*🤦♀🙆ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's friend)*_
_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*_
*LITTAFAN MARUBUCIYA*
_*1. Na Tsani Maza*_
_*2. Meke Faruwa*_
_*3. Ruhin 'Dana*_
_*4. Shi Nake So*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS (ZAW)*
'''(Gidan zaman lafiya da amana In Shaa Allah)🤜🤛'''https://www.facebook.com/ZAMAN-A MANA-Writers-FANS-311893699485963/
*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*
*Page 90*
*BAYAN WATA BIYU*
Luba ce zaune tana shayar d'anta mai suna Nura, kana ganinta kasan bata cikin kwanciyar hankali, d'an watannin biyun nan da tayi a gida duk tabi ta rama ta k'anjame kamar wacce tayi shekara tana jinya.
"Ke tun d'azu shayar da yaro ne har yanzu baki gama ba? " Luba ta tsinkaye murya Inna na mata magana cikin d'aga murya.
"Na gama ko, yanzu zan tashi" Luba tace tana me cire wa yaron baki daga mama, zip taja sannan ta mik'e ta goyashi.
"Ki hanzarta ki d'ibo mana ruwa don ko na kama ruwa bamu da ita, sannan ki zo ki d'aura sanwa " cewan Inna.
"Inna don Allah ki tayani da wasu ayyukan mana wallahi na gaji tun safiya nake aiki" Luba tace tana goge hawayen da zubo mata.
"Au toh dama wa kije son yayi maki aikin, ni ko wa?. In ciyar dake sannan kuma nayi maki bautar? Ina ai wannan ba mai yihuwa bace. Ina ce uwarki na raye amma ta bar da wahalarki. "
"Haba Inna ai duk wannan abunda ya sameni kece sila kuma lokacin da nake samu ai duk ke nake kawo ma don ko na ba mama ba karb'a take yi ba. Wallahi Inna kin cuce ni... " Luba tace cikin matsanancin kuka.
"Lahaula-wala-kuwata ni Gaje naga ta kaina, Luba yanzu ni zakiyi wa sharri?. Ni na sakaki kije kiyi ciki? Ko ni nace ki lak'abama wani?" cewan Inna.
"Amma dai ko ke bace kika sakani yin haka a matsayina na yarinya da nazo na fad'a maka yakamata ki tsawata min amma sai kika yi sab'anin haka, illa ma gidan boka da kika kai ni akayi asiri ya aureni. Inna kin cuce, wallahi uwarta bata yi sa'ar mahaifiya ba. Ina ma ace na bi umurnin mahaifiyata da yanzu duk wannan bai sameni ba" Luba ta k'arasa zance had'a da d'aukar bokitin da zata d'ibo ruwan tayi ficewanta ba tare ta jira ta cewan Inna ba.
Tsabar mamaki ne ya hana Inna magana illa idon da tabi Luba dashi, wuri ta nima ta zauna tana mai zance zuci fad'in take "lallai duk wanda ya koyawa yaro rashin kunya ko kuma ya k'i tsawata masa watarana shi zai yima. Hmm ni Gaje na shiga uku gwara nasan abin yi kan wannan yarinyar tazo tafi k'arfina. "
A hasale Luba ta isa bakin bore-hole wanda yake cike da layi, "waye na k'arshe " Luba ta tambaya don itama ta ajiye bokitin ta a layin. Nuna mata akayi sannan taje ta ajiye a bayan bokitin da aka nuna mata. Komawa tayi gaefe ta jira layi ya kaeo kanta.
D'aya daga cikin matan take wuri ne taji suna maganar tana cema 'yar uwarta " ke jibi inda wannan yarinya ta koma kamar ba ita, kana ganinta kace mutuniyar kirki ce kamar ba itace ta shuka rashin mutunci ba da wai don wai tana auren maikud'i."
"Ke dai bari wallahi har ta bani tausayi, shiyasa bashi da kyau wulak'anta jama'a don kana dashi yau" cewan d'aya matan.
"Nikam babu wani tausayin da ta bani don naji ance wai asiri sukayi ma mutumin ya aureta, ashe ma mijin mai d'akinta ne" wacce ta fara magana tace.

YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...