🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤
🖤🖤
🖤*RAYUWAR BILKISU*
*🤝ANA TARE WRITER'S ASSOCIATION*
_Na Miss Ayusha_
_Bismillahir rahmanir rahim_
_Wattpad@ ayshartou_
_Page 3-4_
Zafi k'irjinta yake mata amma yaya ta iya dan dole haka ta hak'ura dauko itacen tayi gasu d'anye abinku da yanayi na damuna idonta taf cike yake da k'wallah ta shiga jerasu cikin murhun har ta kammala.
Wurin Inna ta nufa wacce ke zaune tana kallon duk abinda Bilkisu takeyi
"Inna babu kalazir d'in ya k'are"
"Sai kije ki hura hakan nan mana koko zan zama kalanzir neh kiyi amfani dashi"
Kai ta girgiza mata kai tare da nufan hanyar waje dan ta samo abinda zata had'a wutan dashi taci sa'a kuwa ta samo 'yan robobi nan ta had'a kansu ta dawo cikin gidan cikin Nana da Inna babu wanda yace da ita ci kanki ana haka Talatu ta shigo gida.
"Kaga aminiyar arziki takawarki lafiya kawata" Inna ke fad'in wannan magana wa Talatu.
Dariyar 'yan bariki tayi tare da buga shewa
"Kina sha'anin ki Jummala ki 'yar da uwa saura diyar uwar"
Sarai Bilkisu ta gane da ita take amma sai ta maida hankali kan abinda takeyi Nana dake faman lallatsa waya tashi tayi ba tare da tace da Talatu uffan ba tayi d'aki
"Ke baki iya gaisuwa bane?"
jiki na rawa Bilkisu ta kai k'asa tare da gaidata mai makon ta amsa gaisuwan sai ma dungure mata kai datayi inda sabo ta saba hakan neh yasata komawa b'akin aikin ta.
"Kawata ta kaina"
"Ya ake ciki toh? Inna ta tambaya
"K'udi nazo ki ranta min wani abu ya taso min kuma banida hanyar samun su"
Dariya Inna tayi tare da magana
"Talatu nasan halinki da rashin biyan bashi kar azo ana jin kanmu a titi"
"Bama za'ayi haka ba"
D'aki Inna tayi tare da dauko jakar k'udin ta fito nan ta tarar da kiran Bappah kusan uku
"Yoo ni Jummala na shiga uku ashe Bappah su Nana yayi ta kirana ina aikin banza"
"Bai baci ba kya iya kiran shi ai amma kafin nan nazo miki da wata shawara"
"Kawar arziki ta miye?
"Wannan yarinya Bilkisu meye zai hana bazaki zamar da ita kamar jari ba"
"Bangane meye kike nufi ba?
"Kawo kunnen ki"
Kamar wata doluwa Inna ta bata kunne tai mata rad'a aiko karaf suka saki shewa
"Kai aminyar shiyasa nake sonki har cikin raina"
Baiwar Allah tana gefe wuta tak'i kamawa sai hayak'i takeyi tana hurawa ga idonta da ya kad'a yayi jawur da kyar wutar ta kama tukunyar ta aza kan wuta tare da zuba ruwan tatan awaran ta koma gefe da zama.
"Yanzu dai nawa kike buk'ata?
"Dubu biyar neh babu yawa?
K'irgo k'udin tayi tare da mik'a mata tai mata sallama ta bar gidan Inna sai juya maganar Talatu takeyi a zuciyarta lallai zatayi arziki kenan.
Wayarta ta jawo tare da danna kiran Bappah tana fara ringing ya danna busy tare da kira
"Assalama Alaiki uwar yara"
"Amin alaika sallam Bappahn mu ya kasuwar da hidindimu?
"Alhamdulillah, yaya kuke ina su Nana da Bilkisu?
Sai da ta kalli gefen Bilksu data kafeta da ido tukun tai magana
"Ga Bilkisu nan Nana kuma na bacci"
"Allah sarki bata wayar mu gaisa"
Sai data ja kunnen ta sannan ta mik'a mata wayar.
