part 24

571 11 0
                                    

🖤🖤🖤🖤🖤🖤
  🖤🖤🖤🖤🖤
     🖤🖤🖤🖤
        🖤🖤🖤
           🖤🖤
              🖤

*RAYUWAR BILKISU*

*🤝ANA TARE WRITER'S ASSOCIATION*

_Wattpad@ ayshartou_

_Na Miss Ayush_

_Bismillahir rahmanir rahim_


'''Walida to you again🥰🖤'''

_Page 47-48_

Basuji tafiyan shi ba sai zaman shi sukaji zuciyar shi fal tunani daman Rahama tana san Tahir neh shine bata taba fad'a ma kowa ba ya Rabb

"Auta"

       D'ago ido tayi tuni ta rungume shi

"Brother Daddy meyasa zae min haka wallahi banason auran ni karatu na zan tafi kar ya aura min wani idan ba Tahir ba"

       "Auta we have nothing to do about this issue kawai kiyi hak'uri kita addu'a Allah yasa haka shine zai zama alkhairi a gareki kinji koh"

Kai ta gyada masa fuskarta duk ta kumbura dan kuka Hameed ya lallabata ta k'wanta bacci yayi gaba da ita.

Bilkisu ganin bacci ya kama Rahama tayi yunkurin tashi ya kamo hannun ta

    "Ina zakije?

"Wurin Umma zanje"

        "Naga Umma dai suna tare dasu Daddy"

  "Nasan sun tashi ni ka barni na tafi"

Yadda take maganan yasa shi sakin baki yana kallon ta wannan b'akin sae yayi maganin shi wallahi

  "Toh kafin ki tafi zauna muyi magana"

Kallon shi tayi da ido kaman zatayi kuka

  "Dan Allah Ya Hameed ka barni naje wurin Umma magana zamuyi"

"Shikenan kinci albarkacin Umma kije zamu had'u anjima"

Da gudu ta ruga tare da nufan yadda Umma take taci sa'a kuwa Umma kadai ke wurin.

   "Ummana"

"Na'am 'yar Umma"

"Hira nazo muyi"

      "Allah sarki yarinyan kirki Allah albarkaci rayuwan ki kinji koh ya kuma kare ki d'aga sharrin masu sharri"

  "Nagode Umma da addu'a"

"Yauwa 'yar Umma meh dame kike buk'ata Bappah ki ya sai miki?

  "Nidai Bappah inhar bashida halin min abu dayawa kawai yamin wadda ya sauwaka karya matsa ma kanshi Umma"

      "Shikenan 'ya ta idan mukaje yola zanma inno magana akan meh gyaran jiki dan tazo kinsan kaman yau abin zai zo"

Bilkisu rufe fuska tayi dan Umma ta bata kunya hakan yasata cewa Umma suyi wata hirar ba wannan ba

Allah sarki Bappah yana wurin aiki amma tunani yakeyi akan kayan auran Bilkisu Salim yake jira gashi yana b'ata mishi lokaci hakan yasa shi tashi dan tafiya gida saboda lokacin tashi yayi.

Alhamdulillahi Salim ya dawo yayinda ya tarar da Bappah a gida bayan sun gaisa Bappah yake tambayar sa yaya ya dad'e neh haka bai zo da wuri ba.

   "Bappah dan Allah kayi hak'uri a wannan karon ka yafe ma Nana ka gafarta mata Bappah ina tsoron yadda zata fuskanci mahillincin ta da fushin ka dan Allah Bappah ka yafe mata"

RAYUWAR BILKISUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora