*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—*
*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2♠️]_** WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_**_{🌼YAHOO ~ smartfeenert@yahoo.com🌼}_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*_[https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation]_**_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
*—•«»•–•«»•–•«»•–•«»•—**_Dedicate this fage to my wattpad fan's luv u more😘_*
*_Episode ~23_*
_Har ya gama lalurar shi ya fito sanye da bathrobe, tana kwance saman gado ko alamar tashi babu a tattare da ita.
Cike da wani matsanancin ɓacin rai ya bude widrop ɗinshi ya fitar da jallabiyarshi waje tare da boxer ya saka ya cire bathrobe d'in, sannan ya koma saman kujerar da ke gefen gadon ya kwanta ba tare da ya ce da ita komai ba, sai famar tunane-tunanen shi yake iri-iri a cikin zuciyarshi cike da k'udurin daukar wani ƙwaƙƙwarar mataki a kanta gobe idan Allah ya ƙaddare za'a waye safiyar da su, dan yana son jin taƙaitaccen dalilinta na rabawa ƴan saman titi budurcinta har zata zo gidanshi haka, sai dai dik da hakan bai ƙudurce sanarwa da kowa wannan abin ba domin a tunanin shi wannan sirrin shi ne kuma sirrin matarshi ne, dole ya kare mutumcinta da na iyayenta.
Da rarrafe ta fara saukowa k'asa daga saman gadon sai famar tsak'e-tsakenta take a zuciya na jin haushin abinda yayi mata.
Inda tana ida saukowa ƙasa ta nufe wajen da yake dan dik a tinanin ta bacci yake, ta yanda zata samu damar ɓuɓɓurma mashi zagi son ranta, sai dai tin yanda ta aza kwayar idanuwanta a saman fuskar shi ta ga shi ma ya zuro mata na shi dake jawur kamar garwashi yana jifanta da kallon ukku saura kwata.
A hanzarce ta ɗauke idoanuwanta daga kan na shi cikin mugun tsoron shi, ta shige bathroom ta wanke jikinta, dan shi wankan tsarki ba'ama san shi ba, balle a yi.
Bayan ta gama abin da take yi ta fito daure da towel ta neme kayan ta na bacci ta saka ta koma saman gado ta yi kwanciyar ta da ƙudurin ɗaukar nata matakin a cikin sili-silin daren nan domin matse bakinshi kafin ya kai ga rutsata da tambayoyin da amsar su suke da matuƙar wahalar bayarwa a wajenta.
*⌘⌘⌘⌘⌘*
Tin 4:am Uncle Mukhtar ya tashi ya nufi masallaci domin gabatar da sallar Subahin dinshi a can, dik da ma lokacin yin sallar bai ida gabatowa ba, amma a yanda yake ji gwanda ya koma masallacin ya zauna ko hakan zai iya sanyaya mashi zuciya, domin a daren jiya ko baccin kirki bai samu damar yi ba a kan tunanin wannan abin, dan ya matuƙar ɓanna mashi rai.
Fitarshi kaɗai ke da wuya ta tashi ta bi bayan shi ta kulle get da key sannan ta dawo dakin a hanzarce ta fiddo wani ɗan ƙaramin a kwati a cikin widrop dinta ta saka security ya bude sannan ta fiddo wata ƴar ƙaramar jaka a cikinshi, ta budeta da zip din da ke make gareta ta ciro wata baƙar riga mai layi-layin jan jare a cikinta.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta cire tufafin dake jikinta ta sanya wannan baƙar rigar, nan da nan ta ji tsikar jikinta ta fara tashi da wani mahaukacin shucking dake ratsa gaba dai ilahirin cikin tsokar jikinta.
Ko 3seconds ba a k'ara ba, kwayar idanuwanta gabadai ta rine ta koma jawur tamkar jini, sannan farin ijjiyarta ya koma baƙiƙirin kamar gawayi...........
Follow me on wattpad and vote.
YOU ARE READING
WAHALA DA GATA season2
FantasySeason 2. "Hhh ai gaskiya ne Rukayya ni wlhy kin san Allah sai yanzu na san nayi dace da sarakkuwar ta gari domin waɗancan dik sheguna ne matsiyata." "Sosai ma Hajiya! ai Aunty Balkisu kam, ta wuce kowa a cikinsu, sannan ta......" Sa...