1

7.5K 293 17
                                    

*NAJEEB*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*


                 *PAGE1*






*ASSALAMU'ALAIKUM*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN 'KAI, TSARKI YA TABBATA GA ALLAH UBAN GIJIN TALIKAI WANDA YA SAKE BANI DAMAN SAKE RUBUTA WANNAN LABARIN, YANDA NA FARA LAFIYA ALLAH YASA IN GAMA LAFIYA🙏*

*WARNING*
~BAN SON KORAFI, WANDA YAGA BAZAI IYABA YA BARI, SHI RAYUWA BABU DOLE,  BAZAN D'AUKI ZAGIN DA AKAMUN AKAN NOVEL DIN *BARIKI NA FITO* BA NOVEL D'INA KYAUTA NE, AMMA WLH IDAN AKA ZAGENI ZAI KOMA NA KUD'I, NASAN REAL FAN'S D'INA WILL COME AND PAY, FAKE ONE KUMA NASAN BAZASU ZOBA, SO PLZ A KIYAYE, IN KAGA BAI MAKA BA, JUST LEAVE IT, SANNAN WANNAN LABARIN ZAIZO DA WANI SALO, KAWAI KU BIYONI NA RIGA NA TSARA LABARIN~


             *LONDON*
Airport wani jirgi ne mai cin mutane 500, ya sauka airport inda mutane suka fara fitowa, yayin da masu taransu suke tsaye suna jiransu, haka har suka gama fita daka cikin jirgin.

Wani Guy ne fari Mai cikar zati ga kyau ga kwarjini ya fito daka cikin jirgin sanye da farin kaya, wanda zai baka tabbacin cewa shi pilot ne.

Mi'ka yayi tare da kallon gefenshi inda ya fara tafiya lokaci d'aya, wani d'aki ya nufa inda Nan ne aka tanadar ma matuka jirgin in sunzo zasu dinga hutawa, d'akuna ne a jere sunkai guda Goma, shiga yayi yana shiga yayi toilet.

Jim kad'an sai gashi ya fito alaman yayi wanka yana goge kanshi da towel, wayanshi ne ya fara ruri d'auka yayi yaga Monica, d'an tsaki yaja tare da danna wayar yace nazo, just coming, yana fad'in haka ya kashe wayan ba tare da yaji Mai zata fad'a mishi ba.

Ko 30mnt da Gama wayan baiyi ba aka fara mishi nocking, daka shi sai boxer a jikinshi, babu ko riga, haka ya tashi ya bud'e kofar, ganin Monica ce yasa ya kura mata ido ganin irin shigar da tayi wanda gaba d'aya half naked, d'an tsaki yayi domin duk da Monica Tana biya mishi bukata baya son tana irin wannan dressing din, dan yana da kishi, uwa uba bazai so ramin daya shiga ba wani ya shiga, shi kaf y'an matanshi sun San halinshi, shi zai iyayin komai a gabanki amma ke baki isa kiyi ba, domin yasha fad'a shi mata bai d'aukesu bakin komai ba, face Abun hutawa, sannan tunda yana da kud'i zai iya harka dako wace mace, ba tare da damuwa ba, sai yasa har yau ya kasa aure tunda yana samun abunda namijin auren ke samu a cewar shi....

Hugging d'inshi Monica tayi wanda yasa dole ya dawo daka duniyar tunanin daya afka.

D'an tureta yayi tare da fad'in just go away.

Tsayawa tayi sororo Tana kallonshi, cikin harshen turanci Wanda bata iya fad'in sunanshi Sosai ba, tace najub what happen?

Kallonta yayi shima cikin harshen turancin yake mata magana, yace nace ki tafi

Sanin halinshi sarai yasa ta juya, domin tasan ko tafi kud'a naci tunda yace mata ta tafi dagaske yakeyi, komai zatayi bazai saurareta ba, tayi nisa Sosai ta tsaya tana tunani, lokaci d'aya ta kalli dressing d'inta, kaita dafe alaman ta kwafsa.

Shiko rufe kofarshi yayi domin bacci yakeji Sosai, dama yaso tayi massaging d'inshi ne, but ta bata mishi rai, dole ya kwanta bai dad'e ba bacci yayi gaba dashi.

Waye wannan guy din?

Ku biyoni nan gaba kad'an za kuji ko Waye.




           *NIGERIA*
Tafiya take tana sauri daka ganin alama tana cikin farin ciki Sosai, domin kallo d'aya zaka mata ka gane irin farin cikin da take ciki, wani Gida ta shiga, cikin sauri, a tsakar Gida ta iske umminta da kakarta wacce take kira da granny, tace ummi ummi ko sallama batayi ba, tace ummi kalla naci jamb d'ina, na samu 198 wayyo dad'i naci jamb.

NAJEEBWhere stories live. Discover now