52

3.1K 176 0
                                    

             💖ABDUL-MALEEK!!💖
                             (BOBO)

             Bilyn Abdull ce

Pg 53

Alhmdllh abubuwa nata tafiya yanda yakamata, su Rahma harsunyi arba'in, yara sunyi 6ul-6ul dasu abin sha'awa da birgewa kamar subani, bak'aramin gyara Ammi takrma Rahma ba awanan zaman wanka, aiko ko ita kanta tasan taji gyara Dan fatarta tayi wani k'yau da laushi, kuma zammm takejin kanta.
    Bobo nata fushi Dan yaso sukoma gidansu tuni, ammi ta ce, "saidai yakoma shikad'ai su Rahma dai ba yanzuba, wanan dalilinne yasashi fita harkar Rahma gaba d'aya, shi adole fushi yakeyi da'ita, daga gaisuwa babu abinda yake had'asu, saikuma yad'auki yaransa kokuma yazauna ad'akin yana musu wasa, ada Rahma tashiga damuwa da sauyin nasa, amma da Ammi ta zaunar da ita tana lallashinta da nuna mata itama tafita harkarsa da Kansa zai dawo gareta, daganan sai Rahma tasami nutsuwa, wani lokacinma har dariya yake bata idan yana shan k'amshi, musamman idan takamashi yana satar yimata kallonnan nasa k'asa-k'asa, dasun had'a ido saiya gimtse fuska, kokuma yakwashi yaran yabar mata d'akin.
    Ita kanta ammi bobo yana bata dariya, data kasa daurewa har Appa tabama labari, shima yaci dariya ya ce, " babana na kaina.

Bayan kammala arba'in suka fara zaga dangi.
  Gidansu tafara zuwa, bak'aramin farinciki Abba da ummi sukayiba daganin jikokinsu, anan tawuni sai dare oga yazo yad'aukesu abisa matsawar Appa, Dan ya ce, "dolene yakaita ko ina takeso.
   Haka suke tafiya amotar babu mai tanka wani.
   Washe gari kuma gidan ya ishaq sukaje suka yini saidare yaje yad'akkosu, daganan kullum akwai gidan dazasuje su yini, haka sukaita zaga dangi, sunje gidan ya sulaiman, gidan ya Hamza, gidan ya Shaheed, gidan ya muneer, gidan Ammar, gidan aunty yahanasu, gidansu marigayiya Ni'ima, gidan khairiya da khursiyya, gidan Ameera, gidan Basma, kai babu Inda basu zagaba, gidan Safna ne k'arshen zuwa, tabar gidan Safna k'arshene dantasamu suje weekend yakaita tunda safe tawuni sosai.. 
     Aiko ayau Asabar suka Isa gidan, cikin farinciki Safna ta tarbesu, har mamaki Rahma tayi, sai nan-nan takeyi dasu, tamkar tagoyasu Rahma, cikin mutunci suka gaisa da bobo, Wanda shima canjawar safnar kebashi mamaki.
   Itakam zuwa yanzun zuciyarta fes, kallon bobo takeyi amatsayin d'an uwa kuma mijin k'anwarta, bayan haihuwar Rahma tak'ara dukfa da addu'a, takuma k'ara Neman gafarar iyayenta, suka kuma k'ara jaddada mata sun yafe mata suna kuma k'ara tayata da addu'a ALLAH ya daidaita lamuranta.
  Wad'annan abubuwanne suka taru suka k'ara taka rawar gani wajen inganta farincikita dakuma jin son bobo yafita fit azuciyarta, saidai tana ganin girmansa damasa soyayya irinta 'yan uwantaka tamkar su ya munner, soyayya mai tsafta kuma ingantacciya suke gudanarwa itada mijinta, wani bala'in sonsa takeji ayanzu haka, shima soyayya yake nuna mata irinta 'yangatan mata kamilallu, dankoba komai yana alfahari da safna, cif tazo MASA a cikakkiyar budurwa shiyya 6areta aleda, dama baita6a kallonta dawata illaba saita tsiwa.
    Su Kansu Rahma da bobo yau sunsha kallo, danba kunya safna da ya Kamal suke narka soyayya agabansu.
     Rahma taji dad'i sosai dataga 'Yar uwarta tak'ara kwantar da hankalinta, aiko yau sosai takejanta ajikinta, su shareefa kam ai tamkar ta lashesu Dan so da k'auna, wuni sukayi ahannunta, tad'auki wanan ta ajiye ta d'auki wannan, haka suka wuni cikin farinciki da k'ara k'aunar juna.

Su bobo na fita sallah Safna taja hannun Rahma suka shige k'uryar d'aki, magunguna tad'akko tabama Rahma, tanata mata bayanin yanda zatayi amfani dasu, Rahma tarufe fuska yana fad'in kai aunty Safna ALLAH kina bani kunya.
    Dukan wasa Safna tayima Rahma, kai auta gulmarki tayi yawa wlhy, idan kina tareda ya Abdulmaleek aii idonki rufewa yakeyi amma saikina gabanmu kice wata kunyar gulma, dama sabodake na had'asu, jiyannan nakecema my heart yakaini gidan Ammi nakuma gano yarana, ya ce, "nabari sai ranar Sunday, to ashema kuma hanya, 'Yar uwa k'ara gyara kanki ya Abdulmaleek yaji zammm danya k'ara rik'e manake d'amm, safna tak'are maganar da d'agama Rahma gira, dariya suka saka harda tafawa tamkar wasu k'awaye, Rahma ta ce, " ALLAH yabarminke auntyna, suka kuma kashewa da dariya.

ABDUL-MALEEK (BOBO)Where stories live. Discover now