38

3.3K 247 10
                                    

*RUHI D'AYA*
      46-48

© HAFSAT RANO

HASKE WRITERS ASSOCIATION 💡

***
D'ago ta yayi fuskar nan ta jiƙe gaba ɗaya da hawaye, ajiyar zuciya take sauke wa alamun tsananin kukan data ci,shafa kanta yake a hankali tausayin ta yana ratsa shi sosai, babu yadda ya iya dole ce ta saka. Gyara mata kwanciyar yayi ya sauka ya nufi bathroom zuciyar sa wasai.

***
Zafin da ake yi ne ya hana ta sokuni gashi nepa sun dauke wuta, duk kuwa da yan da gidan yake da fili sosai yanayin jikin ta ne jin zafi, in ba haka ba ma yaushe sanyin ya wuce, tashi tayi ta janye jikinta a hankali kar ya tashi, a nutse ta sauko ta nufi falon ta bubbud'e kofofin da windows d'in ta baje sosai, barci ne ta kwashe ta a wajen har aka dawo da wutar ma ba tare da ta sani ba.

Wajajen karfe goma ya farka sai dai be bude idon sa ba, gefen sa ya shafa yaji wayam hakan ya sashi saurin bud'e idon, da azama ya duro ya lek'a toilet bata nan, falon ya nufa ya tarar da ita a saman kujera tana ta bacci hankalin ta kwance, daidai kan fuskar ta ya tsuguna yana gyara mata zaman hular da ke kanta, sosai ya jima yana kallon ta yana hasaso abinda ya faru a daren jiya, duk kuwa da cewa akwai yarinta sosai a tare da ita sai dai ya yaba mata wajen dauriyar da ta yi, a hankali ya kai bakin sa saman goshin ta ya manna mata kiss yana lumshe ido

"I love You so much Sady!."

"I Love you too." Ta furta a ranta, daidai Lokacin ta farka sai ta kasa bude idon ta, sai da ya gama budurin sa ya tashi sannan ta bude tana sauke ajiyar zuciya.

***
Toilet ya shiga ya had'a mata ruwan zafi bayan ya yi wanka, a gefen gado ya tarar da ita tayi saurin rufe idon ta don ba k'aramin kunyar sa take ji ba, ruwan hannun sa ya fesa mata a fuska yana dariya

"Inna ta wayyo Malam."

Ya fad'a cikin kwaikwayon muryar ta, tashi tayi da sauri zata fice yayi saurin damko ta.

"Babu in da zaki wallahi."

"Ka bari Allah." Ta fad'a a shagwabe tana jin jikinta wani iri babu dad'i, yanayin fuskar ta ya kalla yayi saurin cewa

"Menene?"

Kafarta ta nuna masa da hannu

"Ciwo take?"

"Ummm."

"Ayya sannu."

Hannun ta ya kama har cikin toilet d'in, ruwan zafin ya dan kara yace mata ta matso, ki tayi don ta ga alamar cewa zaiyi zai mata kamar jiya da daddare, ya gane sarai me take nufi, hanyar fita yayi kawai jin wayar sa na ringing aikuwa tyi saurin maida kofar ta murza mata key don kar ma ya dawo.

Da sauri ya k'arasa ya daga wayar, Seema ce suka gaisa, Muryar ta na dan rawa tace

"Na dawo ne ashe ban fita da key d'ina ba ina waje."

Samun kansa yayi da dan duburburcewa, baya so yace mata ba a gidan suka kwana ba saboda har ga Allah baya son yayi hurting feeling d'inta, kame-kame ya shiga yi kafin ya samo abin fad'a

"Minti biyar mun dan fita ne yanzu zamu dawo."

"Ohh... Ok."

RUHI DAYA (Completed✅)Where stories live. Discover now