9

2.3K 177 19
                                    

*NAJEEB*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*


                 *PAGE 9*





Mum kam ita duk wannan abunda sukeyi, ita bata ganin zata yarda, " Ayi ma d'anta haka, "dan ita gaskiya bazata yarda a d'aura ma d'anta wa Innan matan ba, haba ai wannan ba adalci bane ko kad'an, "taya yaron daya taso a waje, yayi karatu a can, ace za'a aura Mai wa Innan matan, gaskiya da sake, inshi Dad yayi shuru gaskiya ita bazata yarda a cuci d'anta ba, 'In ma auren akeso yayi sai a Bari ya zaba da kanshi bawai a Kawo mishi wa Innan y'an kauyen ba, ai sai a matsa Mai ya kawo mata a aura Mai indai haka akeji.

Dad tashi yayi "yana fad'in saida safe Bari inje in huta.

Granny tace "Allah ya tashemu lafiya.

Ya amsa da Ameen sannan ya wuce "itama Mum ta tashi tabi bayanshi

Ibtisam da zarah da Granny suka rage "Granny ta kalli ibtisam "tace wai yaushe shima kabirun zai turo ne? "naji shuru ya kamata dai ya turo "musan halinda muke ciki.

Ibtisam tace "haba Granny aikya Bari in warke koh, "kuma Kinga ga yaya Najeeb baiyi aure ba, ya kamata injira in yayi nima sai inyi hakan zaifi.

Granny ta tsuke baki, "can tace ke nifa so nake a had'a bikin duka, dan ban son Ayi ta hidima kan hidima aita abu a rarrabe, gwara a had'a, zaifi, " saiki fad'a ma Kabiru ya turo, inbai shirya ba mu sani. "kallon zarah tayi tace kema ya kamata in kina da manemi anayin nasu Kema kice ya turo, nida so samu ne duka basai a had'a ba.

Ibtisam tace ni saida safe tare da tashi tabar wajan.

Granny tace " oh ni Amina yara basa son zancen aure, daka an fara saisu tashi, kaman masu iska, "Zarah Anya bakya tunanin suna da aljanu kuwa? Granny ta jefo ma Zarah wannan tambayan.

Zarah dariya tayi tare da biye ma Granny "tace ashe bani d'aya nake tunanin haka ba, "Granny tace haba ashe Kema kina tunani kai na shiga uku, "Kinga miskili shi tunda yaji zancen aure yabar gidan har yanzu bai dawo ba.

Zarah tace "Granny nifa ina tunanin wannan matan ne baya so, " inda zaki canza mishi wasu da hakan yafi, ko kice ya kawo wanda yake so.

Granny tace "sam wannan ba abu mai yihuwa bane, "koso kike a maidani karamar mutum? 

Zarah tace "kaman ya Granny?

Granny tace "inje in kwaso Mata har hud'u, sannan ace bai d'auki ko guda d'aya ba, "inna koma Mai zance ma iyayen yaran? "Kinga tashi kije ki kwanta, "Granny tashi tayi tana fad'in saida safe, "miskili d'an banza ya'ki dawowa.

Najeeb bai farka ba sai wajan d'ayan dare, "tashi yayi yaji gaba d'aya jikinshi yayi mishi nauyi Sosai, "Kai tsaye ya nufi toilet yayi wanka tare dayin alwala yazo yana rama bashin sallah, Allah dai ya kyauta, "bayan ya idar ya tashi ya d'auki key din motarshi yabar hotel din, " Kai tsaye gida ya nufa inda yayi horn Mai security suka bud'e Mai kofar ya shiga part d'inshi ya nufa direct, "Bayan ya shiga gaba d'aya kayan jikinshi ya cire yasa jallabiya tare da kwanciya bai dad'e ba bacci yayi gaba dashi

Washe gari da safe tunda Granny tayi sallah asuba, ta fito falo ta zauna "wai miskili bai kwana a gida ba Tana jiran ya dawo taji gidan uban wa ya kwana, sai gyangyad'i takeyi, "amma ta'ki tashi tana nan zaune Wai tana jiran miskili, " a haka bacci ya bingirar da ita a nan Hhhhh, "shi dama bacci barawo ne gashi ya sace granny.

NAJEEBWhere stories live. Discover now