Part 7

689 21 0
                                    

🖤🖤🖤🖤🖤🖤
  🖤🖤🖤🖤🖤
    🖤🖤🖤🖤
       🖤🖤🖤
          🖤🖤
             🖤

*RAYUWAR BILKISU*

*🤝ANA TARE WRITER'S ASSOCIATION*

_Wattpad@ ayshartou_

_Na Miss Ayusha_

_Bismillahir rahmanir rahim_

_Page 13-14_


_"Bilkisu mahaifiyar 'yar asalin garin kaduna ce iyayan ta Alhaji Aliyu sai mahaifiyarta Fatima, su uku Allah ya bama iyayan su Aliyu shine na farko,sai kuma Zakiya ta biyu sai Ummanki (Bilkisu wacce kikaci sunan ta) iyayan ta sunada hali dan a lokacin baban ta yana d'aya d'aga cikin masu arziki, Aliyu dayake babba shine yayi karatu a jami'ar ABU dake zaria mahaifiyarki batayi zurfi a karatu ba kamar yadda 'yan uwanta sukayi da kuma yadda iyayan ta sukaci buri sakamon had'uwana da ita_"

"Bappah meye ya faru bayan kun had'u d'in? Sake kallon Bilkisu yayi yana gyada kai

_"kamar yadda nakeyi akwai wata rana na tashi bayan na nufi kasuwa yadda shagona yake lokacin gaskiya banida k'arfi dan kayan miya ma nake sayarwa a time d'in k'watsam sai ga mahaifiyarki ta sauka a mota ashe yayanta shine ya kawota kasuwar wurina ta nufo da niyar siyan kayan miya tunda naga mahaifiyarki Allah ya daura min sonta a lokaci guda toh amma ina gudun mata magana saboda ganin motar da ta fito a ciki uwa uba sanin halin Innarku nada kishi yasa ban mata magana siyayya sosai tayi a wurina har na dubu biyu da d'ari biyar, gashi banida d'ari biyar da zan bata canjin ta ganin tana b'ata lokaci duk da an naima bamu samu ba yasata cewa na rik'e canjin kawai nai mata godiya itama tai min sannan ta shiga wannan motar suka tafi tunda mahaifiyarki ta bar wurina nake ta tunanin wannan baiwar Allah gashi bansan ina zan sake samunta ba a ranar haka na kwana da tunanin mahaifiyar ki_

"Ehen Bappah ka cigaba"

Wani wawan kallo da Inna ta zuba ma Bilkisu yasata yin shiru tare da sak'e mak'ale hannun Bappah.

_"Washe garin ranar da wuri na tashi amma idanuna suna mararin sake kallon ta bayan na gama shiri nayi komai na tafi kasuwa haka dai aka rik'a min ciniki a ranar har na tashi batazo kasuwa ba, kwanaki hud'u nayi babu labarin mahaifiyarki a k'wana na biyar kuwa ta sake zuwa wurina siyan kayan miya wani farin ciki neh ya ratsa zuciyata ganin yau ita kadai ne aikuwa bayan gama siyayyan zata tafi na tattaro duk wata k'arfin gwiwa nawa nayi mata magana mahaifiyarki matar kirkice wacce bata dau duniya da zafi ba bata lura da irin gidan data fito ba ta amsa min harma da numbern wayarta ta bani, da dare bayan na kammala komai na kira Innar ku bayan gama gaisawa muk'a dan taba hira sannan mukayi sallama, dannan numbern mahaifiyarki nayi tare da kiranta kamar jira kuwa takeyi ta dauka wayan bayan mun gaisa na gabatar mata da kaina tare da yanda na fito dan ainihina dan garin Adamawa neh addu'a tayi akan Allah ya shige mana gaba inhar tarraya na da ita alkhairi neh sosai naji d'adin hakan kuwa mukayi sallama, tun d'aga wannan ranar muka kulla soyayya tsakanin mu da marigayiya da shakuwa yadda na lura da ita abin duniya bai taba tsole mata ido ba kuma na sanar mata akan tai ma iyayan ta magana_"

_"Ranar da mahaifiyarki tai ma iyayanta magana a ranar aka sanya ni zuwa gidan su abinda nafara gani 'yan gidan basu san marashi sun fi son mai abu a hannu bayan sun gama ganina suka buk'aci dana tafi jiki a sanyaye na tafi, bayan k'wana biyu mahaifiyarki ta kirani shaidamin tayi da iyayanta inhar na aureka toh fa duk halin da ta shiga babu ruwan su saboda son da takemin yasa ta amsawa da ta yarda ga 'yar uwarta tana ta karunta ta_

