*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**_Episode ~ 7_*
"Innalillahi illah wa'inna ilaihim raju'un" ita ce kalmar da tayi gaggawar zuwanmata a baki cikin faduwar gaba, ta shiga dube-duben ko wanne gefe lungu da sak'o domin gasgatar da abinda take gani ba mafalki ba ne.
A hanzarce dubanta ya koma wajen flowers, sai dai da mamakinta wa zata gani?
Amratu ce kwance a yashe kamar wata tsohuwar gawa. sai sharbar baccinta take a wajen cikin rashin sanin inda hankalinta yake.
Nan take Hajiya Munira ta ji zuciyarta ta katse kamar ta fashe da wani raki'in kuka akan wani azababben tausayin 'yarta da ta ji ya yi mata katutu a cikin zuciyar, bata ankara ba ta ji alamar fitowar wata 'yar munafukar kwalla a cikin kwayar idanuwanta tana bidar yi mata tambari a saman kunce.
Cikin hanzari ta yi gaggawar cira hannunta sama ta cinna farcen ta dagal a saman kumatunta ta samu damar yarfe ta tare da Addu'ar Allah ya saka masu, sannan ta tashi ta koma gefen da Fatie ke kwance da gabad'ai illahirin k'afufuwanta ta gama kakkasa su waje daban-daban ko wacce k'afa ta kama wajen zamanta can nesa da daya sai kace wata k'azamar tunkiya, sai birkid'a take tana mulmula A saman tabarmar kamar wadda Aljannu suka tasoma, sai dai daga ganin wannan baccin kasan bana jin dadi ba ne.
A hankali ta shiga tayar da ita cikin tausasa murya mai kama da zallar tausayi.
_A hanzarce Fatie ta zabura ta mik'e zaune tare da cira hannayenta sama tana miqa mai hade da hamma sai kace wadda ta shekara biyar bata saka lomar tuwo a bakin ta ba, sannan ta maida hankalinta wajen mahaifiyarta cike da firgici tare da tambaya a bakinta, ta ce "Hajiya dik ina sauran mutanen dake wajennan? ya kuma naganmu saman wannan guntuwar tabarmar kamar Almajirai? Hajiya meke faruwa ne ko dai an batar da mu ne?" a jajjere tayi ma mahaifiyarta wad'annan tambayoyin tare da mik'a aron hankalinta gareta, tana jiran k'arin bayani.
Cikin wani irin murmushi mai cike da kunar zuciya Munira ta ce "Uhum Fatie ki kwantar da hankalinki, ba wanda ya batar da mu, a nan ne muke kwance tin dazu sai dai ban san yanda aka yi mutanen dake wannan wajen suka tashi suka bar gurinnan ba, nima yanzu ne tashina daga baccin."
Cikin kwancewar brain Fati ta waiga baya tare da ta sake ce wa ko k'ala ba, ta hango Amratu kwance a cikin flowers kamar matacciya sai kwasar baccinta take.
A rud'e ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihim raju'un! Hajiya Aunty Amra ce ke kwance yashe a wancen wajen dako rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba akan ba za'a rasa kunama ko miciji a wajen ba! wa ya yi mata wannan danyen wulaqanci sai kace wata baiwa wadda bata da amfani?"
Hajiya ta ce "Hmm! ke de bari kawai Fatie, ita din ce ba kowa ba! kije ki tadota lokacin sallah ma ya yi ta tashi tayi."
A sanyaye ta ce "To Hajiya! Amma gaskiya wlhy wannan wulak'ancin ya yi yawa tin da muka shigo gidannan muke fuskantar wannan abin! gashi ko kadan kin hana mu maida masu martani wallahi ni da na sani banzo gidan nan ba Hajiya, wannan wulak'ancin da me ya yi kama? idan an gama da wannan kuma sai a farma wannan! wannan wanne irin abu ne haka sai kace wasu marar galihu wadanda aka tsinto a jeji kamar ba gidan dan-uwanmu ba , a nai mana yadda aka ga dama."
