10

2.5K 138 17
                                    

*NAJEEB*

     *BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*

*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*

*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*

*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*

                 *PAGE 10*



Granny ta kalli zarah tace "Mai yace fad'amin.

Zarah shuru tayi "Tana tunanin Mai zata cema Granny, "domin bazata iya fad'a mata abunda Najeeb d'in yace ba, dan tasan rashin kunya ne, bai kamata ta fad'a mata ba.

Granny tace "ina magana kinyi shuru, "gayamin abunda dan banzan yace, "Nasan zagi na yayi koh?

Da sauri Zarah tace a'a Granny, "cewa yayi shi bata mishi ba, baya Sonta.

Shuru Granny tayi na wani lokaci, "sannan ta sauke ajiyan zuciya tare da kallon hanne tace maza ki koma ciki, "Hanne ta amsa da toh tare da juyawa tayi ciki, "Granny wani irin murmushi tayi tare da fad'in zanyi maganin d'an banza Wlh, zai gane shayi ruwa ne.

Najeeb kam gaba d'aya ranshi a bace yake "bukka ya nufa ya zauna yana jin ranshi na mishi zafi tare da fad'in "wai ita wannan tsohuwar Ina ruwanta da rayuwa na? And naga Dad kaman yana biye mata, "kafad'a ya d'aga tare da fad'in mum dinshi ce, but ni ba uwata bace, Dad zai iyayin abunda tace but banda ni, "wata iska ya furzar mai zafi tare da fad'in ta rasa wanda zata bani sai wa innan kazaman matan munana, y'an kauye, harda wani yaro mummuna duk jikinshi a bushe, tsaki yaja tare da fad'in kamata yayi in d'auki wannan tsohuwar in kaita asibitin mahaukata, ina tunanin ta Fara tabuwa, Inba haka ba " how can she think of getting me married with that old lady's," and she  asking me to choose one among them" nace bana so tana cewa in auri Mai yaro, "murmushi ya saki alaman takaici da mamaki, ko an gaya Mata ni aure yana gabana? " yaushe zan iya ajiye mata a matsayin matata kullum ta dinga takura min, "women are only for fun..... D'an shuru yayi yana nazari, lokaci d'aya ya tabe baki shi ba namiji bane mai son yara ba, har ake k'okarin aura mishi Mai yaro, shi koda an matsa Mai dole yayi aure ai budurwa zai aura, yaushe zai aura wacce ta taba yin aure, "Dan yasan for sure saita dinga tuna mijinta na baya, "and he can't take it dan yana da kishi, ajiyan zuciya ya sauke tare da fad'in " ya kamata ma kawai in koma inbar k'asar tun Kafin wannan mental tsohuwar ta sani gaba ta cinye d'anye, mata kaman mayya sai nacin tsiya..... Muryan Zarah yaji tana fad'in bros

D'agowa yayi, ya watsa mata sex eye d'inshi, tare da fad'in what?

Tace Bros ina son magana dakai "Plz kaban dama ka saurara kaji, " Zan taimaka maka wajan wannan matsalan na granny

Tsaki yayi tare da fad'in, "don't worry Sis ban d'auki wannan a matsayin damuwa ba, aure ne bazan yiba, sai dai ta mutu, "and inma tayi mistake tasa aka aura min ita saina kashe yarinyar nima a kashe ni, Waye yayi Asara?

Uhm Zarah tace "tare da fad'in amma bros inda zaka ji shawarata da komai yazo maka da sauk'i, ba tare da d'aga hankali ba.

Yace Zarah just leave me for a while, "ban son damuwa.

Tashi tayi tace "OK but in kana bukatan taimako am ready for help, Tana fad'in haka tayi gaba abunta

najeeb yana nan zaune lokaci d'aya ya d'auki wayarshi ya fara dannawa " wani irin murmushi ya saki lokaci d'aya tare da fad'in yes, tashi yayi ya shiga cikin gidan "inda yaga Granny a falo .

Ganin Najeeb ya shigo yasa tace ja'iri, ka Fara kallon kanka a matsayin ango Wlh

Baiko kalleta ba ya wuce part d'inshi, toilet ya fad'a yayi wanka tare dasa kaya, ya shirya cikin k'ananan kaya, "koda ya fito ya tarar da harda Dad d'inshi a falon da Mum da Granny sai su Zarah.

NAJEEBWhere stories live. Discover now