Page 25

2.9K 191 6
                                    

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
 
           *_MENENE MATSAYINA ?_*
                 *(fiҫтiоηӑι sτοrγ)*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~

    *Written by*
Phatymasardauna
         *🎈Mrs Sardauna🎈*

*Dedicated to my lovely Sister Maryam*

       *Wattpad @fatymasardauna*

*🌹Wannan page ɗin nakine dukansa, My Lovely nd Sweet, MANAB ƴar baba, marubuciyar MONAH nd IYA RUWA (fiddakai) nagode sosai MANAB Allah yabar ƙauna atsakaninmu, duk sanyi duk zafi, munajone insha Allah, Inayimiki son so acikin zuciyata, kiji daɗinki kiyi farinciki mai ɗorewa tawajena , ilove you masga nd sambaɗa sambaɗa Mrs Sardauna ta kice ....🌹*

  *Editing is not allowed 📵*

   *page 3⃣1⃣*

Ahankali yakamo  hanunta haɗi da soma murzasu cikin nutsuwa, magana yafarayi kamar haka..

"Kinada babban matsayi awajena Farhana,, bansan damai zan kwatantamiki irin girman matsayin dakike dashi awaje na ba,    haƙiƙa ban nunamiki tsana saboda wani abu daban ba, sai don ni mutum ne mai matuƙar kishi, akan abun dana keso, nasoki fiye da yanda naso kaina,  na ƙaunaceki tunbakisan wacece keba,  nayi dakon soyayyarki na tsawon shekaru, kikalli idanuna babu tsanarki ko kaɗan acikinsu, kuma koda sau ɗaya ne bantaɓa jin tsanarki acikin zuciyata ba, amma kece silan rugujewar duk wani farinciki na,    maiyasa Farhana ? maiyasa alokacin da nake tsananin sonki, kika fito da wasu irin ɗa bi'u, irin wacce tasaɓamawa addini ?  maiyasa kika zama mai saurin yadda haɗi da bada kai ga maza ? maiyasa kike mu'amala da maza tamkar yadda kike mu'amalantar ƙawayenki ? maiyasa kikayi watsi da tarbiyan da  Ummie tabaki tahanyar mallaka mawa wani namiji jikinki ? kin kosan girman zunubin dakika aikata,  da kika bar namijin da ba muharraminki ba, yake taɓa jikinki don jin daɗi, ke aganinki hakan soyayyace ko wayewa ?? kinyi kuskure domin kuwa, babu wata wayewa mai kyau daya wuce killace kanki, wa mijin aurenki,     duk da nasha kamaki da Farhan kuna kissing juna, amma ban taɓa yi miki kallon mazinaciya ba, sbd nasan bazaki taɓa aikata zina ba, domin kuwa sam hakan ba ya daga cikin ɗabi'ar ahalinmu,,    kinma kuwa san yanakeji aduk sanda na ganki kuna aikata wani mummunan abu da Farhan ?   jinakeyi tamkar zuciyata tafito waje, nakan jin zafi da raɗaɗi marar iyaka aduk sanda na iske ku keda Farhan kuna aikata saɓon Allah, kuma inaso kisan cewa tsananin kishin ki shiya haddasa nuna rashin kulawata agareki.."  yakai ƙarshen zancen nasa yana mai kafeta da manyan idanun sa dasuka kaɗa sukai ja...

Hanu Farhana tasanya haɗi da share hawayen dasuke kwaranya daga cikin idanunta. Wanda tun sanda Hameed ya fara magan ganunsa hawayen ke zuba da ga idanunta...

kasa ce dashi komai tayi saima tashi da tayi daga  kan gadon kaitsaye tafice acikin ɗakin..

Handle ɗin ƙofar dake kusa da ɗakin da  tafito, ta murɗa haɗi da kutsa kanta ciki,     komai dake cikin wancan ɗakin shine anan ma saidai banbancin colour domin wannan light pink ne saɓanin wancan dayake milk colour,,    zama tayi kan gadon haɗi da sakin kuka mai sauti,,     haƙiƙa duk abun da Hameed yafaɗa gaskia ne, domin kuwa takan sakewa da namiji tamkar yadda zata sake da ƴar uwarta mace,,      tsananin soyayya ne yarufe musu ido ita da Farhan, har yasanya suke aikata saɓon Allah, amma suke ganin hakan tamkar wayewa ne,      amma zatai ta roƙamusu Allah daya yafemusu zunubansu... Saida Farhana tayi kuka sosai kafun tashige cikin bathroom tawanko fuskarta,, takuma yi nadama sosai akan abubuwan dasuka aikata ita da Farhan....

(( Gareku ƴan mata masu soyayyar zamani, wallahi ku farga kukoma ga Allah, domin kuwa hakan dakukeyi ba abu bane mai kyau, duk wata salon soyayya  da kuke son nuna mawa juna ku bari idan kunyi aure kwayishi..))

MENENE MATSAYINA ? حيث تعيش القصص. اكتشف الآن