Hajiya ta ce "to ya munka iya Fatie in banda hak'uri? mu fallama wa Allah komai, shi kadai ne zai iya karemu daga dik wani shairin na su! Allah na tuba kwana nawa ne zamuyi mun daga mun basu waje daganan kuma ba zasu sake ganinmu ba sai idan wata lalurar ce ta sake hadamu da su, ai komai na duniya yana da lokacinsa wata rana sai labari, Ni yanzu babban abinda nafi buk'ata a gareku yanzu shine, dan Allah kuyi banza da Al'amarinsu dik abinda suke ku daina ma kula da shi balantana har ya dinga banna maku rai kuna zama daya da su."Fati ta ce "To shi ke nan Hajiya! in sha Allah zamu yi kokarin kiyaye wa, bara na je na tada ta din."
Hajiya Munira ta ce "To Allah ya k'addara Nima ai tashi zanyi nayi alwala tin lokaci bai k'ure ba, nayi sallah."
Fatie ta ce "Wlhy kuwa Hajiya! na ma ji kamar wani gurin har sun qarqare."
Ta ce "Eh wlhy Fatie bara naje wancen fanfo na yi alwalla kafin ki tayar da Amra."
ta ce "toh Hajiya"
ita ma tashi ta yi ta je wajen tayar da Amratu, wanda tana k'arasawa wajen ta shiga bubbugar ta a hankali dan ta samu ta tashi.
A gajiye Amratu ta bud'e idanuwanta cikin rashin kwarin jiki, domin dik inda gab'b'an jikinta suke ciwo suke mata kamar wadda aka dank'ara ma wani dan banzan duka. ta kai zaune cikin d'aukar Kalima a bakinki, sannan cikin mamaki ta duba Fatie ta ce "wa ya kawoni nan.?"
Fati ta ce "wlhy Aunty Nima ban sani ba amma na san dik wannan abin ba zai wuce aikinsu Gwaggo Uwani ba domin gabadayansu sun tashi daganan sun komawarsu daki sannan sun kwashe tabarmin dake shimfide anan muma saman waccen guntuwar tabarmar suka barmu da ita."
ta ce "To ba damuwa, Allah ya fisu."
Fatie ta ce "Wlhy kuwa Aunty, tashi muje muyi alwalla muyi sallah lokaci ya yi."
Ta ce "To Fatie taimaka man na mik'e tsaye."
Ta ce "To Aunty" ta dagata ta tashi suka nufi wajen da suke hango Mahaifiyarsu a can tana Alwalla."
Bayan sun gama alwala, suka zo nan saman tabarmar suka shimfida dankwallayen'su a sama sannan suka saka hijabayyansu suka tayar da sallar su, da yake da hijabayyan'su suka kwanta dan dasu sukayi lullubi.
Bayan sun gama sallar ne suka dan samu waje daganan wajen da suke, suka dan gincira kafadunsu suna jiran safiya ta ida wayewa su tashi su farma aiki.
Ba su wani jima da kwanciyar ba saiga munafuki bacci ya zo ya fara zund'arsu.
Sai misalin 7:30pm suka farka a lokacin da suka ji alamun ana kokarin budar kofar main palour'n da su Ammie suke ciki da key.
Suna maida dubansu ga wajen suka yi gaggawar kauda kansu gefe domin sun halkanta da fitowar dai daga cikin "yan uwan Ammie a cikin dakin dauke da wani qaramin flat a hannunta gefe guda kuma Atika ce tafe ita ma dauke da nata flat suna tin karo wajen da suke.
ko da suka iso daf da su suka ajiya kayan ba tare da sunce da su komai ba suka koma inda suka fito, haka suma basu ce dasu ko uffan ba suka yi banza da su kamar yanda sukai masu.
Ba su tashi daga kwanciyar da suke ba saida suka ji alamun shigewar su Atika cikin daki sannan suka mik'e zaune suna duba abinda ke cikin flats din, kayan soye-soye ne zube a cikin k'aramin flat din wad'anda basu taka kara sun karya ba. Irish potatoes ne da biredi soyayye mai hade da kwai dasauran dagwalgwalon yara, wad'anda da ganinsu kasan ragi ne aka kawo masu, inda shi kuma flat guda dauke yake da kofukan shayi guda ukku wanda dik yabi ya gama tsarwakewa da ruwan banza, kamar ba'a saka madara a cikinshi ba sannan ko wanne bakin cup din dauke yake da Jan jambaki alamar sai da aka sha ne aka rage masu saura.
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...