35

3.4K 309 16
                                    

✨*RUHI DAYA*✨
             35

©HAFSAT RANO

Wattpad: *HafsatRano*

Haske Writers Association 💡

This page is dedicated to you kanwata *MSS XOXO*  ki cigaba da yimin biyayya yadda kika saba😂😂. #*SAIFUL-ISLAM* yana tafiya dai-dai but yana kaɗan, ki dinga irin typing dina read-more goma😝😝. Saura inji bakin ku anan🙄  🚴🚴

*#Dota Meela*
*Sis Jamila*
*Oum imaan*
Ina yinku irin sosai ɗin nan. Thanks dearies for sticking with me all xa tym.✌️

✨✨✨

*K*allon ta yake har ta ƙaraso cikin ɗakin, hannu tasa ta kunce daurin da yake hannun sa, tana gamawa tayi saurin rungume shi, da karfi ya hankaɗe ta yana mata mugun kallo, kallon shi take ita ma, zaro ido yayi a d'an razane ganin kamar a buge take, yadda take sake matsowa kusa dashi ne yasa shi saurin mik'ewa yana ja baya. Koƙarin kamo shi take yi tayi baya ta faɗi a wajen saboda rashin ƙarfin jikin ta, surutai ta fara yi cikin maye, da sauri sauri ya fara ƙoƙarin ƙwance Malam, yanayin ɗaurin da akayi masa kaɗai zaka san ba ƙaramin jigatuwa yayi ba, yana ƙoƙarin ƙwance igiyar ƙarshe yajiyo maganganu daka nesa, sauri ya ƙara ya ƙwance shi, bashi da ƙarfin da zai iya tafiya hakan yasa Ahmad ya fara tunanin yadda zai iya fitar dashi daga wannan wajen, tuno nisan tafiyar yayi gashi babu wani da yazo daga gida hakan yasa yayi tunanin lallai Sadiya bata ga ni ba, kallon ko ina yayi a cikin d'an ƙurƙutaccen ɗakin babu wani wajen buya, ko wajen da mutum zai gudu. Kallon ta yayi ganin yadda take surutai yayi saurin zuwa ya d'an dungure ta,

"Tashi, kina so na ko?"

"Sosai..." Ta faɗa da sauri tana yin baya. Hararar ta yayi, dole yayi amfani da ita ya fitar da Malam daga wajen nan ko dan lafiyar sa.

"Nima ina sonki."

"Da gaske?" Ta faɗa cikin Muryar maye.

"Da gaske, amma sai dai mu fita daga nan muje gari, komai zaifi tafiya dai-dai."

"Allah?" Kamar ta san Allahn ya faɗa a ransa, a fili sai ya ɗaga mata kai

"Da gaske mana, zaifi ai ba yan sa'ido."

"Ummm, ina zuwa."

Mik'ewa tayi ta nufi hanyar fita tana ɗan layi, lekowa yayi kad'an ya hango ta nufi wani haɗaɗɗen gida da sam be lura dashi ba ma sai yanzu, mamakin girman gidan yake a ransa ya raya ko ita ma aljanar ce? Yana ganin ta shige ya sauke ajiyar zuciya ya jingina da wajen yana jiran ta.

Chan ya ji kamar tsaiwar mota a waje, kafin yayi wani yunkuri sun shigo, tare take da wani namiji, kallon ta yayi kamar ba ita ce ta fita a buge ba, fes take ta sauya shigar ta ma.

"Muje ko?" Ya tsinkayi muryarta  akansa.

"Shi fa?" Ya nuna malam dake ƙwance.

"Anan ka sameshi ko? Toh ka barshi anan kawai."

"Anan? Mesa zan barshi? Yana bukatar magani kin ga bashi da lafiya."

"Tsakanin su wannan. Muje kawai kafin ya dawo."

Kamar zai musa kuma sai ya fasa, gefen da Malam Yahaya yake ya kalla sannan ya kalleta, daga mishi gira tayi, murmushi ya kalalo yace

"Minti biyu ku d'an jirani a waje dan Allah."

Dan jim tayi kafin ta juya ya take mata baya. Matsawa yayi da sauri ya riko Malam yace

"Zan dawo na tafi da kai a yau yau ɗin nan, zanyi duk ƙoƙarin da zanyi a kama Garbati, karka damu komai yazo karshe."

RUHI DAYA (Completed✅)Where stories live. Discover now