11

487 24 0
                                    

*🤦🏼‍♀🙆🏼‍♀ILLAR RIK'O*

    _('Yar rik'o)_


          *Na*


_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_


*♻REAL EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
_(Home of peace, honour & super writers)_



*Dedicated to all my fans*


_*Gaisuwa ta musamma ga member din kungiyata, ina yinki irin sosai dinnan. Allah ya hada kawunan mu. Ana mugun tare @ Exclusive writers forum.*_


_*BILKISU Z. YA'U*_
_*(Tawan)*_

_*Ina godiya da kaunar da kike nuna min. Ubangiji ya karemu da sharrin shaidan, yabar xumunci (Ameen). Alhamdulillah jikin da sauki.*_


*Wannan shafin sadaukarwa ce gareku members din EXCLUSIVE WRITERS FORUM, one love dearies😘😘.*


_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_


_*An karbo daga d'an Abbas Allah ya karamasu, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:Shayarwa yana haramta abinda haihuwa ke haramtawa.*_
    _*Bukhari da Muslim suka rawaitoshi*_


_*Page 11*_



Waige Ammi tayi da nufi cewa Yusrah taje dakinta ta dauko mata audunga(pad) sai ganin tayi itama Yusrah tana. Tashi taje wurinda Yusrah ke tsaye tace taje ta zauna kusa da Luba sannan tayi ficewata. Jim kad'an sai shi ta dawo rike da Pad da saba bin panties , zama tayi kusa dasu Luba naganin Ammi na shigowa da abu a hannu tayi maza ta share hawaye sannan ce "Ammi wani kalan biredi kika siyona mana, dagani zaiyi dadi, ko Yusrah? ta  k'arashe zance da tambayar Yusrah.

" I guess so" Yusrah ta bata amsa.

Murmushi Ammi tayi kannan tace " toh sarakan kwad'eyi wannan ba biredi bace."

" Toh Ammi menene?" Yusrah ta tambaya cike da zumud'in son sanin ko meye din.

"Wannan auduga ne wacce zaki ta anfanin dashi duk sanda kika jini domin tsaftace jikinki" laden ta yaga sannan ta ciro guda daya ta nuna masu yanda zasu yi anfani da ita.

"Kuma shi wannan jinin da kika gani ba abinda xaki tada hankali bane ko wacce mace baliga tana wata yinta duk wata, yana hana azumi, sallah,dawafi…… ynx tunda kina jini ba zakiyi sallah  har lokacin da ya dauke kuma da ace a watan azumine shima bazakiyi azumin ba amma bayan azumi zaki rama iya kwanakin da bakiyi azumin ba, sannan kuma banda wasa da maxa a makaranta, kin ji ko?!.

Gyanda mata kai Luba tayi. Ammi ta kara da cewa " duk sanda kika bari wani namiji ta taba ki ko kikayi wasan bazan, to ciki zakiyi kuma duk wanda yayi ciki batare dayayi aure ba mutuwa akeyi, kina son kin mutu ynx?!

"Eh" Luba ta fada idan nan raurau dasu kamar zatayi kuka.

"Yauwa 'yata,yanxu maza tashi kiyi wanka sai kixo ki saka wannan pant din". Tashi Luba tayi ta shige bayi.

"Yusrah hope kema kinji abinda na fadawa 'yar uwarki ko?!"

"Yes Ammi tnx mum, u are the best mum ever".

Murmushi Ammi tayi sannan ta tashi ta koma falo.

_*Don Allah iyaye ku zama masu sanya ido akan al'amarun 'ya'ya, koya ma 'yarki yanda zatayi idan ta tsince kanta a irin wannan matsayi. Amma abin haushi a ce kinada ta diyata mace har ta fara al'ada baki sani sai k'awaye zasu koya mata yanda zatayi in kuma tayi rashin sa'a k'awaye shi kenan daga nan sai su koyata mata abinda bashi. Ki fara motoring yarinyar ki tun tana shekara tara(early stage din fara period kenan) zuwa shekera 16. Idan kuma ta fara ki sanya ido duk watan da batayi call n ask, though atimes is normal bt da hakan zaki gane wasu abubuwa da dama. Don Allah iyaye a kula*_



。。。。。。




"Innalillahi-ina-ilaihi rajiun……" bintu na fada yayinda take bud'e idanuwanta  a hankali.

Da sauri Rahma ta karaso wurin daidai wurin filonta ta zauna tace " sannun Bintu  kin tashi?!"

Gyada mata kai tayi tana murza idonta sabida dishi-dishi da take gani.

"Barina kira ta Umar ta fada likita kin farka ko……" bata jira amsar Bintu ba ta fice da gudu ta fada masa.

Jim kad'an sai gashi ya shigo dakin tare da dr.

Dubata likatan yayi sannan tambayeta ko abinda dake damunta. Nuni ta masa da kanta wnda yake mugun sara mata. " Da me kuma" doc. din ya sake tambayanta. Dakyar ta bude maki ta fara magan a sanyaye tace " da idona, bana gani wuri dashi sosai in kuma nace zan bude shi sosai shine kan ke min ciwo". Dan dubeduben sa ya kuma yi sannan ya juya ga Umar yace " zamu barta zuwa gobe for more observation".



。。。。。。。。




A kauye kuma Inna ta tasa salale gaba wai sai ya nimo mata Bintu. Yayi  iya kokarin shi ya samu ko da adreshin gidansu Jameela ne amma abin ya faskara.

Yau kamar kullum daga gun aiki salale ya biya gidansu Jameelan ko zaiyi dacen samun wanda ya san gidan. A kofan gida ya sami Lado yaron kishiyar maman Jameela yana allola, sallama salale ya masa sannan yace " Lado don Allah wata taimako nake son kamin".

"Allah yasza zana iya" Lado ya fada takaice.

" Don Allah cewa nayi ko kasan gidansu Jameela, walahi yau kimanin shekara daya da rabi kenan tazo ta dauki 'yar gun inna amma har ynx bbu amo bbu lbr."

"Yo ku baku sanda halinta ba kuka dauki diya kuka bata ai walahi haka takeyi."

" Toh yanxu lado menene abinyi?"!

" Nikam wallahi bansani ba amma kace wa inna taxo gida tasamu baba delu wata kilan ta taimaka maku".

"Toh Lado nagode". Sannan ya nufi gida a tsakar gida ta tadda Inna tayi tagumi, karaso yayi gunta yace "Inna albishirinki?"

" Dallah  ni ka rabu dani, duk wani albishir zakamin inda bata gani Bintu ko hanya da zai sanya naganta ba bana maraba da ita".

Washe baki yayi yace "Inna ai na samo inda zaki samo labarin".

Tashi tayi da sauri tace " toh zama tahi,mutahi mana".

" Inna ki zauna mana kiji tukunna".

Zama tayi cikeda kosawa da son jin labarin. Yanda sukayi da Lado ya labartawa Inna sannan ta hada dacewa " Inna don Allah kibari gobe zai kike kinga gari yafara duhu".

"Tom "inna ta fada a takaice.



_*Mummy's Friend ce🤩*_

ILLAR RIK'O ('yar rik'o)Where stories live. Discover now