*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_**WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_. 🤧 frnds ina neman addu'ar ku kwana biyu banajin dadin jikina🤕🤒_**_Episode ~16_*
*_Previous_*
*_🤕EMTY🤒_*_Bayan an fito da ita daga wajen wanka abokananta su biyu suka shiga shiryata, Maimunatu wadda suke kira da Memu ita ce ke tantsatsa mata kwalliya taji da fadi wadda daman ita sana'arta ce domin har shago gareta na makeup, sai Hansa'u dake fidda mata kayan da zata saka waje tana zolayarta cikin raha sunata famar dare-darensu.
*—•••«»•«»•«»•••—*
A bangaren Ango kuwa shi ma har an gama wankeshi tass da ruwan lalle kamar dai yanda al'ada ta tanadar, inda Muhsin sarkin zolaya gabadai ya gama wankeshi da maganganun k'eta kala-kala har wadanda zaka yi k'ok'arin kira ma "Subhannallah." wanda hakan yasa suma sauran abokanayenshi ba a barsu a baya ba wajen tofa albarkacin bakinsu cike da nishadi mai hade da tsantsar farin ciki.
****
Hajiya kaka ce kwance a cikin dakinta ta saka mukulli ta kulle kanta a cikin, an yi da k'arya, an yi da gaskiya amma tak'i ta bude sai famar "Allah ya isa." take zobo ma mutane tare da dungureren zagi mai cike da bak'in bala'i na bak'in cikin an wanke Uncle Mukhtar a gidan Alhaji Ibrahim domin ita a yanda ta so, a wankeshi tas kamar kwarya a cikin gidan ubansa, amma babu wanda ya goye bayan ta domin al'adance a garin sokoto ba a haka, shi ya sa ta tsunbula kanta tsunbulbul a cikin tekun zargin mutane bila adadin akan sun mata ssiri ne.
*****
Bayan an gama shirya amarya tsaf a cikin wata hadaddiyar atamfa Super holland bak'a mai cakude-cakuden pitch acikin'ta riga da zane.
Atamfar ta yi matuk'ar yi mata kyau sosai tamkar wata balarabiya, inda dik wanda ya kalleta sai ya ji baya son dauke idonsa gareta.
9:20pm, motocin daukar amarya suka bayyana a gidan Alhaji Usman, inda cikin masu daukar Amaryar kuma har da su Hajiya Saudat da Hajiya Khadija da sauran tsofaffin unguwa wadanda aka yi zaman mutumci da su.
Ba tare da bata lokaci ba, aka dauki Amarya sukutun aka kaita wajen mahaifinta ya saka mata albarka, inda cikin tattausan Lafazi Daddy ya shiga yi mata huduba iri-iri masu ratsa zuciya wanda saida hakan ya yi sanadiyyar wargajewar dik wata k'asungumar rashin kunyar da take tak'amar zata tafi da ita gidanta, domin sai da wata 'yar guntuwar kwalla ta zubo a saman kuncenta.
Bayan daddy ya gama yi mata nasihohin shi tare da fatan sake sabuwar rayuwa mai inganci a gidan mijinta, aka kwashe ta aka wuce da ita bangaren Ammie, ita ma babu wani bata lokaci ko jinkiri, ta shiga suburbudo mata tata kadan-kadan mai had'e da shashshek'ar kukan rabuwa da diyarta da zata yi, a bayyane kamar yanda ta nuna, wanda hakan yasa gabadai 'yan daukar Amarya komawa palourn salun-alun dan ba su waje.
Ammie na ganin sun fice daga cikin bedroom d'in, ta saka hannu ta share hawayen munafurcin da suka mata shane-shane afuska, a hankali ta ce "Dik cikin abinda na fada a yanzu! ban yarda ko daya ki dauka a cikinsu ba ko da kuwa cikin rashin sani ne."
Cikin wani tantirin iskanci, Balkisu ta share hawayenta ita ma, kana ta ce "Kar ki samu damuwa Ammieta, na fahimta da komai dama ni tin can azal ban yarda da "yi, na yi, bari, na bari ba." dan maganar ma ni ta bayan kunnena take bi tana wucewa."
"Allah ya yi maki Albarka d'iyata haka nake son ji a wajenki!. sannan abu na k'arshe da zan k'ara tunatar maki da shi a yanzu shi ne, "ki tabbatar cikin gidannan baki raga ma kowa ba musamman Hajiya Lauratu maihaifiyar mijinki, dan dik wani rashin mutumci da ta ke ma sarakkunnenta ba wanda ba'a sanar da ni shi ba, haka ma dik wanda ya kuskura ya shigo harabarki ni na ce ki watse dan iska ko da kuwa uban shi ne."
"Ai In sha Allah Ammie ba zan taba yin sake, damata ta wuce ni ba."
"Haka nake son ji, amma dai ina fatan baki manta da rigar da Boka Mintsinkyu ya bamu ba?"
"Habaaaa Ammieta! Ina zan manta da tsokar jikina? ai ita ce jigon rayuwar zamana a cikin wannan gidannan, dan ganin na rarraba kawunansu tare da taimakon Ustazunmu Boka Mintsinkyu." gabadayansu dariya suka kwashe "ehahahhhhh" kamar wasu Alhazzan karuwai......
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...