"Bappahna"
"Na'am gimbiyata ya kike?
"Lafiya lau Bappah"
"Meyasa mi muryarki kamar wadda kikayi kuka?
"Babu komai Bappah mura nakeyi shiyasa"
"Ayya toh kinsha magani koh?
"Eh" tare da share k'wallar dake neman zubo mata da sauri Inna ta karbi wayar
"Bappahn yara satin shigowa yayi fa"
"Na sani Jummala kasuwa ta bud'e amma da zarar na kammala abinda nakeyi zakiji ni"
"Shikenan Allah ubangiji ya baku sa'a"
Amin ya amsa mata yana mai kaunar matar shi kodan soyayyar da take yima Bilkisu ai dole ya sota hmm niko ina gefe Bappah bai taba sanin abinda Inna takeyi ba.
Tana zaune gaban murhu dan bata san abinda zai sa wutar mutuwa gashi fitsari take ci haka ta hak'ura tare da nufan bayi don yin fitsari dan Inna ta koma d'aki amma kafin meh ruwan ya fara zuba har itacen ya fara mutuwa dai dai fitowar Inna
"Ina wannan shegiyar ta tafi abu yana zuba?
"Inna fitsari nayo"
Duka ta kai mata tare da buge bakin ta
"Ina magana kinayi koh"
"A'a Inna dan Allah kiyi hak'uri"
Dan Bilkisu tana bala'in tsoron duka duk da ta saba shan na Inna, wurgi da ita Inna tayi yayinda ta fad'i
Share jikin ta tayi tako mik'e abinta dan idan da sabo ta saba
Takun takalmin neh ya jawo hankalin su Nana ce anci uban ado kamar meh wurin taron kyau
"Kaga 'yan matan Inna sai ina kuma?
"Zan dan zaga gari neh sai na dawo"
_wannan wace irin uwace babu tsaro ba komai hmm muje zuwa_
Tana nan zaune gaban murhun har awara ya dahu duk abinda ya kamata tayi sai data yi shi yayyankawa tayi tsaf tare da zuba shi a bokiti
"Na nawa neh dukka?
"Dubu daya da d'ari uku?
"Saura naga k'udi ya bata kuma idan kin fita"
Murmushi kawai Bilksu tayi dan da d'ari biyar ne ci zatayi ta koshi itama idan ta fita suna haka Labiba ta shigo gidan.
Bilkisu na ganin ta tayi wurin ta suka k'araso tare
"Inna yini"
Rai a bace ta amsa kafin tayi d'aki
"Bilkisu yaya jikin dan kina bacci na tafi makaranta"
"Da sauki Labiba amma nasha bugu a wurin Inna"
Wurin da ya tashi ta nuna mata tsaban duka
"Bakomai Bilkisu Allah yana tare dake"
Juyawa baya Labiba tayi taga ba kowa sai ta jawo hannun ta
"Kinga wannan Yusufa neh yace na baki kinji ko"
Da sauri Bilkisu ta k'arba amma ai Inna ta riga data gani
"Sannu munafuka wato ke mai wayau ko tashi ki bar gidan nan kafin na miki shegen duka"
Kallon ta Labiba ta tsaya yi daba dan darajar Bilkisu ba matar nan da taga rashin mutunci ai kuwa karban ledan hannun Bilkisu Labiba tayi ta fita
"Ke kuma zakici ubanki"
Bulala ta t'sinko a bishiya dake cikin gidan ta shiga dukan ta ba sassauci tun Bilkisu na ihu har yazamo babu k'arfin da zatayi ihun sai da ta gaji dan kanta ta barta tana sharar k'wallah.
_yawan comments yawan typing_
_Miss Ayusha_

YOU ARE READING
RAYUWAR BILKISU
Short StoryA painful story.... Dan d'aki neh tana k'wance sai ji tayi an watsa mata ruwa,tashi dan ubanki... Ta taso babu mahaifiya, step mum ta saka rayuwarta cikin garari...ku biyoni jin yaya.