31

4.2K 177 0
                                    

           💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 32

Babu dad'ewa aka basu hannu, tuni jikin Rahma yajik'e da gumi dukda AC dake aiki amotar, jikinta sairawa yakeyi, duk addu'ar datazo bakinta karantawa takeyi.
     Dakansu suke nuna mata hanyar dazatabi, sunyi nisa sosai datafiya awata hanyar k'auyen da Rahma batasan ko inaneba, wayartace tayi wringing harzata d'auka Wanda yake rik'e da bindiga yadaka mata tsawa, kina d'agawa zan tarwatsa kanki.
    Janye hannunta tayi da sauri akan wayar, Wanda yake rik'eda Nawal ne yad'auki wayar, saidai kafin yad'aga ta katse, wata uwar dariya yashek'e da ita Dan ganin sunan daya kira Rahman, *_dadyn Nawal_*.
       Wani gida suka kaisu, zuwa sannan Nawal tayi barci, Dan sun shak'a mata wani abune, Rahma tarungume Nawal tana kuka maiban tausayi, aranta tana tunanin misukayima wad'an nan mutane dazasu kawosu nan??.

Bobo kam hankalinsa yafara tashi Dan ganin yayima Rahma kira wajen 10+ amma bata d'agaba, dukda d'umbin aikin dake gabansa haka ya tureshi yabaro office d'in.
       Makarantar su Nawal yafara zuwa, auntyn su ta ce, "aii tund'azu bayan yakira kamar yanda ya ce, " momynta ce tazo ta d'auketa, to babu dad'ewa tazo ta d'auketa.....
    Bai tsaya yagama saurarentaba yayo waje, daga nan gidansa yanufa, tun a gate yatambayi mai gadi, amma ya ce, "basu dawoba.
    Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kawai yake ammabata azuciyarsa, amma dukya birkice, da sauri yaciro wayarsa a aljihu yakira khursiyya, itama ta ce, " basu zoba, Abu kamar wasa dukya rewad'e dangi dakira amma kowa amsa d'aya yake bashi *_basu zoba_*.
     Cikin rawar jiki yakira Appa yaturo masa number Abbansu Rahma.
    Cikin girmamawa ya gaidashi, tareda masa bayanin shine, Abba ya ce, "ALLAH sarki Abdulmaleek ngd ALLAH yayimaka albarka, ya su Rahma d'in?. Tun anan jikin bobo yayi sanyi, murya asark'e ya ce, " dama ita zantanbaya ko sunzo nan gidan?.
     Kai A'a gsky Rahma batazoba, kunyi da'ita zatazone?.
     A'a Abba dama...... Nan yafad'a masa yanda akayi.
     Abba yaja numfashi, to mud'an k'ara hak'iri zuwa d'an anjima mugani kota biya wani wajen, dukda dai nasan wannan baya d'aya daga cikin halayen Rahma, tabbas da Safna cema bazan damuba Dan nasan tanada rawarkai, amma Rahma kam batada wannan halin.
     To abba. Kawai bobo yafad'a ya yanke wayar, kuma kiran Number Rahma yayi amma ank'i d'auka, yadafe Kansas tamkar zai FASA ihu, yana nan tsaye ak'ofar gate saiga ya ishaq da ya Hamza, suka tambayi yanda akayi yasanar dasu.
     Ya hamza ya ce, "kasanarda Ammar ne?.”
    Girgiza kai kawai bobo yayi danya kasa magana, ya Hamza yakira Ammar yayamasa bayanin kimai, salati ammar yashiga yi, bai tsaya 6ata lokaciba yabaza yaransa ki ina.

Al'amarifa kamar wasa hardare babu wani bayani, zuwa yanzun labari yakarad'e dangi, bobo kam dukya fita hayyacinsa, sai kuka yake tamkar mace, shidama haka yake akwai jarumta amma Abu kad'anne ke karya azuciyarsa.
      Duksun dawo daga sallar isha'i, suna zaune afalo gidan Appa zugum², harda Abban Rahma da Umminsu, momyn ya Kamal da dad d'insu Ameera ihsan ya Muneer ya shaheed duk suna gidan Appa, Safna CE kawai babu, dantana makaranta abin yafaru, bayan tadawo mai gadi yashaida mata komai, yad'ora da fad'in 'yangidanma duk suna gidan surukan Rahma d'in.
     Safna ta ta6e Baki ta ce, " kaga baba bud'emin gate nashiga nahuta tukunna, Dan bazan iya zaman jigum jigum ba wlhy tunda ba mutuwa akace sunyiba.
     Maganar tata tarazana baba mai gadi, bayan yabud'e mata gate yabi mortar da kallo yana jin kina kai, aransa ya ce, "lallai yau nakuma shaidawa yarinyarnan batada mutumci ko kad'an, inbanda rashin mutumci d'an uwanka uwa d'aya uba d'aya ya6ata kanuna rashin damuwarka, kai ALLAH dai ya k'yauta to.
     Safna dai bamatasan yanayiba Dan tuni tashige cikin gida abinta, sai wata fara'a takeyi wadda nadad'e ban ganiba daga gareta.

🤔araina Na ce, " safna Kodai kidai??.

    *_3days_*
Tsawon kwana uku kenan da 6atansu Rahma, Abu tamkar  wasa, zuwa yanzu kam aii kowa yajigata, Appa yabaza rok'on ALLAH amasallatai, hakama gidan redio Dana TV, social media ma haka, amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, kuma tun ranar ba'a sake samun number Rahma ba.
      ALLAH sarki bobo acikin kwana ukunnan Yayi wata uwar Rama, ko abinci bayasonci sai ammi ta tsareshi tamkar yaro tabashi abaki, shima lauma hud'u zuwa Biyar zaice yak'oshi, saitata lalashinsa sannan zaiyarda yak'ara kad'an.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now