6

2.6K 135 11
                                    

*NAJEEB*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*MY BESTY OF LYF HABIBA BUZY🥰🥰 LOVE U WUJIGA WUJIGA💘💘*


                 *PAGE 6*


*wai Mai yasa wasu mutane basa tsoran Allah ne? Sai dai a baki kawai, nifa Maryam bacewa Nayi bana son kud'i ba, Yooo ni wacece da Zan'ki son kud'i ai kud'i Abun sone, but in mutum zai naima kud'i saiya nema ta guminsa, akan wani dalili zan zauna in bata lokaci na inyi typing in rubuta Basira na, bata wani ko wata ba, in siya data da kud'ina ba tare da nace wani ko wata ya siya min ba, sai na gama rubuta y'ar basiran da Allah yayi min sai wani ya d'auka ya dinga neman kud'i dashi, toh Wlh Wlh daka yanzu bazan k'ara d'auka ba, abun ya zama raini dacin fuska, da farko an d'auki novel d'ina har guda uku ansa a okada ba tare da neman izini naba, ansa BA'KIN ALJANI in zaka karanta saika biya 500, ansa FATIMA ZARAH, shi kuma in zaka karanta saika biya 200, ansa DUKIYAR MARAYA,  wanda barawon ya canza mishi suna izuwa dukiyar marayu, in Zaka karanta saika biya 300, akan wani dalili, ni Ina rubuta littafi a kyauta sannan wani yaje ya kaimun okada yana amsan kud'i da Littafina Wanda Nina rubuta bashi ba, nima fah ina son kud'in bawai banso ba, amma nayi a kyauta, akan wani dalili Kai ko ke zaku dinga siyar da novel din mutane without our permission, sannan Bayan haka wasu suna bud'e group akan in zasu tura maka novel complete saika biya kud'i, kuma Abun haushin basu suka rubuta novel d'inba, novel dinmu da muka rubuta suke saidawa, wasu ma saisu cire sunanmu akan novel din su saka nasu, Toh Wlh duk wani wanda ya k'aramin haka Wlh bazan d'auka ba, ba cika baki ba ko fariya Wlh akan hakkina Zan iya Shari'a da mutum, Abu d'aya shine in samu number d'in mutum, shikenan an wuce wajan,na fad'a zan k'ara fad'a maryam novel d'ina kyauta ne kar ku yarda ku biya kud'i domin a tura muku novel d'ina, ga sunan littafai na Zan fad'a, *FATIMA ZARAH*
*DUKIYAR MARAYA*
*BA'KIN ALJANI*
*BANDA ZABI*
*AMINIYA TACE*
*KISSA KO MAKIRCI*
*SUHAILAT*
*TAMBARIN TALAKA*
*JAWAHEER*
*SAINA AURESHI*
*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*BARIKI NA FITO*
*SAI YANZU WANDA NAKE RUBUTAWA NAJEEB*
*Gaba d'aya kyauta ne karku yarda wani yace saikun biya kud'i ya tura muku, kuma inna k'ara Kama wani yana saida min da novel saina d'auki mataki*








Zarah tace Kai granny mata har uku? Sai kuma ta fashe da dariya tare da fad'in sunyi mishi yawa ai.

Granny tace rabu da dan banza, koya zabi d'aya koya auresu duka, dan wannan karan bazan mishi wasa ba, inda a kauye ne da yanzu an fara maganan zai aurar da y'a, amma wai sai yanzu zaiyi aure, wannan lalacewan har ina, wlh ni rayuwar Bariki batai min ba.

Ibtisam tace uhm toh saiki koma kauyen ai ki zauna, Muma sai mu huta

Granny taja tsaki tare da fad'in basai ki Mai dani ba, mutuniyar banza, fita tayi dan taji muryan d'an Nata yana waya, alaman ya fito

Alh Abdullahi yana ganin Granny ya kashe wayar yana gaidata cikin girmamawa tare dayi mata ya hanya.

Tace Alhmdlh Ai Kai zance ma ya hanya kaida ka dawo daka k'asa Mai tsarki.

Zama yayi suka fara fira da Uwar tashi, suna cikin firan mum tazo itama anayi da ita,  Alh Abdullahi yace Ina mamana ibtisam?

Mum tace suna ciki ita da zarah, bari in kirasu, tashi tayi ta nufi d'akin sai gasu tare sun dawo, ibtisam gaida uncle din Nata tayi cikin girmamawa, ya amsa tare da sakin fuska yace kin Kawo takardun naki koh, y'an makaranta.

NAJEEBWhere stories live. Discover now