*🤦♀🙆♀ILLAR RIK'O*
_*('yar rik'o)*_
*Na*
_*Aysha Isa (Mummy's Friend)*_
*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana, In Shaa Allah)🤜🤛__*Ashe dai akwai masu karanta illar rik'o har haka, 😂😂😂 anyi walkiya Allah ya toni asirin masu lab'e, sai Luba gashi ta sanya duk kunyi talk 😜😜😜*_
_*Masu cewa ina ja masu rai kusani fa ba laifi na bane rashin sharhin ku ne yasa na dauka ki basu karanta shi ne shiyasa nima bani son maku typing, am sorry dudes tunda kun gyara nima In Shaa Allah zan gyara don da bazarku nake taka rawa, duk rintsi duk wuya ana mugun tare🤝🏻🤝🏻.*_
_*BIMISMILLAHIR-RAHMIR-RAHIM*_
_*Page 58*_
"Abba ne" Luba tace cikin rawan murya.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"abin ilahin falon suke a nanatawa kenan.
"Luba kina tsoron Allah kuwa?"Jabir yace yana nuna ta da d'an yatsa.
Yusrah tace "Ina kuwa tagan shi ta rasa wanda zata kullawa sai Abba, wallahi karya take.... "
"Dallah ku rufe ma mutane baki manya na magana kuna sako baki, ke Luba fad'a min gaskiya waye yayi maki ciki?"
Abba tana nuna ta yatsa "Inna wallahi shine.. " tace tana me fashewa da kuka.
"Innalillahi wa ina ilaihi raji'u" Abba yace yana share zufar dake karyo masa, kai ya girgiza kawai don k'asa magana yayi tsananin mamaki.
"Yo shiru ma kayi ka zuba mana ido kenan?"
"Inna wallahi na rasa abin fad'a tsananin mamaki wai ace har ni zan yiwa 'yar da na dauka matsayin d'iyata irin wannan"
"Dallah rufa min baki, ku maza ina ruwanku da k'ak'anta yarinya toh wallahi bari kaji na fada maka aurata zaka yi ehee. "
"Aure kuma?" Yusrah da Jabir suka had'a baki, sannan Jabir ya cigaba yace "haba Inna yanzu har kin yarda Abba zai aikata haka kenan?, kuma ina kika taba jin anyi aure da ciki?, wallahi babu aurenta da zaiyi nasan k'arya takeyi "
"Yo ni nasani ai ky maza baku da tabbas, kuma ai bance da ciki zai aure ta ba, ka saka a ranka kamar an riga an gama yinshi babu fashi."
"Inna don Allah kiyi hakuri wallahi bazan iya aurenta ba a matsayin 'ya na dauketa."
"Au, ha dauketa matsayin 'ya shine baka ji kunya yi mata ciki ba?, toh wallahi baka isa ba"
Mikewa Ammi tayi ta nufi tafiya daki don abin ta fara isarta kanta in banda sara babu abinda yake mata har tana gani, tayi taku kamar hud'u sai suka d'if da alamar wani abu ya fadi, juyowa sukayi domin ganin ko meye, Ammi suka gani kwance da gudu yo kanta, Yusrah ce tafara kiran sunanta amma shiru girgiza ta shiga amma ko gizau batayi ba da alamu ta suma ne. Da sauri Jabir ya nufo yara bata taimakon gaggawa har ya samu ta farfad'o,
su kam Bintu da Yusrah suke inda kuka barin ma Yusrah, Luba ma tasha jinin jikinta ganin halin da Ammi ta shiga, itako Inna ko a jikinta daga baya ma tashi tayi tajq tsaki tare da fad'in "wallahi ko mutuwa zakiyi sai anyi wannan auran."Abba ne yace "Jabir me kaje ganin ya sameta?", "jinin tane ya hau, an auni arziki ma da aka samu ta farfad'o da wuri haka, Abba wai dama Ammi na da BP ne?"
"Wallahi nima ban taba sani ba sai yau."
"Hmm Allah ya kyauta, yakamata mu kaita daki ta huta"Jabir yace yana me da dubansa ga Yusrah da take faman shashaka, mikewa tayi ita, Abba da Jabir suka tallaba suka kaita daki sannan suka fito suka bar Abba a dakin, gefenta Abba ta kwanta yafara aikin rarrashi, ido Ammi ta bishi dashi hawaye na zuba kan fuska a zuciyata kuma tana son gasgata maganar Luba gaskiya ne ko k'arya, haka dai Abba ya cigaba da rarrashinta har bacci yayi awon gaba da ita.
**********
Lamarin gidan su mummy kuma sai gaba yake tun barin Bintu gidan basu kara samun yarinya zata iya hakuri zama dasu a kalla yanzu son samu kusan 'yan aiki hud'u zuwa biyar ko amma babu wacce ra kai ko wata d'aya a cikinsu sai su gudu.
Umar kuma kullum cikin kewarta yake idan yaji abin nason damunsa yakan ya kawo masu ziyara har su d'anyi hira da ita.
Ummi kuma har yanzu babu abinda ta iya in banda gayu ko dakinta bata iya gyara wa dama Bintu ce ke gyaran. Aunty Rahma yanzu 'ya'yanta biyu Sabir da Najwa, tayi bakin cikin jin bintu tabar gidan.
*Bayan Kwana biyu*
Zaune suke a falo suna hira bayan sun gama dinner. Ammi tace "Jabir ina son ka maida Bintu k'auyensu ranar asabar"
Zaro ido Yusrah tayi tace "Ammi but why...?
Muje zuwa
_*Mummy's Friend ce🤩*_

YOU ARE READING
ILLAR RIK'O ('yar rik'o)
RandomLabarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta far...