🖤🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤🖤
🖤🖤🖤
🖤🖤
🖤*RAYUWAR BILKISU*
*🤝ANA TARE WRITER'S ASSOCIATION*
_Wattpad@ ayshartou_
_Bismillahir rahmanir rahim_
_Na Miss Ayush_
_Page 31-32_
......Sunbi kasuwa yadda Hameed ya sai mata kaya masu kyau na gaske sannan suka kama hanyar Kaduna Bilkisu anji Ac sai bacci Hameed yana juyowa tareda kallon ta Tahir na ank'are dashi tun yana basarwa har ya gagara yayi magana.
"Brother ka zurma da yawa fa"
"Banason iskanci kanaji koh"
"Ai naga duk juyi sai ka kalleta neh"
"Hm ka bari kawai yanzu muna isa gida ma zanma Mummy magana Daddy na dawowa ayi magana dan bansan a b'ata lokaci kafin mu dawo takan Inna da sauran su"
"Gaskiya neh Hameed abinda ya kamata kenan kodan masu irin wannan halin su daina"
"Kai dai ka bari kawai"
"Brother anjon Bilkisu"
Murmushi Hameed yayi yana shafa gashin fuskar shi.
_ ******** _
"Friyal ki shirya gobe Auntyn ku zataje gida sai ki bita koh idan kika gama hutu sai ki dawo"
"Yauwa Inna wuro daman kaman kinsan nagaji da zaman yolan nan"
Wacce suke kira da Aunty tana murmushi tayi magana
"Inna wuro ai ba dadewa zanyi ba komai yana daidaituwa zamu dawo"
"Yarinya kaman gaske kike fad'a"
"Dagaske nake Inna wuro kuma zaki gani"
"Shikenan Allah ubangiji ya kaiku lafiya ya tsare"
Friyal na murna ta riga answer wa da Ameen
Aunty da Friyal shiri fa ya kankama Friyal Allah Allah take gobe tayi dan su tafi.
_ ******** _7:00pm Sun iso garin kaduna Bilkisu an wartsake d'aga baccin da takeyi ganin tun d'aga gate take ganin sojoji da bindigogi a hannun shi tuni tsoro ta kankame jikin ta Hameed dake ank'are da ita sai murmushi yakeyi itako ta mak'ale wuri d'aya.
Sun iso cikin gidan tsayawa fad'uwar gidan bata lokaci neh gidan his Excellency guda hmm abin babu magana sunyi tafiya mai nisa har ta sada su da wurin ajiyan motoci suka fito itafa bazata iya wannan rayuwar ba gam ta rik'e hannun Hameed tare da kallon fuskarshi murmushi suka sakarma junan su sannan suka hau tafiya.
Mummy, Mubinah da 'yarta Nihal sae Rahama da masu aikin Mummy duk suna zaune sukaji sallamar su Hameed da gudu Rahama tayi wurin shi tareda rungumar Hameed.
"Oyoyo brother"
Mayar mata da rungumar yayi ta juya tareda murgud'a ma Tahir baki da gudu ya bita zae kamata a guje tayi bayan Mummy dake kallon su tana sanye glass a idonta
"Ku dai bazaku taba girma ba koh?
"Kaji big sis fa da wani magana nawa ma muke?
"Eh lallai yaran nan bakuda kai kam"
"Yanzu duk kuyi shiru Mummy surprise"
Kallon shi tayi tana murmushi
"Yes Hameed"
Bud'e labulan da suka rufe ta yayi tareda jawo hannunta suka fito yayinda duk suka zuba mata ido banda Rahama gidan rawan kai data taho wurin Bilkisu ta kama hannun ta.
"Hameed" Mummy da Munibah suka fad'a wurin had'a baki
"Mummy my dream girl"
Jin abinda Hameed ya fad'a Rahama ta rungumeta.
"Watou kece meh wahalar da yayana koh?
Ware ido Bilkisu tayi yadda Rahama taja kumatun ta dagani zakiyi tsoro murmushi Bilkisu tayi mata yayinda Mummy ma ta taso tare da rungumeta sae a sannan Bilkisu da duk ta tsorata ta gaida Mummy cikin sakin fuska ta amsa mata ta juya ga Mubinah itama ta gaisheta yadda ta lura da gidan gaskiya sunyi nisa wurin karrama mutane.
Jan Hannun ta Mummy sukayi tare da zama.
"Hameed bakuyi sallah ba nasan ga yunwa ga kuma gajiya dan haka duk kuje ku kimtsa sannan ku fito ku sanar damu yaya kuka had'u"
"Shikenan Mummy" Hameed da Tahir suka answer
"Auta ki kaita dakin ki tayi wanka da sallah sannan itama ta fito"
Hannun ta Rahama ta kama suka shige d'akin komai ta had'a ma Bilkisu matsalar d'aya neh kayanta sun ma Bilkisu yawa hakan yasa bayan ta shiga wankan ta nufi d'akin Hameed.
"Mummy yarinyar nan dagani zatayi hankali kuma batada hayaniya"
"Hakane Mubinah farin cikin da Hameed ya ganta"
Nihal data damu mamanta akan zata sauka tako saketa take tayi d'akin Rahama da tafiyan ta wanda bai nuna ba tana gwalatu.
Tana nan zaune har Hameed ya fito a wanka yana kallonta
"Ya dai?
"Kayan sisterna"
K'warai yaji dadin yadda Rahama ta nuna ma Bilkisu so dan yasan hakin kanwar tashi sarai.
"Ohh kinga na manta dashi a mota ga key aje a dauko mata"
K'arba tayi tareda nufan motan ta k'waso mata kaya lokacin da taje d'akin har Bilkisu ta fito wanka tana daure da towel d'in da Rahama ta bata
"Sister na ga kayan na karbo nida kaina zan zaban miki wadda zakisa"
"Shikenan toh"
Wata dogowan riga mai dan banzan kyau ta zaban mata nan ko ta saka tare da fara sallah Rahama na zaman jirantan.
_Dan Allah kuyi hak'uri zazzabi ya kamani kuyi manage da wannan zuwa gobe_
_Miss Ayush_

VOCÊ ESTÁ LENDO
RAYUWAR BILKISU
ContoA painful story.... Dan d'aki neh tana k'wance sai ji tayi an watsa mata ruwa,tashi dan ubanki... Ta taso babu mahaifiya, step mum ta saka rayuwarta cikin garari...ku biyoni jin yaya.