_"Ana haka na dawo gida sanda na sanar da Innar ku ta d'aga hankalinta kwarai da gaske da kyar na samu ta sauko d'aga fushin da take na sanar ma iyayena komai akan lamarina da Bilkisu watou mahaifiyar ki addu'a suka sanya min komai daya kamata ayi anje anyi d'agewa nayi na mata ak'wati masu kyau da kayan ciki saboda kar a samu matsala auran mu wata d'aya aka saka tun wannan lokacin take ganin tsangwama a gidan saboda ta zabe ni akan kowa ,rana kuwa bata karya tun lokacin da bikin ya karato na gyara gidana tsaf har Allah ya kaimu lokacin akayi bikin tun ranar da 'yan uwanta suka kawota babu wacce ta sake takowa gidan_

_"Watan mu uku da aure na shiga wani hali wanda ko abincin da zamuci yayi wahala anan kuma aka fara yada zance ai auranki shiyasa sa na dawo haka bansani ba har mahaifiyarki taje gidan su akan su taimake mu amma babu wadda ya saurareta sai ma korarta da sukayi tana kuka take fad'amin duk yadda sukayi da iyayan ta hak'uri naita bata haka muka cigaba da hak'urin tun d'aga ranar bata sake zuwa gidan su ba cikin ikon Allah aka fara daukar ma'aikata a lokacin kuma na samu aikin da nakeyi yanzu na teaching da kuma kasuwancin dana cigaba dayi_"

_"Rayuwar mu ta gyaru nayi niyan kama haya a kaduna amma sam Innar ku tace bazasu koma ba shiyasa na koma ni kadai sai dai na rik'a zuwa auranmu wata 8 mahaifiyarki ta sake zuwa gidan su amma tarbar da sukai mata ya karyar da zuciyarta har Mammansu take gaya mata ai da ta hak'ura da zuwa gidan tunda lafiya muke zaune tun wannan ranar kuwa bata sake zuwa gidan su ba bayan wata 9 nagane mahaifiyarki nada juna sosai take kulada kanta ta fanni na ina aikina da sana'ata har cikinta ya isa haihuwa bana gari kuma bata sanar dani ba Innarku da Talatu su suka kaita asibiti bayan ta haifeki neh Allah ya amshi abunta Innarku ma tayi kuka duk wadda suka santa da halinta babu wadda bai koka ba kafin nazo har an suturta gawarta addu'a sosai nayi mata muka kaita gidanta na gaskiya haka Innarku ta cigaba da rainanki har ranar sunanki ya zagayo saboda kaunar da nakema mahaifiyarki na mayar miki da sunan ta tun d'aga wannan lokacin rainonki ya koma wurin Innar ku har kawo girmanki yanzu_"

Fuskarta taff da hawaye take magana

"Allah sarki Umma Bappah to ka sanar da 'yan uwan ta neh?

"A'a Bilkisu naje har gidan su amma babu wanda na samu sun bar gidan"

"Allah sarki Bappah zan samu hoton ta a wurin ka?

"Bilkisu hoton ta yana kaduna amma da izinin Allah zan taho miki dashi"

"Shikenan Bappah nagode"

Murmushi ya mata yayinda Inna take tunanin lallai Bilkisu sai tayi wanka da ruwan kaikayi

********
YOLA(Wurocheke)

Suna zaune suna hira

"Inna a gaskiya na damun da son ganin 'yar uwata bansan a wani hali take cikiba matsalar d'ayama da bansan wacce duniyar take ciki ba"

"Toh ko dai zakije dubata neh?

"Da sauran lokaci dan bansan wani duniya take ciki ba tun bayan rabuwar mu"

"Kar ki damu Insha Allah ma tana lafiya"

"Allah yasa Inna"

**********
LERE

BAYAN K'WANA BIYU

Bilkisu an huta da jarabar Inna kuma a yau neh Bappah yayi shirin tafiya Bilkisu sai kuka takeyi yayinda Inna suketa lallashin k'arya wanka zata shiga amma ta fasa sai da suka raka Bappah sanda ta dawo Inna ko kallonta batayi ba dan ita kadai tasan meh ta zuba mata a cikin ruwa idonta daya cika da hawaye tayi shigewarta bayi tayi tare da fara wanka tuni jikinata ya fara sosa takeyi amma kamar k'arawa akeyi zubar da sauran ruwan tayi tana kuka da ihu.

"Zakimin shiru koh sena ci ubanki iyye sakamon abinda kika aikata kenan yadda na tsani uwarki haka na tsaneki dan babu wacce ta isa had'a miji dani ya k'wana lafiya"

"Iya k'arfinta take kuka Inna ta fara had'a mata da duka" abin tausayi am ma Inna babu imani take bugunta shigowan Salim yasata tsagaita dukan da take mata.

"Inna wallahi ki guji ranar da ubangiji zai kamaki ranar da babu bakin magana" fuu yaja hannun Bilkisu suka tafi Inna sai huci takeyi ranar baccin azaba Bilkisu tayi😭😭


_Poor Bilkisu sakkaya tana gaba akwai Allah_

_Comments nakeso ba Heart ba ko thank you ko stickers duk na yafe su_


_Miss Ayusha_

RAYUWAR BILKISUWhere stories live. Discover now