanyin murya tace "Yaya Saif"
Hararar da yajefeta dashi yasa nandanan ta shiga taitayinta,
Yafito da'ita daga motar ya rufe murfin gwarab kamar tashin hankali,
Yana tsaye yana huci suna kallon kallo da Mr Aminu da yafito yana 'karemai kallo kamar ba Saifallahin da yasani ba,
Uffan ya kasa cewa banda huci da harara da yake sakarma Mr Aminu, chan yayi tsaki yaja hannun Zinaru suka shiga ciki,.
Mommy da Daddy na parlour ko kallon inda suke baiyiba, zuciyarsa na turnu'kui'kui dushu-dushu yake ganin hanya, yana tafe tana binsa sukahau staircase yana ri'ke da hannunta har dakinsa,.
Ya zaunar da ita gefen gado idanunsa jajir yace "ke kinasan zama dani?" Kamar saukar aradu taji tambayar danhaka tarasa tayi sai 
Shuru tana kallan kwayar idonsa da yachanza launi yayi cikiciki ko kwayar idon ba'a iya tantancewa,
Ya buga mata tsawa yace "kiban amsa nace kinasan zama dani ko bakyaso?"
Nan danan ta razana cikin furgici da tsoro Zinuru tahau girgixa kai tace "A'a Yaya wallahi banaso, banason zama dakai"
ganin ya zaro idanun da suka shishshige ta tashi da gudu tabar dakin,,
Ya buga hannunsa jikin bango yace "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un", lokaci daya 'kafarshi takasa daukan gangan jikinsa, yafad'a kan gado yayi dogon ajiyar zuciya, maganarda Zinaru tayi ke kashemai gabbai suna shiga cikin bargon jikinsa, aranshi ya maimaita "Saif batason zama dakai, bataso"
Kamar maishirin kuka ya langwabar da kansa, baibar addu'ah ba aransa har saida yasamu nutsuwa,
Ahankali yake tunanin abunda kefaruwa tsakaninsu (recall) yasa tafin hannunsa ya shafa fuskansa yace "Saif u being little bit harsh, kana zafafawa gaskiya, shiyasa tace zata tafi badan batason zamaba, and you knw she is not even Your girlfriend or wife, kasama ma yarinyar mutane lafiya, in mijin nema aminu is well deserve"
Kamar wani ke kintsamai yahau girgiza kai, azahiri yace "eh ammadai mijin bana Zinaru ba, she deserve better" yaja tsaki yabar dakin yafada dakinta,

Ta tasa akwati gaba tana faman kuka, daidai ta kira layin Hajiya tana ringing yashigo,
Sallamarshi da yadda yake sanda kamar mara gaskiya yasa koda Hajiya ta dauki wayar tana kwada Sallama Zinaru bataji ba, idonta nakan Saif har yazo ya kar'be wayar dake hannunta ya yanke kiran (hangup) yazauna kusa da ita,
Sunfi munti biyar babu wanda yacema wani 'kala harsaida Saif yagaji da zaman shirun,
Cikin sanyayyar murya mai dadin saurare yace "kinshirya tafiyarne?"
Bata kalleshiba ta gyada kai tace "eh"
Yanda ta amsamai yaji kamar an dokamai mari akan kuncinsa yace "okay, toh shirya inkaiki, ina zaki?"
Da dukkan alama maganar baimata dadi ba, tsammaninta zai hanata or something of dat nature, wit her disappointed face tadago kai sukai 4eyes,
Duk yadda taso tajanye idonta akan nashi ta kasa, ta narke cikin kallan kwayar idonsa da suke sparkling, tarasa haka idonsa suke kodai ita daiy take ganinsu haka,
Cikin muryar da bata futa tattare da shagwaba ta langwa'be fuska tace "Yaya intafi?"
Yar yaji ajikinsa, tsam yamike dan yadda tayi maganar ji yake kamar ya daukota yasata akan kirjinsa ya rungume.
Kan kirjinsa kawae? a'a jiyake tamkar yabi duk wani gabbai najikinta da kiss ko hakan zaisa yarage jin irin matsi da zuciyarsa takemai akan Yarinyar,.
A tsaye yake kwayar idonsu nakan juna yace "a'a karki tafi," yafada atakaice,
Ji tayi maganar namata kizo, kamar maganar badaga bakinshi tafitoba, sanin halinsa karta 'kara tambaya ya chanza ra'ayi yasa tayi shiru tana kallonsa a nutse,
Ya janyo kujera gefen madubinta yazauna suna facing juna,
Yayi gutun ajiyar zuciya, ya nunamata wayar hannunsa yace "wannan fa?"
"Wayar da Hajiya tasiyamin ne" tafada tana kallonshi, ya d'aga gira yace "oh really! Hajiya nasanki fa, Amma dai nafita sonki"
Dariya tasaki har ha'koranta nafita, yadda yayi maganar cikin xolaya tace "hakane nasani" ya 'daga gira yace "Wow toh bani Number,"
Tayi yar'fari da ido yadda taga Hadiza nayi ta turo bakinta very kissable tace "bansani ba" baiyi mamakiba, yayi dialling Number sa yace "haddace shi zakiyi"
Kiran yashigo wayarsa ya yanke yayi saving yace "ki kwanta ki huta, kin gaji anjima zamu fita,"
Kallo daya zakai mata kasan tana cikin farin ciki mara musultuwa wani irin dadi da annuri ke ziyartarta aranta tace kamar bashi yake fushi da daniba dazun, tana murmushi tace "Toh Yaya"
Kai kawai yagyada ya fita, Zinaru ta kwanta harda mi'ka,
Karfe biyar (5:00pm) Zainab tashigo ganin tana barci bata tashetaba tafita,

Kaine Rayuwata😭❤❤ CompleteOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz