ILLAR RIK'O

215 12 0
                                    

*🤦🏼‍♀🙆🏼‍♀ILLAR RIKO*
_*('Yar riko)*_

*Na*

_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_

*♻REAL EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
_(Home of peace, honour & super writers)_

_*Dedicated to all my fans*_

_*Ina bukatan addu'arku Allah yabama Ummanta lafiya. Mummyna Allah ya baki lafiya yaja da nisan kwana.*_


_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_*Page 3*_

" Lfy klau " Luba ta fada cikeda ladabi.

" Masha Allah. Baba yarinyar nada hnkali wlh ga natsuwa."

Washe baki Baba tayi tace " ai shiyasa na roki alfarma gun aminiyata ta bani ita na kawo maka *RIKO* tunda ba wasu 'ya'ya gareka ba."

" *RIKO* " Ahmadu da kuluwa suka fad'a a tare cikeda mamaki, sannan yace " gsky Baba tunda dai iyayenta duk suna raye a bar ta mana su yi rikonta ni gsky......"

" Dallah rufe mani baki"baba ta katse masa hanzarinsa " sallamamme kawai, ba dole kace haka ba tunda kuluwan ta nuna bata so, kawai ka fito fili kace min baba bazan rike ta ba ya fiye maka wannan zance banza. Luba tashi mu tafi." Baba ta k'arasa zancen rai bace ta nufi hanya fita.

Da sauri ya tashi ya sha gabanta ya risina " Baba don kiyi hkr wlh na amince."

Murmushi tayi cikeda takaici tace " yo baka jira uwar taka ta baka izini ba, ka tafi ka nima izininta kar ranta ya ......"

Kuluwa ce tsugune gaba baba itama ta ce " Baba don Allah kiyi hakuri, wlh ba......"

" Ke yi mani shiru, ta Allah ba taki ba ke ba haihuwan kirki kika yiwa d'a na ba amma kibi kin mai dashi tamkar soko sai abunda kika ce yake yi ko?, toh bari kiji na fada maki wlh rikon yarinyar tamkar yayishi yagama kuma ko da rana daya kika musguna mata Allah ya isa. Kai kuma ga amanar na bar kama wlh in kaci amana kai da matar ka kuka hada kai kuka cutar da ita ban yafe maka ba." taja tsaki had'e da fadin " shashasha kawai"sannan tayi ficewar ta tabarsu gun risine.

Kuluwa ce ta tashi jiki sanyaye ta karasa gun da take tsaye rike da bakkon ta tana kallon abinda yake wakana, ta riko hannunta tace " Muje ba kai ki dakin kiyi wanka,ki ci abinci sannan ki huta ko?"

Dakin 'yar Yusrah takai ta, ta nuna mata duk abinda ya kamata sannan tace " nan ne dakin ki kai da 'yar uwarki Yusrah, itama sa'arki ce kilan ma ki girma mata. Shekarun ki nawa?''Kuluwa ta tambayetata. Sanda ta gama kirgenta da yatsu tace " goma amma innata tace watab gobe zan cika sha daya ."

Murmushi kuluwa tayi tace " ni kuma Yusrah ta sauran watanni 5 ta cika shakara goma kinga kin samu k'anwa ko, ai kina so ko?"

Gyada kai Luba tayi cikeda da murna tace " eh ina so ai zata barin muna wasa tare ko?"

" Sosai ma mai zai hana. Luba ina sonki dauki tamkar mahaifiyarki kinji ko?"

"Eh, toh ke ya sunarki?"

" Ammi Yusrah da yayata suke kira, shi kuma baban naku suna ce mashi Abba."

" Lah ashe kinada yaro, babba ne irin Abba?. "

Murmushi Kuluwa tayi sannan tace " eh amma bai kai abban ku."

Zata sake wata maganar, Kuluwa tace " maza tashi koje kiyi wanka ki zo ki ci abinci sai muyi hira ko."

Sauri ta shige bayin,tana shiga Kuluwa itama ta fita tana mai addu'a a zuciyarta Allah yasa yarinyar ta daure a haka ta kuma hada kai da 'ya'yansu. Dakin ta nufa taje ta samu Ahmad zaune yayi tagumi da sauri ta karaso gunshi ta cire mashi hannun da yayi da tagumin tace " haba mijina yasa yake damuwa kan wannan abun?, don Allah kayi hkr ku rabu da Baba lafiya kajin Abban Yusrah."

Ajiyar zuciya yayi sannan yace " hakika nagode wa Allah fa yabani matar kwarai, ke ya kamata na bai wa hkr amma sai gashi kece kike bani. Allah yayi maki albarka kuwa yasa 'ya'ya mu suyi gadon halin taki da kwarai, don Allah ki cigaba da hkr In Shaa Allah watarana sai lbr."

" In Shaa Allah Abban Yusrah kaima ta tayi da addu'a Allah yabani wasu 'ya'ya kuma nima ina bukatansu."

Murmushi yayi yace " inayi mana tawan, wai ina yarinyar take ne?"

" Na barota tana wanka wlh yarinyar bbu ruwanta."

" Allah yasa ta daure a haka." Matsowa kusa da ita yayi sannan ya rada mata wani abu a kunni da sauri tashi hadin da dan gudu tana murmyshi tana kaiwa daidai baki kofar tace " naki wayon salon na biye maka yarinya ta wuni da yunwa ka bari daddare koma menene na yarda" sannan tayi ficewarta.

。。。。。。。。。

Da yamma lis Bintu suka isa duk ta kosa suka kai gida don tayi bala'in gashi wannan farko zuwanta. Kallo kuwa sha shi har ma ta gaji da yinta.

" Helo Habu kana ina gamu a gareji sun iso ko " Jameela tace ga drivernta.

" Toh hajiya gani wannan zuwa."

Jim kadan sai gashi ya iso suka shiga motar, ya nufa gida dasu. Daidai harabar gidan yayi parking sannan yayi horn. Da gudu wasu yara suka fito daga cikin gida suna murna suka dosa yanda yayi parking. Da sauri karamin cikin ya dosa gurinta Jameela ta risina sannan ta rungumo shiyace " mummy oyoyo " cike da murna .

" Oyoyo my boy, how are you?"

" Fine mummy " Farid ya fada. A tare wasu yara mata biyu suka ce cikeda shagwab'a " watoh mummy Farid kawai kikeyi kewa mu baki k'ewan mu."

Sauke Farid tayi sannan ta rungumo su a tare tace " haba Ummi ni na isa kina uwata nafi son Farid a kanku, ina son dukkan ku "

" Ai sai ku bari ta huta kafin ku fata shirme ku" Umar yace shima yana mai karaso inda suka tsaye.

Bintu dai tana daga gefe tsaye tana kallonsu, sun matukar burgeta ina ma itace da Ummata.

A falo suka yada zango, sai a sannan suka lura ashe mummy ba ita daya ta dawo ba. Rahma tace " mummy wacce wannan ta nuna bintu."

Murmushi tayi tace "sunar bintu tare muka dawo da ita. Ummi maza budo mata ruwa tasha kafin taci abinci."

Ummi tace " mummy baga Rahma ba ita da bude mata mana."

Tsawa Umar ya daka mata " ai tahan Tahman ta ake ki, zaki tashi ko na bata maki rai."

Tashi tayi tana tura baki hadin ta buga kafa kamar zatayi kuka taje ta dibo ruwan.

Bintu dao sai kallon ikon Allah take a zuciyar tace " yo ashe haka 'ya'ya birni suke."

Kusa da mummynsu Ummi ta zauna sannan tace " mummy halan sabuwar housegirl kika samo mana?"

" A'a 'yar riko ce."

Cike da mamaki Umar yace " mummy riko fa kika ce."

" Eh shifa nace, ka gan na huta da daukar housegirl zata dinga tayani aiki ba tare na biyata ba."

" Allah ya tayaki riko " Umar ya fada a takaice.

" Rahma ki kaita dakin ku ta hutu."

Ummi tace " tab ynx mummy da housegirl za'a hada mana daki, nidai gsky bazan kwana daki daya da ita ba."

" No Ummi ba dakinku zata zauna ba, is jst for the main time kafin gyara dakin da zata zauna, kuma point of correction ba housegirl bace;rikonta zanyi."

Duk kan Bintu ya kulle ko menene *housegirl* kuma, a zuciyarta ta dauwa kanta alkawarin sai ta nimo ma'anar wannan kalmar.

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now